← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 312

Sashe 171

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannin tunanin ya zamo kusan kowani rana yace ta turamsa pic na morning face dinta sai ta tura mai hotonta dats almost half naked wanda da inyagani sai ya jima yana cikin wani hali.

Tun suna morning Selfie hqr tafara tura masa night gabaki daya ta zautar dashi yayansa henry dake zaune dashi a gidan har yafara tunanin ko baida lafiya ne baisan vicky ke gigitamai lafyar idanunsa ba. She is good in taking erotic pose, shikuma saidai ya sake recreating din pose din a zane ya turo mata wanda yaci uban wann din kyau, dan ya iya zana mutum ya fito xak zak shi. babu kalar rokonsa da batay ya tura mata kansa ba amma haka yaki, Tace masa in bazai tura ba ma ya zana mata kansa tagansa. It took him a while kafin nan ya zano kansan, da shape din fuskansa da komi amma blank face babu kamanin sa ajiki tunda ya tura mata kwakwalrta yake dawowa mata da siffar kayden amma to bata taba ganinsa full babu riga ba how cud she even testify.

Tun tana hada kamanin dirinsu da shape din fuskarsu hartazo ta hakura ta dena kullum zai na tura mata hotonsa amma na zane baikuma taba zana kansa da fuskansa ajiki ba amma haka kawai take ganin kamarsa da most annoying and pestering student dinta kayden.

Haka tay printing hoton ta cire ta manna a gefen gadonta sabida tatoo din sunanta dake gefen kirjin shi dayake mugun kashe ta intagani,".. wani irin soyayya me zafi suke yi acikin wani irin ruddyar yanayin da bai bayyana musu ba...alkwari ta masa cewa duk sanda suka hadu she wll draw his real name on her boobs too..inta fadi hakan saidai yay dariya.
shikuma tunani yake duk sanda ya mallaketa ta kwana dashi he wll draw her naked body on his back amma baiko gaya mata hakan ba.

********
Rana bata karya yau sassafe hafsa ta farka da shirin tafiya wales dul wani abunda take bukata na field trip dinta ta zubashi a karamin jakar trolley nata na LV brown colour, doguwar wandon data saka maroon color ne irin me fadi sosai din nan snn ta pairing dinsa da beige top kalar kasa da doguwar winter jacket dinta maroon colour kalar wandon, tasaka beige boot shiba me tsini ba shiba guntu ba, veil din datay rolling kalarsa zak irin rigarta na ciki ko kwalliya bata ma fuskata ba amma wayyo tay kyaune kamar asaceta.

Hakanan ta gama shiri ta sauko kasan cikin sauri tana qamshin turaren cloud by ariana grande qamshin baiya tashin hauka amma daga kazo jikinta zakaji kamar jikin flower kazo.

inna hjyace ta sakata dole tana karyawa, Sama sama taci breakfast din tana cewa mummy dan Allah kiy sauri ki fito wallh nayi latti karsu tafi filin jirgin su barni..

Tanakan surutun saiga hajya bintan ta fito da wani abu a envelope toh gashi dama wann aikan mahmud ne nay magana da supervisor naki, zai barki, zaki kai masa har inda yake pls already na gayamai zakizo, kasar wales kam duk a waje guda suke u wll just go by bus or train ba wani nisa.

Tunda hajya ta ambace sunan mahmud taji abincin ya tsaya mata a wuya saida tasha ruwa kafin ta turasa kasa da kyar tace toh sai ta rasa me zatace kawai ta karbi sakon ta saka ajakarta ta musu sallama har waje suka rakata suka rabu ana kewar juna dan sati biyu zasuyi a wales din kafin nan su dawo.

Tana isa schl park ta samu kawayenta azrha da Jasmine na jiranta da permit tickets dinsu duk sun shirya tana zuwa sukaje suka nuna ticket aka barsu suka shiga schll bus tare da sauran students daga nan aka wuce dasu filin jirgin da zai kaisu yankin Caernofen castle dake cikin kasar wales din.

Bayan sun isa aka kaisu acomodation dinsu da safe suka fita field yin abunda ya kawosu na research din karatu.

Wani bin haka zakaga tay shiru tana kallon waje guda kamar marar lfya badon komi ba saidan mamakin yadda rayuwa ya dawo mata yau gata a wani duniyar nadaban kuma dama hakanan Allah yake tsarinsa bakasan zuwanka bakasan randa zaka mutu ba hakama bakasan yadda ya tsara maka rayuwarka ba wata rana sai kaga kanka a inda baka taba tsammani bama.

dan Shikansan wann trip din ma wani bude idon ne me zaman kansa, sunje wajajen tarihi da dama sunji labarai kala kala daga bakin masana da kuma malamansu da sukaje tare bayan kamar kwanan su biyar lkcin ana washe gari hidimar su mahmud ta lura kamar kullum ne sai tay mafarkin mahmud, a mafarkin sai taga cewa gashinan ya fadi a kasa cikin turbaya ruwan sama yanata dukansa yanata kuka ita kuma tana tsaye akansa tana hawaye batare da tasan meke damunsa ba.

tsakar dare ta farka tana jin matukar tsoron wann mafarkin datay wanda kwata kwata bata gane me yake nufi ba, gashi tasan gobe zai je ya baje basirarsa a bainar dumbin mutane masu ilimi da fasaha arnd the globe yadda taga ya sha wahala akai ya jajirce tasan it must be really huge for him komeye mafarkin nata yake kkrin gaya mata oho...PLS DONT SHARE MESO YA SHIGA YA BIYA CHAT 08060712446. ONLY!!SURAYYAHMS.

Thank you All for ur unwavering support and coments Jazakhallah khairan, is wish zan iya jera suna but u get mita pass me, these page is dediceted to all tue comenters and likes
❤️❤️❤️❤️❤️ Meenal da kawarta Shema'u suna gaisheku kyauta😂🤗

Sauka tay akan gadon ta doro alwala ta gabatar da nafila cikin dare ta masa yan adduoi Na musamn ko babu komi bazata taba mancewa da tausayi da kuma hallacin da mahmud ya nuna mata da ita da mahafyar ta ba addua ta zage ta masa sosai na fatan samun nasara har saida hanklinta ya dan dawo jikinta snn tahau tuna cewa wata tsohuwa agarinsu takance musu idan wani mutum yay mafarkin ruwan sama na dukansu ko yana kuka toh duk alheri ne ke bibiyar rayuwarsa.

Duk dama ta damu amma bata wani daga hanklinta sosai ba she just remain optimistic cewa in sha Allah Wani abu na musammn zai faru dashi a rayuwansa koba akan wnn hidimar ba.

Hakanan ta tashi da azumi abakinta kowani lkci silently zakaga tana cikin ambaton Allah akan samun nasarar mijinta mahmud, duk abunda akayi ranar tunaninta nakan mahmud ne dan tasan duk yadda akayi yana can tunda yaune ranar da suke ta jiran gashi tazo.

yau ma sassaafe suka fita aka Tattara su izuwa L' euston, sede tun kafin su fito supevisor nasu ya tsareta ya bata leave card dinta da addres da phone number ajiki yace mata daga zarar sun gama hidimarsu ta yau zuwa four clkc zai sakata a train daga euston zuwa chester da banqor, daga nan kuma har cikin birnin london which is almost 4hrs 3 min by that train..

a lissafinta kenan Zata iya isa wajen mahmud wajajen karfe 8 Da rabi na dare, yace mata tana sauka a train station din ta kira lambar card din, na taxi cap ne zaizo da tag ya kaita har inda mijinta yake basai tajira ba. Saida ya tabbata ta gamsu da bayaninshi kafin nan suka shiga hidimarsu babu wanda ya gane cewa tanama azumi.

Bangaren mahmud kuwa yau tun dayay sallahn subh bai koma bacci ba yanata bitan abubuwan da yay snn yana kuma addua bayan nan yay waya da iyayensa dukan su biyu suka dan kwantar mai da hanklinsa sosai snn ya shirya kansa cikin wata brown suit kalar kasa wadda bata shiga brown din sosai ba yasa farar rigarsa yar sharara me kyau ata ciki da agogonsa da takalminsa all black he look so neat, smart and confident ya dau badge dinsa na engineers ya jona agaban aljihunsa jikinshi na baza wata sassanyar qamshin turare ya fito a hotel din ya nufi wajen taro da wur wuri. Kirjinsa na bugawa amma haka ya fuske Bai saka komi aransa ba, snn duk sanda yaga wani abunda zai damesa awajen yakan tuna maganan iyayensa ne da suke ce masa nasara na Allah ne ba a hannun mutum yake ba

shide yasan inhar aka zabe project design dinsa to har abada yay gaba kenan, dan babban advantage na kawo shirin london shine manyan kusosi daga wasa kasashen zasuzo and frm der daga zarar sungan aikinka yamusu kyau toh shikenan kuma contract kam saima ka ture hakama kudi. Dats why alot of cin hanci da politics is involved, shi kuma gashi shi badan siyasa bane kawai dai yabarma Allah komi.

Ata bangaren shema'u ma yaudin kusan wata ranane da taci burinsa finally alhaj shafi'unta ne zaizo ya amshe contract snn Sabuwar rayuwarta dataci burinsa will soon spring into a marvellous reality wayyo dadi.. yau be nemeta bama ita dakanta ta nemesa akan gadon sukayi kusan awa akan gadonsa na hotel yana caccakarta ta baya kamar ya samu jakar bijima. Daga nan suka shirya kansu inkunga shema'u bazakuce yar musulma bace sabida wata arniyar open back shade of blue silk dress ta saka taci heel din hermes me dan karan tsada da jakarsa da ake mai taken hermes birkin jakace yar karama me sosa qashin zuciyar yan gayu, an mata wani irin gyaran gashi dakyar ma ta hakura ta dora turban akanta half way, kwalliyar nan ubansu duk kamar bikinta kawai za'aje.

Wani irin nishadi takeji jin kamar yau rana ne da babban burinta na rayuwa zai cika kamar sauraniya haka suka fito tare da alaji shaf sukaje filin jirgi yakaisu birnin london koina zai shiga tana tare dashi.
Chapter 171 · 0% Book details