← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 312

Sashe 201

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga isar su Hotel din
Suka rage kayan jikinsu
Izuwa casual wear suka yi booking table a daya daga cikin restaurant din suka ci abinci suka koshi snn kowa yaje shiryawa event din zai fara 10 am kwana biyu kawai zasuyi dan haka babu wani bata lokaci security sun gama aligning kansu duka kafin nan larabawa su iso dukka manyan kasa da ke da hannu acikin huldan sun hallara anata shige da fice.

Halisa bata wani bata lkcinta wajen shiri ba amma tay kyau matuka acikin wata pret a poter collection na kmfnin saint laurent data saka ajikinta yay mata cas cas

wani irin calm burgendry colour flowing gown ne kayan, me fallen neck, ta kama sumanta in a old school house wive style daya sata looking classy mature and wealthy da feline eye shape saidan dry peach lip da tay wearing to make her look natural and friendly. 15 min after 10 ta fito ta samu khaleel a kofarta yana jeka ka dawo har ya gama shiri yanata jiranta gashi ta saka wayarta a DND bajinshi tay ba sabida jarabar jasmine dan itama yau din zata shigo nigeria for her traditonal weding preparation..

..tana fitowa ta karemai kallo tana murmushi he look hot and gentle barinma dayay scrping kan shi da wata haddaen askin data saka shi yay looking soo fresh And younger in his all black girgio armani slim fit suit,
She is here to support him no matter what kamar yadda shima ya tsaya mata a lkcin da ta samu babban cigaba. tana daga gefen sa har suka isa hall din anata daukar camera da hoto idon kowa nakansu dan shigarsa da nata ya zamana yana mugun daukar ido sabida all black ya saka ita kuma calm burgendry ga wani classy Heels din datake takawa daidai akai me shegen kyau da kuma tsini....their simple and captivating dress sense yasaka duk inda suka ratsa sai kaga mutane ana son kulasu.

Halisa Tadan sassan manyan mutane dedeku awajen wnda She can chat with while khaleel yana dan bada hanklinsa ma ogansa Dr Aseem dake tare da larabawan tunda suka iso. Strict oder Dr aseem din ya bashi akan karda su yadda subar hotel din shida halisa musmn ma ganin yadda Dr khalid da ogansa suke hankare da su awajen sosai.

wani irin decoration na kece raini aka ma Wajen cos gaba ki daya jamaar dake cikin hall din mood dinsu is screaming with wealth and class.

Team din investors na larabawan sunkai 8 da suka zo Ana fara progrm din daya bayan daya aka introducing dinsu kafin nan aka zazzauna.

Yau din ma ya zamana musu kamar rana ne na bude fagen wasa dan haka akayi nishadi aka san juna aka ci abinci akayi permorfance kala kala snn akayi long lectures Akan topic kamr su depression mental illnesses da cutakan kwakwala kala kala tun 10 din nan suke abu daya har saida aka kai wajen shida na yamma cur snn aka tashi me gabaki daya.

Later by nine pm haka aka sake canja shiga aka sake haduwa duka wajen dinner nanma duk wani muhimman abubuwan da project din ya kunsa shi aketa fayyacewa masu making contact da netwking duk anan aka dinga zancen business wani bin khaleel da kyar yake iya jure ganin inda maza ke bawa halisa dinshi attention musmn ma inta kama na zancen harkan business ne.. Wani bin in kishi ya damesa haka zasuyi chicken fight dinsu su sake shiryawa atake but its all in his favour dan tamkar nuna nasa hanya takeyi na yadda ake bude hanya na gina tsaftaciyar alakar kasuwanci da sabbin fuskoki.

Sai wajajn 1am na dare ya rakata room dinta har saida tay bacci snn ya dawo nasa room din ya kwanta, bayan yay waya da mum dinsa still ya kira meenal yaji wayarta kashe na maman tan ma haka Dake ya gaji kawai saiya kyalesu yay bacci.

ranar gabaki daya wanda suke neman meenal da mahaifyarta basu same su ba dan kuwa tunda aka fidda result na caca Meenal din take asibiti an sankama mata ingin taya nunfashi ko motsi bata farayi ba tukuna acikin matsancin tashin hankli mahaifyarta hjy nadiya da mutanen ta suka bazama gari neman American guy din da ya nuna musu hanya wato don james don su ji yadda akayi kudinsu ya salwance gabaki daya dan ko kashi 3% basu gama samu aciki ba.

acikin daren abubuwa dayawa sun faru masu ban mamaki, fannin khaleel kuwa mutane dayawa suna ta zagawa tabaya suna neman hanyar samun contrct din kota halin kaka ne. su Dr khalid ne agaba a wanm harkan dan sunzo da shirin su ne sosai na bribe harda charms da suka karbo daga wajen bokaye. Haka akata drama acikin daren
tsakaninsu da Dr Aseem dake shima kansa a bude yake duk yasan hakan zai iya faruwa shima sosai ya shirya musu sei sun turu alburushan tsafin su akan khaleel sai ya maida musu abunsu hakan suka kasance duka basu yi bacci ba.

Sassafe tun ba a kira asuba ba ya zo ta tayar da khaleel abacci yace masa maza ya shirya akan lokci larabawn sun ce shine zaiyi delivering lecture na yau dake ma yau za'a karkare hidiman 10 am to 2 na rana za'a tashi dan kowa ya koma destination dinsa akan
Lkci. Kusan dukansu da suka fafatan da anxiety suka farka kowa na fargaban shine ko ba shi bane...kusan ma fargaban da khaleel yakeji aransa yafi na kowa duba da shine zai magana yau agaban dumbin mutanen nan batare da ya shiryawa hakan aransa ba shikan sa besan wasu daga cikin larabawan are dyieng to meet him ba

Badon komi ba saidan video dinsa da suka kalla wancan karon da aka kai musu da niyyar bata shi and now alot of them are earger to have him on the team already.

Bayan yay sallah yay yan adduoinsa yakira maman sa sukay magana ta kwantar masa da hankli Tasaka masa albarka but still yanajin dar dar aransa Haka yay wanka tin 8am snn ya taso Halisa daga bacci tazo room dinsan ta zauna tare dashi tana dan karama masa karfin giwa anan sukayi break fast basu fita koina ba.

9:Am ta fara taya shi karasa shirinsa tana daura masa tie tana ce masa ya kwantarsa hanklinsa dan yau ko bashine ya samu ba, it doesnt matter cos he did his best and he was highly noticed hakan ma wani babban achivement ne... Kalaman nata haka suka dinga rage masa anxiety hade da kalmn hasbiyllahu wa neemal wakeel da lahaula wala kuwwa illa billa dayakeyi a zuciyansa every minutes.

Irin designer din da zata saka shima ya saka ajikinshi watch da shoes da suit duka na hermes da True blue men suit. Da farar shirt aciki, within 30 min itama taje ta shirya ta fito tay nude make up me shiny nude lips ta saka eye lens dark brown daya kusan sauya mata kamanin izuwa na wata halittan da ido bai saba gani ba, sanye da black abayan da mumynsa ta bata me stones and crystals ya mata wani irin azaban kyau sabida rolling kanta datay da mayafin takillace sumanta duka aciki akaro na farko kenan a rayuwanta dataji kanta kirif koina ajikinta a rufe.

haka Ta fito tana baza ssnyar qamshin humran qamutse da turarenta na rebel by rihanna, ta rike wata mini classy bag
Me taken constance daga kamfanin hermes hade da shoes dinsa da abun wuya da agogon dake hannunta duka na diamonds ne.

Duk yawan anxiety dake damunsa daya ganta ahaka ta fito tamkar balarabiya sai dayaji zuciyarsa ta narke ta zama tamkar kankara.

tun anan ya fara jin kamar bazai iya juran jiran lkcin da zai furta mata sirrikan dake boye a cikin zuciyarsa ba halisa is simply a goddess in his heart and eyes, yanayinta na rigima da shagwaba da jan ajin datake janshi aciki tini ya saka shi ya mance duk wata tsoro dake damun ransa yanajin kamr dik duniya babu wanda zai kaishi cin sa'ar mata.

Suka shigo hall din kusan idon kowa nakansu har da larabawan ma ba'a barsu abaya ba dan wani compliment din ma kamr poem suke mata in suka fadeshi da larabci sai khaleel ya dan fasara mata take ganewa..

Bayan dan bayanai na gabatarwa nan Aka saka katon projector khaleel ya hau kan step yana lecturing akan ilimin pyschology halisa tana masa video da phone dinta su Dr khalid ana gefe ana jiran juju yay aiki.

Tun Daga wajajen
11am khaleel ya fara lectures har izuwa karfe 12:30Am dede inda waje ya dauka da tafi. Lkcin Dr khalid kamar zasu mutu haka suka dingaji har khaleel ya dawo wajen zamansa nan aka fara refrshmnt, Babban host na event din suka dan bada jawabai akan abun da khaleel yay. Kai tsaye aka fara kiran sunayen wanda sukayi gasar daya bayan daya ana basu takardan karramawa da golden recognition kowa da position dinsa ajiki tare da cheque na kudi kimanin 70 million naira for each, And nobody dare to question Arab money dan kowa yasan wnn din kmr chicken change ne agaresu.

acikin su shidan da sukayi participating mutane hudu kawai aka kira kan stage aka basu wann karramawar wanda tun anan suka san cewa badasu za'a je gaba ba sedei kudaden da suka samu na karrmawar wasu tuni ya wanke musu zuciya. Lkcin zufa kawai dr khalid yakeyi daga wajen zamansaa ganin ba akira sunansa ba amma kuma bai wani damu ba dayaga khaleel ma ba'a kirashi saman stage ba.

Khaleel Shine da Abun amma kirjin halisa ya buga yafi sau tamanin
Hannunta ya rike anashi ganin she is soo nervous
Shima naji aransa amma bai wani damu ba babban burinsa shine Inde har zata amince ta aure shi suyi rayuwan su me dadi it wud have been his biggest achievement in his life.
Chapter 201 · 0% Book details