← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 312

Sashe 154

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jawo kwalin yay gabansa snn yace i wil send u the money in na isa office ynxu. Tace toh
tare da bude masa dayan madaidaicin kwalin wasu mahaukatan azurfa rings ne aciki an dora shiny black diamond stone a tsakiyarsu daya na mace daya na namiji tace ibrahim take a look at this gorgeus twin rings
Na siya mana ne a india nida dad dinka, toh ashe ba size din mu bane duk na rasa me zanyi dasu gashi customised ce mani kadai aka kera wann design din.

Idonsa nakan ring din yana murmushi kai tsaye yace 'its so precious kam, can u sell it? Tace hmm nifa yar kasuwace malam in kudina zai dawo ai shikenan kaga sai natura musu asake mana wani irinsa..yace hmm how much? Tace arnd 7 million each inna rage. Yace toh kibarmun
Amma bayau zan tura maki kudin ba na jewries din kawai zan tura maki..

Takasa hakuri Tana dan murmushi tace masa are u buying it for ur wife? Yace "the ring? No, nima ajiyewa zanyi. Ajiyar zuciya ta sauke tace i don't mean to sound sunhow amma inkasaan
ma ita zaka bama ring dina ajemin zan tura maka design ka zaba a muku naku tacan amma ba design dina ba kama

Dariya yay yace toh bakince nayi aure ba, who knws i am going to keep it for dat moment...

hannunshi data rike ya dora hannunsa akai yana cewa ina sane da request dinki maama na, and i wll make sure i make u proud. Wani irin dadi taji aranta tace Allah yay maka albarka ibrahim yana murmushi yace Ameen, daga nan sai baice komi ba tanata kallonshi har ta kyabe bakinta cikin murmushi muje kasa toh lets go and see what is happening...

Bai mata musu ba suka fito atare snn suka doshi hanyar babban falon su, babu kowa aciki nan suka wuce har sama sashen mahaifinsa.

Lkcin su halisa suna zaune a falonsa da sun zo sun samu ne har yanzu baima fito daga inner room dinsa ba, isowar sun kenan bada jimawa ba sai gashi nan shima ya fito,wani irin bugaggiyar farar shadda ce ajikinsa ya rufe ta da alkyabba baki me design din dinkin zaren hannu bakaramin kyau yay da nadin shiwag din kansa ba. Sai satar kallonsa take dna bakaramin kama suke mata khaleel a yanayin siffar jiki ba, Sassanyar qamshin arabian perf dinsa me ya baza wajen, halisa da maryam da kuma aliyu suka mike tsaye har ya karaso, kallo dadda daya yamusu fuska ba yabo ba fallasa yace "ina fatan lafya dai ko? cikin ladabi Maryam tace uhmm Baaba dama Halisa ce tazo zata gaishe ka. Yay karamin murmushi toh toh, waje ya nema ya zauna acikin nutsuwa
..nan halisa ta dan karaso daf dashi tsaf ya kare ma shigartata kallo tana tsugunawa da sanyin murya tace "good morning sir! Fuska babu yabo ba fallasa yace "morning. Kin zo lfya?
Tace lfya kalau, ure highly welcome to the house pls have a seat

Duk dama tana jin shakkarsa amma bata tsorata ba ta mike a nitse ta zauna akan kujerar dayay mata nuni dashi.

ya kalle maryam a dan dake snn yace "break fast"..Maryam tana juyawa, Aliyu ya nemi waje ya zauna yana jin me suke cewa, cike da muryan tausayawa yace ma halisan "ya hakuri kuma? Kanta na dan kallon kasa cikin kirkiran murmushi tace masa Alhamdullh sir. dan shiru ne ya gifta wajen kafin nan ya fara shigarta da sanyayan nasihu masu shiga jiki duk dan gameda abunda ya faru yanamai kara mata karfin gwiwa akan tay hakuri da rayuwa, cos life is not alwys going to be fair with a good souls, dole ne sai ta daure and he asked her to continue being a good lady ta cigaba tsaftace hanyar samunta abunka da malami yanayi yana jawo mata aya da turanci itako bakaramin burgeta taji mutumin yay ba

Yana cikin mata nasihar maryam ta kawo musu sabuwar break fast, ita shayin ma kawai tasha tanamai sauraron dukkn abubuwanda yake cewa sai ganan su khaleel da mum dinsa sun shigo as usual yauma bai wani kulashi ba. Kowa awajen yaji dadin yadda baban nasu ya tarbe halisa suke hiransu cikin nutsuwa anma banda khaleel dayake ganin kamar don kawai tay irin shigar dayake son ne shiyasa yau ya kulata. Aransa yabari cewa his dad jusr want to control evryones life kuma muddin bakayi abunda yake so ba toh shikenan ka zama banza kenan awajensa.

Har halisa ta kammala sallamanta da kuwa suka kama hanyar asibiti bai wani sake fuskarsa ba, badon komi ba sai hirar abunda baban nashi yace mata dataketa meme ta masa wanda harga Allah bason jinsu yakeyi ba. Daga harabar nisa premier hopsital sukay parking nan suka shiga ciki sama can ofishin Dr aseem suka samesa a zaune yana kan waya da arabian contractor nasu. Ganinsu a office din yasaka ya dan katse wayar da fara'ar sa da komi suka gaggaisa, daga irin kallon dayake musu zakasan cewa halisar ce tay masa daban, ya lura cewa kmar
Dabararsa yay daya hadata da khaleel ganin she is looking okay to him Harma fiye dana kowani lkci. Yau kusan agaban khaleel suka tattauna abubuwanda yakamata tayi, she was given permission to go to the office amma under supervision din likitarta sabida haryau report dinsun yanakan analysing triggers dinta ba ason ta kasance cikin hayaniya da taron mutane dayawa atattare da ita.

Tana zaune tana shan coffe agefe taji Dr aseem na ma khaleel bayanin cigaban da suka samu na arab project yama kasa iya boyewa farin cikin sa a fili sabida tin list din sunayen bai fito ba aka turo masa congratularty alert na cewa khaleel is now one of the top listed doctors da zasu iya summiting 10 skilled final test dinsu a website nasu each test za'ana turawa bayan sati bibbiyu har agama dat means nan da wata daya da sati daya kenan zai iya samun contract din ahannunsa in har yaci final test dinsa.

Daga shi har ogan nasa bansan waye yafi wani murna ba Dan kuwa wann fannin baikai wanda yay abaya wuya ba snn baiya bukatar wani munafuncin siyasa, zallan tsagwaron ilimin mutun ke fiddashi, kusan kwararrun likitoci su ashirin suka cika progrm din amma su biyar ne kawai aka zaba frm each region arnd the globe and the only bad news is dr Khaleed shine na biyar din.

Khaleel nata mamaki jin yadda Dr Aseem yake famar fayyace masa irin badakalar da sukayi har suka samu shiga shiga . dan a cewarsa sunyi switching wani null file name na wani likita ne ya dawo kan sunan khalid din wajen verificaficaton sai suka sauya masa ID da kuma suna amma asali sunan khalid din baima fito ba.

halisa batasan kan me suke tattaunawa ba amma yadda taga khaleel da ogansu suka dulmuya cikin farinciki da annashuwa yasaka tagane cewa abun me muhimmacine agaresu sosai..

The man is very much confident in him tana jin abubuwan dayake gaya masa har abun yana matukar burgeta dan kuwa sosai ta gane cewa Kallon uba Khaleel yakeyi ma Dr Aseeem din, da alama dr Aseem wll move the world to see him excell.. Duk wani kalamai na karin karfin giwa da nuna yadda saida ya gaya masa infact aransa ya gama ajewa khaleel dinsa ne kawai zaici jarabawar wann babban project din.

Tunma ba asaka ranar farawarsu ta farko ba yke ce masa muddin yaci gasar zai wuya ya sake dawowa nigeria he wll just go back to india and rest in his academy snn khaleel yay kkri karya zauna a kasar nan cewar sa makiyansa zasuyi masa yawa akansa.

Shidai khaleel saidai yay Dariya haka aka sha hirar project snn basu gaya mai komi dangane da sabanin da suke samu abaya ba.

wajajen karfe biyu na rana suka fito daga wajen dr aseem lkcin yunwa yafara damun khaleel kai tsaye suka dawo gidan suka samu as usual babu motsin kowa aciki meenal harta cikama rigarta iska tay gaba, ko room dinsu ba suje ba suka tsaya daga kitchen wanda yadda ta barshi hakanan tazo ta same shi. Khaleel yaja kujera ya zauna daga gefen kitchen dinning yana ta suggesting mata abunda zasuci patotes din dayace ta tattaro ta zuba agabansa tay providing dinsa da komi ya nade hannun jumfarsa ya fara tayata ferewa.

Dan kwalin abayan kawai ta cire tana kkrin hada musu liver sauce, jefa jefa suna hira me ban dariya suna kuma planning akan yadda batun zuwanta office di zai kasance tunda shima ga aikin nasa ya taso masa ruwa a jallo.

they came into the conclusion cewa kowani rana zasu na ficewa a mota daya, zai kaita HRM grp of companies itama wata rana zata aje shi a asibiti yay aikinsa anan while she is away, snn in time din tashi yay zaizo ya dauketa, ko ita tazo ta daukesa sai su dawo gida. Dokar shine She is only allow to work till four, snn no meeting is allowd to take her out of the premises batare da sannin hukuma ko likitanta ba. Paid book
08060712446 chat onlyHirar hakan suka dingayi kenan harta kammala soya musu chips da liver sauce snn ta zuba musu a plate daban daban ta hado tare da chilled lemonade suka zauna a mini dinning table na kitchen din suna ci tare...
Chapter 154 · 0% Book details