← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 312

Sashe 205

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata jima ahaka ba wayarta yafara ringing kin daukawa tay dan batason ma taji wani abun da zai sake daga mata hankli, kusan sau uku aka kira bata leka ba ana hudun sai aka turo mata sako, shidin ma da kyar ta jawo wayar ta duba tana budewa taga sunan alfahn ta a zumbur ta mike tsaye har ta kammala karanta sakon ahujajan tay dialing lambarsa snn ta fita waje cikin sauri don suyi magana dashi...

Fannin Halisa kuwa washe gari sassafe haka tasake farkawa da tunanin khaleel da mahaifinsa cike a cikin ranta, tunda ta bude ido zuciyarta ke zugata akan taje ta samesa suyi maganan hala ko shi zai saurareta tunda taga khaleel din baya son kulata wanka tay ta shirya kanta cikin abayan data saka jiyan snn ta killace kanta tsaf bata shafa komi akan fuskanta ba.

da sassafe ta fito lkcin wajen ya dau shiru ta nufi suite dinsa dan baida wani nisa da nasu, tafiya take gabanta na mugun faduwa ga fargaba ga komi amma taurin kanta yasaka ko jin sha'awar komawa baya batayi ba.

Koma miyene zataje tarar inyaso koma me zai faru ya faru itade dolene taje ta tunkaresa yau

tana kaiwa kofar kirjinta ya dinga bugawa cikin tattaro makanta jarumta ta kai hannu kai ta fara kwankwasawa ahnkli inta buga sai tay sallama da sanyin murya sai can kafin nan akazo aka bude mata cak numfashinta ya dauke sabida tsoro suna hade ido taga aliyu ne ta kirkiri murmushi tace hi yanata kallonta da mamaki ya juya ya kalle agogo yaga 6:30am ya sha mamakin ganinta
anan muryansa adan rarrabe yace Helo, ure here? tace uhmm, yace okay come in,. Biyosa ciki tay suka zauna akan couch dakin babu kowa dagashi sai sai shi yabi ya tsura mata ido duk ya dauka ko wani abu ne ya same yayan san.

Murmushi ya kirkiro cikin gyaran murya snn yace anty halisa kin tashi lafiya, i hope der is no problem? Ya ibrahim fa

Cikin sauke ajiyan zuciya
Tace "Ohhhh He is fine, probably sleeping..take yaji hanklinsa ya kwanta
Sai Baice komi..Cikin saukar da muryanta kasa kasa tace"Dad dinku fa?.

Da Mamaki yace wajen sa kikazo ne? Kai kawai ta gyada masa,yace ayya yanxun nan kuwa ya fita zasuje da'awa lectures a wani town kusa da Abuja shiyasa suka fita da wuri gashi bansan yaushe xai dawo ba...

Dafe kanta tay tace kash nayi latti kenan uhm pls inya dawo sai ka gaya min amma pls dont let ur brother knw abt this kaji?

Yana kallon yanayinta yace okay i will amma akwai wata matsala ne..

tana dan murmushi tace no I just want to ask him few stuff..atakaice yace ok. Wani Shiru ne yadan ratsa tsakaninsu sai satar kallonsa take aranta tana ta kokonton ko ta masa maganan ne ko tay shiru. sai can taga ya mike ya dauko ruwan tea ya zuba mata cup ya mika mata yace "tea" ta karba tace thank u shima zama yay da nashi a hannu ya tsura mata idanu cikin karantar mood dinta har ta sha kurbi biyu snn ahnkli yace i knw u wan t to say sumting.,..cikin lumshe ido da budewa tace well yes amma ai nasan bazaka so ka amsa ni akai ba shiyasa bance maka komi ba.

Cup dinsan ya aje yace
"Try me..dan shiru tay snn tace hmm wani abu ne yake damuna aliyu..

Ya gyara zamansa snn yace meyene..Hannunsa ta kama cikin nata with serious tune ahnkli tace aliyu dan Allah karka boyemin komi pls menene ya shiga tsakanin Khaleel da babanku haka ya zamo khaleel yana behaving haka agabansa all the time.. Aliyu yay shiru baice mata komi ba tace "i knw i am not part of ur family but khaleel is part of me now, he is my best friend kuma abun sun yana damuna sosai.

Wani nannauyar ajiyan zuciya Aliyu ya sauke snn ya kwace hannunsa anata ahankli ya kalleta cikin ido da sanyin murya yace Anty halisa wann matsalar tasu ta wuce tunanin ki, nide shawarar da zan baki shine ki fita aciki..if not u will end up loosing ur friendship da yaya ibrahim.

Cikin sauriN katseshi tace "but why? Mesa kowa yake cewa haka even sister mryam batason maganan nan she wll alwys dismiss it why?

...cikin katseta yace
"What happen is too personal for him anty halisa, yanxu sama da shekaru goma kenan mamanmu tanason sasantasu amma the more she try the more baba da yaa ibrahim suna nesanta kansu da mu ni kuma bana ganin lefin yaa ibrahim anty Halisa bansan me zanyi ba.
araunane ya karashe fadin hakan kmr hawayen sa zai sauka kasa cikin shanyewa ya karkada kai yace Pls dont ruin evrything.

wallh munjima bamu ga yaa ibrahim ajikin mu ba haka ba har saida kikazo, wani bin a shekara baifi kagansa sau biyu ko daya ba amma tunda kika shigo rayuwarsa muke ganinsa akai akai i am begging u karkiyi abunda zai saka ku bata dan wallh ya ibrahim baison ma ana dago masa maganan nan...

Tunda yafara maganan idonta a lumshe yake har sanda yay shiru kafin nan tabude idonta ahankli ta kallesa muryanta a sanyaye sosai tace toh
Shikenan naji, and i am sorry for making u speak abt it. aje cup din tay snn Ta mike tsaye tace pls dont tell him abt now..i wll figure out wat to do.

Da sauri ya mike tsaye ya riko hannunta, yace pls pls anty halisa don't ruin ur frendship bcos of this pls..Dan Allah kibar maganan nan in Allah yay zasu shirya kansu you knw, lkcin da muke yan kananan sosai mama takan ce mana duk duniya babu abunda baba yake kauna aransa kamar yaa ibrahim. i think maybe dats why is hard for him to forgive him for just one mistake i think dis fight is btwn them pls karki shiga ciki.

...Ahnkli ta kwace hannunta anashi snn tace Aliyu, nay maka alkawari i will not ruin our friendship Amma bazan taba iya zama ina kallonsa ahaka ba so yes zan shiga ciki.

Aliyu na kallonta ya shiga gigirza kansa da alaman jinjiina ma taurin kanta

tace nasan bankai ku ko mumy muhimmanci a rayuwarsa ba but still i am going to try my best anawa bangaren, baban ku yasha gayamin cewa Aljannar mace yana karkashin kafar mijinta ne, amma kasani aliyu aljannar khaleel da jin dadin duniya da lahiransa kaf yana karkashin kafar iyayensa ne, in sunje gaban Allah ahaka kaima kasan still khaleel shine me lefin..
i watch alot of islamic videos with ur dad..and i understand that children are meant to be patient with their parents sabida su samu kansu cikin rahamar ubangijinsu da rabo ranar karshe..

ahnkli tace Aliyu everyday i wish my parents are alive..or i have siblings,or anyone..

,..hawaye ya cika idonta tace but no..Duk dukiyar dana tara duk luxuryn danake ciki bazai bani wann damar ba.

u knw all he eva do was to help me get out of my own miseries, he dug into my personal life and heal me...and i think i will return dat favour to him and pls dont ask me to stop.

..Aliyu ya rasa me zaice haka ya koma ya zauna jikinshi a mugun sanyaye yana furta hasbiyallaah wa neemal wakeel dan yadda yaga ta furta kalaman nata da taurin kai babu abunda zai hanata ayyanawa har cikin ransa kuma yake jin tsoron abunda zai biyo baya...

Batace mishi komi ba takama hanya ta nufi kofa har saida ta bude zata fita snn ta juyo ta kallesa tace masa pls dont tell him anything abt this and pls stay out of this kaji..yace okay ma'am..Ta gyada kanta Ahnkl tace i wll call u up later inbaka komi zamuje wani waje.. nan ma yace okay. Batace komi ba tasaka kai ta fita yabita da kallo har saida ta bace ma ganinta duk sai kuma yaji ya damu sosai.

Daga nan dakinta ta nufa
bata je wajen khaleel Din ba sai can wajajen 9:30am lkcin ta gama shirya kanta tsaf anitse ta fito tana tafiya cikin tunanin me zatayi a hanya suka gamu dashi yana kkrin zuwa wajenta shima, kallon juna sukayi kowa da abunda ke yawo aransa, aransa shi yanata tunanin ya aure ta anytime soon anata ran kuma tanata tunanin yadda zata dinƙa alakarsa da mahaifinsa ne yanxu.

babu yabo babu fallasa ta gaishe shi ya amsa nan suka wuce wajen yin break fast dinsu subiyun su yanata hoping ya gaya mata wani abu dake tafe dashi dan shisam bai iya yin doguwar hakuri he just want to let her knw how much he love her.

Suna zaman awajen ta daga wayarta takira aliyu a waya tace masa ya sauko suci abincin tare.

After few min sai ga Aliyu ya sauko suka zauna su ukun sukaci Abinci in a quite pace daga ganin khaleel kasan yana bukatar lokacinta Amma kuma sai yaga yanayinta da aliyu wani irin kallon kallom da suke jefawa juna a sace aransa yasan hala sun shiryane zasuje wani waje dan haka sai baice mata komi ba.

After break fast din sukaje room dinsa dukansu basu wani jima ba sai ga jasmine tazo hotel din da security inta
Abaya, Aliyu ne yaje ya taho da ita suka zauna ata waje cikin wani mini outdoor tea spot aka gaggaisa ta bawa khaleel
Katin aurenta tare da box na items din customised kayan bikin tay inviting dinsa formally to her weding events, basu wani jima suna hira ba khaleel yace musu akwai inda zaije, haka jasmine din ta sake jan halisa da Aliyu suka fice gidansu domin tana son Aliyu ya dan tsaya mata akan wani abu kafin suje fitting din farko da halisa su dawo..Haka suka rabu
Kowa ya nufi inda zaije
Traditional wear guda hudu aka cire wanda zata saka haka suka dauki the whole day suna
Wajen fitting din ahaka
Ma kaya biyu aka ci nasaran gwadawa snn suka dawo gida yau ma kusan by 8pm halosa da aliyu suka koma da wuri tay bacci sabida gajiyaN datayi harse washe gari suka hadu da khaleel dayazo room dinta bayan sallahn fajr suka danyi hira wanda hakan yasake katse mata boyayyar shirinta na zuwa wajen dad din nasa ayau..
Chapter 205 · 0% Book details