← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 312

Sashe 45

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun ya bata mamki da takaici makura, bata san lokcin da ta aje wayar akasa ba ta dawo jikin madubi ta kalle kanta tafara tuna irin lokcinta data bata, da uban kudin data kashe, da Abincin data zauna ta dafa dakanta sabida dashi, da dukkanin hopes dinta na kawo karshe wa matsalokin rayuwar aurensu ayau din, she sees her dreams being crushed bcos of one stupid birthday. Extreme anger yafara running tru her veins a haukace ta yi watsi da kayan gaban mirror suka zube kasa ta fashe da wani irin kuka me karfi.

Wani zaiyi tunanin cewa Abun bai kaina har haka ba, Sede ita awajenta ya kai harya wuce hakan, sabida ta riga ta saka dukkanin kwayayen ta a kwando daya, tana kuma tsammanin yaune zai kasance mata wata rana na musammn a babi auren ta, kuma rana na daban datake tunanin zai kawo mata kakkarfan maslaha game da sexual life dinta gabaki daya.

Har kasa ta durkushe bisa kan gwiwanta tana rero kuka mai kara mai kuma ciwo da radadin takaicin femi.

She just cant belive she failed to mend her marriage again.

Depression da tsananin Haushi yasakata ta zauna awajen tumus acikin decoratons din ta dinga kuka tana tuna irin yawan hakurin datay da halin femi, da irin kame kanta datakeyi duk dama bai taba bata wani gamsuwar aure ba. To stay Few month witou sexual satisfaction in marriage is not even a bearable bare ita datayi shekaru yaukam ita kanta tasan ta riga da ta kure gejin haqrinta..

She cant take it anymore.
Dis pain and suffering has to stop!

Aranta ta jima da sanin cewa Alakar femi da chief okoro yana daya daga cikin babban matsalar dake damun aurensu, its emotionally draining her musammn inta yi lissafin yadda femi yake bada muhimmnci da fifiko akan chief harma fiye da ita datake matarsa na aure.

In har she is dis irrelevant to him to ya zamo dolene kenan ta dena kokartawa akansa gabaki daya tunda yau ya nuna mata da alaman yana samun kwancyar hanklin da bata bashi ba awajen chief okoro.

Gani tay Wann auren nasu ne su biyu ba nata bane ita kadai. Babu wani dalili da za' ace ita kadaice keneman gyara shikuma hanklinsa yana ta wani wajen akan aboki bama dan uwansa ba unless if he is tired of her and the marriage.

Tun zamanta anan babu abunda batay nazari akai ba..sosai jikinta ya dauki zafi dan takai karfe biyun dare tana sobbing tana kuka, jin kamar kanta na bugawa yasaka tabi ta jawo kwalban ta bude ta fara shansa akai akai har ya kashe mata jiki karshe awajen tabi ta kwanta bacci me nauyi ya saceta.

Ayayinda vicky tay kwana cikin tsananin baqin ciki da kuncin yanayin rayuwarta, mijinta femi da masoyinsa chief okoro kuwa kwana sukayi a gidan suna morar junan su har saida asubahi tay kafin suka kama bacci.

*******
Washe gari Sassafe wajajen karfe shida Henry ya damesa da kira, acikin gigin bacci ya farka ya dauki wayar babu bata lkci henry ya gaya masa cewa vickyn tazo nemansan jiya snn gaskiya shi yanata tsammnin cewa ta gane cewa dashi sukayi waya dan haka yaanaa baashi shawara yaje gida kar vicky taji haushi tace zata rabu dashi maganan ya jawo masa babban scandal da zai saka mutane sufara bibiyar alaqarsa da chief okoro.

Acewar henry muddin jama'a sukaji cewa aka Chief ne matarsa ta rabu dashi toh tabbas da akwai wayanda duk tsiya sai sun bankado gaskiya.

Da can maganan bai wani shige jikin Femi ba face saida ya sauƙa akan gadon da kyar ya wuce bathrum ya gasa kansa a ruwan zafi ya sha pain killers yaji dama dama kafin nan maganganun suka soma making masa senses sosai.

Just then he realized He cant afford to loose vicky sabida itadin kamar garkuwa ce babba wa rufin asirinsa da chief okoro.

Atake atake yahau shirya kansa zai tafi gidan yaje yaga meke faruwa da ita.

Yana cikin saka kayansa chief ya farka yanayin gigin bacci ya hade ransa yanace masa ina zaije bayan basuyi soyayyar safiya ba.

Femi bai wani kulasa ba har saida ya kammla saka kayanshi tsaf snn ya taho gefen gadon ya zauna snn yahau masa bayanin abunda henry yace masa akan vicky

Da mamakinsa sai yaga chief baiji haushi ko ya hanashi tafiya ba dan kuwa burinsa ya riga da ya cika wajen nunawa vicky cewa tabbas shine da zucyar femi ba ita ba.

Alkwarin dayay mata na cewa zai jefata acikin baqin ciki ranar anniversyn su ya cika..

Duk da baccin dame idonsa amma yau Har gaban mota ya rako femi yaname cemasa inhar vickyn tana bukatar wani abun duniya koma miyene kawai ya gaya masa shizai siya mata sabida tay hakri.

Agaban femin sai yay fuskar tausayi kamr irin shima baiji dadi da suka mata hakan ba alhali aransa murna yakyi sosai.

Tunda femi ya watseka ya dawo hayayyacinsa yakejin fargaban tunkarar vickyn na shigarshi..

What if she really want to file a divorce yakenan zaiyi? Shide baison ma su rabu bare yace zaiyi tunanin auro wata dan baisan ya zasuzo su kare da asirinsa ba.

Karfe shida darabi yay masa a hanyar gida sai sharar gudu yake akan titi yana goge kansa da hanky time to time duk ac dake busoshi bai hanashi jin zafi taciki ba.

*****************
Ata daya bangaren kuwa tunda Halisa ta koma bacci bata tashi farkawa sai can da wayarta ya dameta da kara sosai.

Tun bata kammala bude idanuwanta ba ta damke saman kanta dake mata wani irin nauyi sabida maganin bacci da khaleel ya zuba a ruwan ya balain bugar da ita sosai

Batare da ta bude idanunta ba ta luluma kam gadon har saida ta capke wayar tata kai tsaye ta jefashi a kunnenta batare da taga wayeke kiranta.

Muryanta kasa kasa sigar bacci tace Helooo

Ajiyar zuciya Jasmine ta sauke tanamai cewa oh thank god u picked up har kinsan naji tsoro.

Halisa Tanajin muryan jasmine din murmushi ya kufce mata ahankli tace
" tsoron me, why, Did u think im dead???

Jasmine tace
"You dare not die!
Ki cire zancen mutuwan nan abakinki mana halisa? Da muryan lallami tace "cmon tell me Are u okay???

Ahnkli halisanta bude lumsashun idanunta da sukayi jaaa tsabar tsumayin bacci tace
Kowa zai mutu Jasmine
Death is inevitable komun so ko bamuso ba

Jasmine tace naji..ki amsa min dayan tambayar.

Nannauyar ajiyar zuciya halisa ta sauke tace wani tambayane jass?

Jasmine ta dafe kai
"Ohh Bazaki gayamin yadda kike din ba kenan kinfiso na cigaba da zama acikin fargaba.

Jasmine kidena fargaban komo i swear to u bazan taɓa kara tunanin kashe kaina ba sai nawa zance miki ive regreted it, wallh nayi nadaman yin hakan.

Cikin katseta Jasmine tace good nide babban fargabana da damuwa shine zamanki agidan wann baqar macijiyar cos i am sure she is stalking u.

Ahankli tace "Yes she is, but am not allowing it anymore jasmine. Kawai zama agidan nan ne is more than living in Hell

Jasmine tace meyasa?

Mikewa zaune Halisan tay da kyar snn tace "Duk lokcin danaga fuskar meenal kona naga na mijinta a kusa dani ji nake kamar na mutu dan haushi suke cusamin. Gashi na buga na buga amma da alaman babu wanda zai amince dani msmmn innace bazan sake aikata suicide ba.
Dr Asim baima dauka na me cikakken hankali ynxu. Kowa gani yake kamar am mentally unstable, inna koma gidana zan je ne in kashe kaina. But seriously takaici ma kadai zai kashe ni anan gidan.

Cikin yanayin tausaya jasmine tace Hakane Halisa amma kiyi hakuri mana ki daure u need to obey the doctors dan su gane cewa kin warke suyi suyi su sake miki freedom dinki da wuri

Cikin kyabe baki halisa Tace hmmm me ? Obey which doctors..pls take off that plural(s) nide likitana daya ne kuma shine kawai nake ganin girmansa.

Jasmine tace Kai halisa karkice min har yanzu kina bada gayen nan ciwon kai?....

Nake bashi ko shi yake bani jasmine ke kinsan iskancin da gayen nan yakemin kuwa? So yake yamaida abun wasa yara dama neman dama yake da zai walakantani sai kuma gashi ya samu.

Jasmine tace dont see it like that halisa ..ki karbi abun kawai da zucya daya nide nasan da yanada niyyar walkantaki da bazai fa risking rayuwarsa yabiki cikin wann babbaan tekun ba.

Shikenan kuma dan ya ceto rayuwana akace saina fara bauta masa
Nan Tafara mita tanamai zayyana ma jasmine din duk yadda sukayi dagashi.

Banda dariya babu abunda jasmine din takeyi "are u serious ya doraki akan diet time table? Hahahah my god this is intresting

How is this intresting jasmine kema fa babban munafukace bayansa kike bi ko bayana?

Jasmine na dariya tace
I'm with u my friend amma da kika tsaya kina masa kukan ne naga wautarki. Ya riga yasan baki kaunar zama a inda yake zaiyi, kekuma taurin kai toh ai zai ta amfani da taurin kan nakine yana sakaki a matsala awajen Dr aseem karshe sai kiga kinyi shekara kina jinya a hannunsa.

Halisa tace God forbid
Ai satin nan ma banaso ya kare ina gidan nan wallh na rasa yadda zanyi ne in gunduresa ya kare jinyan nan akan lokci ya sakeni in tafi.

Jasmine tace hmmmmm
They are many ways baby girl.. kibari kawai zan rubutu miki tactics din a tex anjima..ki gwada zaki ga shida kansa zai dena shiga harkanki inbaiyi wasa bama sai kiga yana Allah Allah ya gama ya turaki gidanki kawai within kwana uku.

Cikin tsananin farinciki halisa tace "Jesus, i just cant wait to see that text.
Dariya sukayi atare

So hows ur show in london? Sorry ban ma tambayeki ba.

Jasmine tace komi ya tafi dede. Sede anan ma mutane da yawa sunji labarin case dinki na suicide..tsoffin boses dinki na fashion house sunata tambyana wai ko kin fara shan drugs ne.

Dariya Halisan tay cikin kyabe baki tace "wato idan kika samu mutanen movie indusry dana fashion industry to kin gama zuwa bus stop din gulma kenan. Suyi ta harsashen su nide bana cewa kowa komi. Naga Rayuwata ce!
Chapter 45 · 0% Book details