← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 214 OF 312

Sashe 214

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har dare suna gidan Halisa na kwance a dakin maryam suna hirar atamfa Halisa tanason ta dinkasu dan bata da atamfa acikin kayanta ko guda daya itadai designer english wear da materials kawai ta saba sakawa..sunata hiran irin haka..daga sashen kasa kuwa iyayen khaleel ne suka sako sa tsakiya da maganan halisan. Tun a wasa wasa suka fara mishi har babansa ya fito kai tsaye yace masa baison yanayin shakuwar su ahaka, ya fiso ya bayyana niyyarsa kawai suyi aure dan kar wata fitina tazo ta shiga tsakaninsu. Tun da aka fara warware maganan kunya yasa bai musu cikakken bayani ba har sai washe gari da sukaje masallaci babansa yake tambayarsa game da asalin halisan nan ya zauna ya fayyace masa abunda ake ciki, nan ma ya masa nasiha akanta
Sann yace masa inda gaske yake yana so aurenta toh ya tabbata sun sassanta kansu nan da sati guda shima zai yi nashi binciken yagani.

tun bayan nan khaleel ya rasa nitsuwa aransa yasani sarai babansa bazai sake waiwayan sa ba saida maganan aure dan haka dolensa ne ya bayyana ma halisa batun auren da wuri karma azo
asamu wani tashin hankli.

a fannin halisan kuwa bata gane abunda ake ciki agidan ba itade tasan maryam tana mata
Wasan inlaw inlaw saidai tay murmushi.

Cikin week din suna daan zuwa office sama sama dake shidin hutu yakeyi so agidansu yake kwana ita kuma wani bin agidan meenal din take kwana ita kadai wani bi kuma ta kwana tare da maryam.

Tana shirin auren jasmine at same time in khaleel yazo hira suna shirin excuting din wasu plans dinsa dake yana da babban gidansa nakansa a ikoyi wanda yakeyin shi bai karasa ba sabida plan din yana bukatar kudi masu yawa kuma alkcin baidashi. Yanxu da kudi yazo Shida halisa suka tsara abunsu to their taste, duk da ma yasan bazama zasu nayi agidan ba tunda aikin sa na saudi arabia ynxu but after 15yrs zasu dawo lagos ne me gabaku daya, halisa's company is here zata iya lekowa, ga kuma hutu da ziyara Yasan dolene suna dawowa hutu da ganin gida. Duk wann shirin aransa kawai yay bai sako halisa aciki ba hakama plan din gidansa ma lagos da zaman sa a sudiya da ita kawai yay bai sako meenal aciki ba

Badon komi ba saidan yasan yawan ego da girman kan meenal infact she wll neva want to move in with him shiyasa ma ta siya gidanta tace lallai anatan za'a zauna, yasan kuma bazata taɓa ta bar kamfaninta datake mugun ji dashi anan nigeria tabishi wani kasa dan raya sunnan aure.

shiyasa baima bata lokacinsa ya sakata acikin plans dinsa ba da halisan dayasan tasan darajarshi ya tsara rayuwarsa yabi ya fuske abunsa.

*******

Ata dayan bangaren hajiya nadiya ta amsa wayar alfah tana kuka ta zayyana masa dukkan abunda suke ciki alfah yace mata duk ya hango shiyasa ya kirata dan ya bata mafita.

Kai tsaye yace mata ta daga meenal daga asibitin los angeles su dawo nigeria su karasa jinyan anan, yace mata ta kwantar sa hanklinta zai yi tunaani zai nema mata mafita.

Iyakar wann maganan ne kawai ya nitsar da hjya nadiya,meenal na cikin wani hali na tsakanin rai da mutuwa haka ta daga bori aka bata yarta dan sauran canjin dake acct dinta tay booking emergency plan aka dawo dasu nigeria direct aka ajeta a babban asibiti a abuja.

Suna isowa Bayan kwana biyu Alfa ya fara zuwa asibitin yana bata wani ruwa tana ma meenal wanka dashi halin da ake ciki shine yace mata yau cikin dare meenal zata farka.

Tana zauna cikin tsammanin haka tafara tunanin me zatace ma meenal din inta farka,
Haka ta rarumi jakarta ta fita neman shawara wajen wata hamshakiyar kawarta da halinsu yake kusan daya awajen maitar son kudi da bin harkan banza, wancan karon sanadiyarta suka fara kkrin shiga arab contact na su khaleel dataga abun na masu ilimi me sai ta fice tabu caca tabar kawartan aciki.

tana zuwa gidanta ta fashe da kuka ta fara complain tana zuba mata raki akan abunda ya same yarta meenal, matar ita ta dauki waya ta nuna mata komi yadda abubuwa suka kaya tace mata toh ai Mijin meenal dinne ma ya samu wnn kwangilar jiki na bari bari kamar mazari hajya nadiya ta bude wayarta ta dudduba harta zakalo hidiman a website ta gaggani, hotunan khaleel a website din kala kala ga halisa agefensa take idonta yay jajuzir da wutar kishi take tafara hauhuwam numfashi tana huci tana hawa tana kuma dabur dabur cikin matsanamcin rudewa da kuma mamakin ganin wai khaleel ne yaci

matar Kuwa tasha matukar mamaki dataji wai basu ma sani ba tace ke kuwa nadiya mijin yarki yay wann uban kudin hae kyazo kina kukan kudi awani waje??? Ai tashin yarki zakiyi taje taci arziki,dan wallh wallh zai iya biyan mata basukanta tass sann ya rubin rubanyar abunda ta rasa batare da yaji komi aransa ba ke kinsan uban kudin da zai samu kuwa? To shekara 15 zaiyi acan kumaa sun bashi wani hadadden king size mansion ga babu abunda babu aciki wallhi...matar na bata labari, Hajiya nadiya sai ɓari kawai jikinta yakeyi
Tana cewa banci ta zama ba, banci ta zama ba kai banci ta zama ba
ruwan da matar ta kawo mata bata ko sha ba ta rarumi jakarta a hannu ta koma asibiti ta zauna ta kira wnn ta kira wann duk inda tasan zata samu information akan kudin khaleel saida ta kira taji

jeka ka dawo ta dinga har Gani take kamar lkci bazaiyi da meenal dinta ta farka suje suci arzikin khaleel ba...Alhamdullhi gani take babban mafita ce ta zo musu...kuyi hakuri da typing errors
Na kudi ne to join chat 08060712446Da wani irin zumudi game da tarin munafurci aranta ta zauna ko sallah batay yau ba bare ya dameta, saiyau take tuna cewa dama can Alfanta ya taba gaya mata cewa khaleel yana da qashin arziki shisa ma tadan danne zuciyarta tabar yarta take zaune dashi duk dama bawai ta gama amincewa da hakan ba ne aranta toh gashi kuwa kamar yankan wuka maganan alfah ya fara zamowa gaskiya..

Babu kalar lissafin da baizo kwakwalrta yau ba ta rasa ya zatay,shin da baqin cikin ganin Halisa kane kane tare da mijin yarta ne koko da labarin dake yawo akanta na samun arzikin khaleel.

Evrything is just hitting her brain at once tarasa ta inda zata aje zuciyarta

gashi Acikin mutanen data kikkkira a kasar waje wani mutum ya ce mata Ai nan gaba ma sai sunyi dagaske kafin nan su saka Khaleel a idonsu dan wnn huldan nasa da larabawa will surely make him famous, su acan kullum cigaba suke karawa, gashi medical field dinsa ba irin me too much competition din nan bane bare ace zai sauka da wuri, a iya harsashensa shi gani yake nan gaba khaleel will be invited to all these advanced countries ganinsa zai zamo daga wane sai wane in basuyi wasa ba.

Duk damuwarta shine matsayin yarta awajensa yanxu, duba da ta fi kowa sanin duk wani tijara da mugayen abubuwan da meenal take masa. gashi bata ma kawo maganan kai kukansu wajen Alfah dan a mallake musu zuciyar khaleel akan yarta tanata jin tsoron karya alfah bijiro mata da maganan kwana da yarta meenal, tasan ma da wuyane meenal ta iya daukar jarabarsa tunda tana complain akan dick din mijinta to tabbas tsn bazata iya daukar na alfa ba snn ko mutuwa za'ayi meenal din ma bazata yarda da hakan ba...

she just have to find another way..dolene yarta ta zama shugaba ta kuma samu waje awajen juya arzikin khaleel, toh wayasan ma itama akaita can saudi arabia ta zauna acan tare dasu,snn taci arziki dama kuma babban burinta ne ta auri balarabe me kudi tay rayuwarta cikin jin dadi.

gabaki daya Tagama saƙa abubuwa dayawa aranta game da samun kudin khaleel tanata Allah Allah meenal ta farka su san me zasuyi..

ata Wani bangaren zuciyarta kuwa a tafashe yake da hidimar halisa kullum baqin ciki takeji aranta inta tuna Alfah yace kar dasu yadda su taba halisa tsaki taja me tsayi aranta tace Aikuwa ko mayyace ke halisa lkcin rabuwarki da yata yazo kenan, bazaki ma rabeta ba bare kiyi tunanin cin arziki.. cikin tsananin kwadayi da bure tare da kulla mugayen abubuwa aranta ta wuni, duk ta kasa nutsuwa Tana jin kamar dare bazaiyi meenal ta farka ba.

Haka tana zaune batay bacci ba tayita jira har tsakar dare lokcin da Alfah yace mata meenal zata farka dan ita bata yadda da maganan ubangiji kamar yadda ta mugun yadda da maganan Alfahnta ba

Acikin mugun zakuwa take kallon meenal tana kuma kallon agogo time to time haka zataje ta tattabata tana cewa haba Amina haba Amina ki tashi mana haka kusan kwananki shida kina kwance sai kace bani na haifeki ba..Ki tashi kawai Allah ya fito mana da wata babban mafita, Amina mijinki ya kudance kakanmu ta yanke saƙa. Evry now and den sai taje ta tashe ta da ire iren wnm kalaman amma har asubuh ya rufa aka doshi safiya meenal bata motsa ba.

dataga an doshi safiya ba wani motsi sai taji Hanklinta ya dada mugun tashi, haka ta sake fita kofa ta kira alfa da kyar ya dauki wayar yana amsawa ta fashe masa da kuka tanamai ce masa ita batagane komi ba meenal bata farka ba haryanzu ba..

tana cikin sauraransa yana magana Can ta shaƙo sautin meenal din abayanta, tana farkawa ta fara ihu tana cewa wayyo wayyo wayyo kudi na Kudina wayyo na shiga uku na na lalace wayyo wayyo Mummy mummy mummy kudi naaa wayyo kudinaaaa

A birkice hajiya nadiya ta katse wayar ko sallama batama alfahn ba ta bankade kofar ta shigo cikin dakin da sauri ta rungume meenal ajikinta tana cewa Alhamdullh Amina ta farka Allah na gode maka..meenal kuwa sai ihu take tana cewa kudina kudina kudina..tamkar yadda ta suma haka ta tashi ta cigaba da bori da zage zage tana ihun kudinta kamar tababbiya.

Da kyar da wuya hjy nadiya ta shawo kanta ahakan ma saida ta talla mata mari me karfi kafin nan ta samu ta iya nitsar da ita tayi shiru.
Chapter 214 · 0% Book details