← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 312

Sashe 165

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anxiety data ganji yasaka period dinta yazo mata da yawa kuma bazata tana cikin wnn yanayin iarnnd 11pm in the night sai ga hajiya binta da waya tana zuwa ta dan makela mata a kunne..
Tace yi magana Mahmud ne, gabanta taji yadan fado ta dan mike zaune,

Sai yanzu ta tuno ashe dazun hjy binta tace mata mahmud ya aje mata kudaden kashewa da duk dan abunda take bukata tasan lallaine sai tayi masa godiya..

Dan shiru tayi har saida hajya tabar dakin snn tay masa sallama tace Ina wuni jin bai amsa ba tayi saurin cike gaisuwar da yaya mahmud din

Kamar yana jira ta cikan kuwa Yace lpya ya schl din tace fine alhamdull
Tace dama ..uhmmm cewa zanyi nagode..

Sai da ya lumshe ido yana jiwo uneseness dake tafiya da nufashin ta snn Yace ok bazaki tambaye ni na isa lpya ba? Batasan sanda ta dan shagwabe murya kamar zatayi kuka ba tace kayi hakuri tayi shiru kadan can tace ka isa lpya? Yana murmushi Yace "Lafiya, but im tired zan yi bacci, i wll call you back again ko..Ta gyada kai tare da cewa uhmmm itama..Yace toh gud nit.
tace ba waya ta bane zan kai mata ..yace ok me nace, tace kace gudnite
..dama abunda yake jira tace masa kenan yay karamin murmushi Ya katse wayarsa..kallon wayar tadingayi can sann ta yi murmushi me sanyi ta tashi da kyar ta kaiwa hajiya binta wayarta a daki.

Bayan nan bai sake kiransu ba dan har dan zazzabin kwana biyun nan sai da tayi bata fara zuwa schl ba sai da tay 2 days snn ta dawo normal
da activities dinta.

*********

Ata dayan bangaren kuwa rayuwar victoria da secret boss dinta Kayden ya sauya gabaki daya ya zamo wani abu daban duba da yanzun bata da wani sauran shauki akan mijinta femi, rayuwarta kawai take zubawa ta inda zai kawo mata farinciki da nishadi shiyasa ma bata damu da komi ba.

Tun bayan abunda ya faru tsakaninta da femi data zo ta nitsu they had a deep conversation da kayden a chat ranar tun da yamma suka fara magana har tsakiyar dare and its all about ther lives, irin dai random hira na rayuwa, saidai she was suprise dataji yadda ya nitsu har ya fahimce kalmominta ya gano wasu matsalartan lkci guda kamar yadda take fama da boyayyar depression da kuma lonelines da wnn weight din betrayal din dake zucyarta da femi ya lakaba matashi...

He ask to be her friend officially. They spend time talking abt it, kafin nan tazo ta amince, so After she accepted.. in the morning irin da sassafen nan aka buga musu gate then she got a huge gift of bonquet of gifts with dollars in it frm him.

wani irin kinky and petty soyayyar gayu masu kudi da bata taɓa tsammanin a age dinta zata samu irinshi ba ta soma gani..

Sosai hakan yake sace mata zuciya dan wani abun yana sakata taji kanta so young and special, tana ganin gift din ta turomai sako, the conversations start with banters, a wasa Ya fara gaya mata how he can spend on her..

Duk ta dauka wasan ne face saida ta soma ganin yaana mata abubuwa a zahiri kawai abunda yake katse mata jn dadin nata shine da haryau bata san shi a fuska ko taji muryansa ba.

He startrd to give her alot of attention to the point that tafara amincewa dashi, inta tuna baqin cikin femi tasha giya ranar toh she will tell him her marital issures few of it, She ask him weda he gats a girl yace mata da batay aure ba she wll be his first girl kuma be damu yanxu ba If she wll like to date him..

Batadai bashi cikakken green light ba amma bakaramin shakuwa sukayi da junansu ba dan kuwa fiye da yadda femi yakan iya kashe mata kudi shima hakanan yake spoilng nata da kudi sedei nashi salon daban ne, dan kuwa ko awasa tace tana son abu toh washe gari zai aiko mata dashi komim girmansa gashi bei taba kuskuren tambayarta nudes dinta ko wani abu na zubar da mutunci da zai nuna alaman yaudararta yake sonyi ba.

Tun bayan rabuwarta da femi rayuwarta yay wani irin dadi da sauki, they are engrossed soo much in love bombing. Yana ta son ya bayyana mata kansa sarari amma kuma yana tsoron ko kawai tana bashi lkci snn ta na nuna mai soyayyan ne dan ta rasa mijinta femi,

Hakan yasakashi cikin damuwa dan baison garin bayyana mata kansa yazo ya rasata na har Abada, daga karshe wajen baban sa ya nemo shawara dake baiya boye ma baban nasa komi baban yace masa hanya daya kawai ake gane soyayyar mace according to the law of phsycology and human nature, idan kana son kasan mutum yana sonka da gaske ko baya sonka, kabari sai kuna tsaka da soyayya sai ka janye komi ya neme ka ya rasa for sumtimes shikansa he wll figure it out weda the feelinng is true or not and wat is meant to be wll alwys be.

Baida choice hakan yabiye ta babanshi, dan yana matukar kaunar yaga ya bayyana mata kansa akan lkco, Saida ya bari shakuwar tasu ya shigeta sosai then he disapper until she felt it so badly,.. yau kusan sati guda kenan babushi kuma har yanzu bata san inda zataji labarinsa ko ta samesa ba hakan yasaka bakaramin cikin damuwa vicky ta shiga ciki ba.

***************

Bangaren Femi kuwa tun bayan rabuwarsa da vickyn baida wani abun yi sai dai yaje shi gidan abokai ko yaje wajen chief okoro, yana gama yawace yawancensa ya dawo lagos ya sauka a gidan nile yay shame shame yana foaming sickness, haka zaita ɓari yana birgima da dare ana rireikkiesa kamar me jariran aljannu just to sleep in his room domim ya samu daman taba mai jiki, and hugging him in the name of high fever

abun ya fara isan Nile ranar ya tashi da safe ya bashi drugs da tea yace masa lallai suje asibiti kawai a dubasa ko akai sa therapy. Femi najin haka ya susuce a Take take ya sauya fuska ya fara kawo wata magana na daban, saying he just wants him to be free with him, saidai duk iya dadin bakinsa bai ganekan nile din ba he even tried spending several wknds exposing himself to him amma shiru harya gaji ya fara jan abokinsa lucio ajikinshi sosai a tunanin sa in suka saka lucio a harkan zai musu saukin jawo nile ciki... If u dindt see me pls dont panick is a busy week ahead.#SURAYYAHMS

Montcalm royal london house 5-star luxury hotel ne dake zaune daram a tsakiyar garin united kingdom Kusa da filin finsbury square wanda daga nan kuma tafiya kadan zakayi ya kaika har cikin moorgate underground station.

Wajajen motsa jiki, dakin gyaran fata da wajajen shakatawa dana cin abinci kai hatta rooftop restaurant akwai wann hamshakin hotel din.

Kimanin Dalar amurka dari biyu zuwa dari uku ake kashewa akan kowani kwana daya tal wanda a kudin najeria ta yanxu zai kama kusan Dubu dari uku zuwa dubu dariya biyar wanda badon komi ake biyan wnn maqudan kudin ba sai dan sabida harkallan su ta manyace, suna da stylish bedrooms dinsu na zamani da abubuwan dake ciki na more rayuwa

Yau watan shema'u biyu kenan a wann kasar amma acikin wann hamshakin hotel din take zama tana baza life tana kuma holewa, shiyasa koda acikin wasa bata taɓajin tana son ta kalle baya ba bare ma ta tuno da wani abu waishi auren mahmud dake yawo akanta.

Kusan dukkan wani abunda take so a duniyarta ta sameshi wajen saurayinta ALHAJ shafiu, Ga soyayya, ga ruwan kudi ga rayuwa mai cike da kyale kyalen duniya azagaye da ita, kusan babu abunda takeyi anan kasar face juyi cikin nishadi da more rayuwa cikin jin dadi....

kullum suna tare dashi suna holewa suna kuma yawon bude ido agari izuwa yanxu shemau ta masifar amincewa dashi dari bisa dari sabida duk tsananin soyayyar nan tasu basu taɓa kaiwa ga yin wata harkallan sex tsakaninsu ba saidai ayi taɓe taɓe da shafe shafe.

Saidai tun bayan sallah
Abubuwa suka fara sauya musu dake an riga an saka ranar gabatar da contract previews din da suka ci burinsa a london wanda tamkar birni ne a cikin UK din da suke zaune acikin ynxu.

Tunda aka fara wann shirye shiryen shema'u take cikin yanayin ɓarin jiki da zumudi dan kuwa alhaj shafiun nata yariga yagaya mata cewa tasha kuruminta ta cigaba da hutawa kusan komi shi zai musu in maqudan kudin ya sauko kuma hamshakin aure zasuyi kalar wanda ba ataba irinsa a nigeria ba snn ya maidata sarauniya.

Alkwawuran kyale kyalen duniya da mutumin yay mata izuwa yanxu ita kanta bazata iya tunowa da wasunsu ba, bakomi ke rudarta ba face sake mata kudaden dayake yi tana danashanta dasu kamar wanda baison su.

Yanayin yadda rayuwa ya kasance musu kenan har izuwa yanxu da sauran baqi suka soma hallarowa domin fafatawa.

Acikin baqin kuwa har da mijinta mahmud daya iso kasar london din da wuri ya kama hotel dinsa kusa da inda za'ayi hidimar ita kuma da saurayinta suna can UK ranar gasar suke saka ran tahowa filin gabatarwa.

Tunda ya kasance musu saura sati hudu aje filin gabatar da project saiya zamto kowani enginer da dan siyasa kansa ya dau dumi babu lkcin wasa ita kanta shema'un ynxu holewarta kawai take ita kadai dan bata fiye samun lkcin alhaj shafiu a wayann kwanakin ba.

All her tots was yana musu shige da fice ne dan kominsu ya zo musu da sauki gashi yace zai sakata acikin harkan idan komi ya samu tazo hannunshi, tun zuwan su nan ya tabbatar mata da cewa babu tantama shine zai samu wann project din sabida kaf mutanensa nacikin alkalan hidima Hankllinta a mugun kwance take rayuwa aganinta rana kawai suke jira da zaa damka musu project din a hannunsu babu wani tantama tsabr ta aminta dashi ko sau daya bata taɓa duba jerin sauran engners din ba bare ma tasan ko mahmud zai samu shiga ciki.
Chapter 165 · 0% Book details