← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 292 OF 312

Sashe 292

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo kallon sukayi suna hade ido da mumynta sukaga har ya sungume matarsa a hannu halisan tabi ta kankamesa sosai, he look very pissed cikin yin banza da su ya wuce da ita daki direct ya ajeta a bathrum ya dudduba wuyarta inda suka jajja mata wajen haryay jaaa.
ji yay kamr bazai iya hakuri ba, dede tafara aman kenan ya kalleta yace Stay here my love
Ina zuwa kinji..ynxu zanzo..gyada masa kai kawai tay yana ficewa ta tsuguna aman da bata san daga ina ya fito ba ya fara kwazowa cikin toilet daga bakinta kamar ana tuttudosa daga can ciki

Daga falon banda ashariya da manyan manyan zagi babu abunda hjya nadiya take wai ita a dole tana kishi jin halisa tace zatay amai agabansu.

mani za'a gwdawa Barikanci da makirci?? Ayyuriri hehehe wai baby amai nakeji..heheheh halisa ke ar karamar yar iska ce wallh Yar jakar uba yar matsiyata ashawoooooooooo

barrakar huci meenal take cos she doesnt even knw wat dat means bare ya dameta, ita babban damuwarta mijinta ne Allah Allah kawai take taga ya fito dan ji take kamr ma tabishi dakin yanxu dan gani take kamr khaleel nata ne ita kadai.

Suna tsaka da zage zagen sai ganan khaleel ya fito fuskan nasa babu alaman rahama akanta yana waya harya iso daf dasu snn ya sauke wayar

Dankwalin da suka shakewa halisa wuyan ya kalla a hannun hjya nadiya calmy yace "ke kuma hajiya ya da girmanki da hanklinki zakizo har gidana ki shakemin matata tana gidanta me ta miki ne da saikin mata irin wnn hukuncin???.

kafin hjya nadiya ta amsa caraf Meenal ta hayayyako tana cewa bura uban can khaleel ashe baka da kuna uwar waye ce matar taka...

cikin katseta hjya nadiya tace barshi in amsashi tunda dani yayi Marar kunya kawai azzalumi khaleel wallh kabani kunya tunda har zaka iya cin amanan amina da babban kawarta tirrrr wallh kayi kyan banza kyan dan maciji..

fuskansa a dore yace no Ba wann na tambayeki ba.

Tamasa kallon up and down ohh amsa kake jira abakina marar kunya? wurga masa veil din tay a hatsale snn ta ce toh gashi shakureta nayi bakuma tambayata zakayi ba rama mata kawai zakayi domin nasan hakan ya maka zafi.

Kankance idonsa yay akanta sigar rashin mutunci yace "In rama mata fa kikace???

Tace ehhh in uwace ta haifeki ka rama mata

Wani Tasssss taji ya dauketa da mari abazata, zatay magana ya kare wanka mata wani gingimammen mari me kara wanda saida taji kunenta ya dauke ji cakkkkk atake ta zube kasa dafe da kuncinta.....

A ragwabe meenal ta fado kanta cikin razannen murya a mugun rikice tahau cewa mummy mummy innalillahi mummy..ganin mumynta bata ko motsi ta mike tsaye tayo kansa ahaukce cikin kuka da bori ta kawo hannu zata mareshi ya riketa ya watsata gefe tare da mata wani irin kallo mai mugun darsa fargaba

Jikinta na matsancin bari tahau masa ihu yana tsaye yana kallonta kmr wacce bata da hankli

khaleel khaleel khaleel "How dare you, how dare how dare u khaleelll mummyna fa ka mara yanzu in uwarka ce haka zaka mareta mugu kawai azzalumi tsinanne Allah ya isa ma mumyna.

tana kan ihun ta dada Rushewa da kuka ta fado jikin mumytan tana cewa mummy mummy kiyi shiru kidena kuka mummy saina rama maki wallhy bai isa ba ko akan uwar sa ne saina rama maki mummy kiyi shiru kinji azzalumi kawai tsinanne akan wancn tsinanyar karuwarce zaka mare uwata wallh sainga karshenku maye kawai...

hannayensa biyu duka suna aljihu yana kallonsu shide baice dasu uffan ba har Hjya nadiya ta share hawayenta ta mike tsaye a zuciye ta kallesa tace kai yaro kalle ni nan

Cike da rashin kunya tare da bushe idonsa akanta yace waye yaronki hjya ni fa ba danki bane Allah ya sawwake ki haife da kamar ni saidai ki haife ya mace me tabiin hankli irinki kamar Amina. Yo Inbanda shafewar basira ma harke xaki kira kanki uwa..ai daga zarar babba ya zubda girmansa yaro hawa yake ya taka. Ai Yarki nake aure bake ba..so u have no right to lay ur hands on my wife.

a zuciye menal tace Toh ai ba ita ta taba maka karuwarka ba ni ce na taba ta and why must u slap my mum bcos of that akan me..yanzu fa sau biyu kenan kana cin mutuncin uwata akan halisa.... have u not respect?

cikin katseta yace Respect for what? Ke Amina u shud be grateful ure a mad person tonite.

Zatay magana cikin datsar numfashinta yace
"I have heard enuf..ya isa haka..idan masu hankli suna magana marasa hankli bai kamata suna tsoma baki aciki ba ..get back..in an kira likitanki ya baki magani haukar Taki ya lafa u can chip in..

Kasa magana meenal tay cos she have neva feel batterly insulted like ryt now Hawayenta na zuba zirr kamr ruwa tana kallonsa a mugun raunace amma bata iya cemai komi ba sai kuka...

hjya nadiya tace Kaine babban marar hankli ba yata ba...kar ka kuma cewa yata marar hankli
tsinanne kawai butulu
Wallh asiri yata ta rufa maka data aureka.

Calmly yaja tsaki yace ehh ai danta rufa min asirin ne ma yasa kuka laka mata ciwon hauka dan ta zauna dani, ni wallh ban taba ganin mutane masu mugun naci irinku ba. Anyways dats not my prblem now, kece mai hanklin dan haka im going to call my lawyer to press charges on you bazakizo gidana ki attemtping kashemin matana na kyaleki ba

Hajya nadiya ta dada rushewa da kuka ranta na kuna tace kai ibrahim Inkafasa kaini kurkuku ka raina uwarka data haifeka. Dan kutubar babban bura uba...

cikin kyabe baki yace wa iya zubillah... Ban rainatan bane shisa zaki kwana a cell yau da dare ai...inyaso gobe kya musu bayanin uban meyasa kikazo zaki kashe min mata ta..meye hadina dake..ke nake aure ko yarki?..

Juyawa tay with immense frustration and anger ta kalle meenal dake tsaye a kangare tana kuka Amina kina kallonsa yana cimin mutunci amina kinga mijin aure anan? Cike da bakin ciki tace Allah wadai naka ya lalace wallh duk abunda yaron nan yamn kece sanadiya
Haba sai kace shikadai ne namiji a duniya dan iska marar kunya wanda baisan girman babba ba.

Baice mata komi ba ya daga wayarsa zaiyi kira

meenal tay sauri ta rike wayarsan cikin magiya

"khaleel dan Allah karka kaita station pls i beg u dare yay wallh,..kar kai mummyna can wajen, ga mari ka tsinka jaka hba wann wani irin fitina ne haka duk akan halisan

Da mamaki ya kalleta yace ahnnn yaukece me bada hakuri hahaha ashe kinfi hankli acikin yanyin haukarkin.. and why not? "U love ur mum ryt?...

cikin kuka mai tattare da fushi sosai Tace yes god damn it..uban waye baisan darajar uwarsa ba

karamin dariya yay Yace naga ai ure all the same ne. cikin jan tsaki me sauti yace komi naku na yan daba yan ta'adda omo terrorist.. toh ke dah baki da hanklin zan iya miki uzuri akaiki gidan mahaukata kika sake yin yunkurin taba matata Amma ita bazan iya mata wani uzuri ynxu ba sabida da hanklinta..u have to knw dat i love my wife as much as u love ur mum okay? Uwarki bata fi matata ba fa..

zatay magana cikin katseta da harara yace Yanxu abunda zaayi shine ask her not to ever come back here again inkuma kinason ta dawo gidana toh muje na rakaku dakina kubawa matata hakuri...kinga kotu tace muyi zaman lafiya this migh be a begining of it...

A borance meenal tace khaleel karka yadda ka raina min hankli matarkan banza matar kan wofi, toh baza aje abata hakuri ba..uwata tafi karfin ta bata hakuri ka raina kanka danka furta min haka wallj saidai ta mutu inde uwatace zataje ta bata hakuri..
Hartana bari ta karashe maganan a zafafe tana hawaye.

Yace okay toh ask her to leave and never come back to my house. Ga hauka ga dabanci abun zai min yawa anan ai
...Amina make it snapy 'out" or "apologise" karna kira muku security ni sauri nake zan wuce..

Cikeda karayar zuciya hjya nadiya tace Amina
Kibàri kawai zanje na bata hakurin nide wallh bazan barki a hannun wann azzalumin yaro marar imani ba..inna tafi bansan ke me zai miki akan karuwar matarsan ba... ta kalleshi tace Azzalumi marar imani

Yace uhumm duk rashin imani da zalunci na ban kashe kowa ba..u have no idea how i want u two behind bars dadin abun Allah yana kallonku.

Tunda ya fadi musu haka basu kara cewa komi ba suka rungume juna suna kuka daga bisani hjya nadiyan ta kama hanya a mugun fusace tay waje me gadi ya rakata har can gate tana tafiya tana rubuta tex ma lawyrnsu tana karta zage zage dan batama san ina zataje acikin daren nan ba.

Harsaida takai bakin titin anguwan kafin nan taga wani mota yazo ya tsaya agabanta yace mata an aikosa ne ya dauketa yakaita masauki she was desperate and scared duk ta dauƙa lawyernsu ne ya taimaka dan haka batay wani tunani ba ta shiga aka kaita wani hotel me kyau aka bata isasshen masauki tare da lafiyayyen Abinci..

Meeenal Kuwa tun da ta shiga sashenta banda kuka babu abunda takeyi a daki nata, duk ranta ya
Dagule ga kishi na cinta kamar zai hallakata tarasa me zatayi ma halisa ta huce haushi

hjiy ndiya daga can saida taci abinci tadan huta a hotel din snn ta kira lawyernsu tahau maida masa duk abunda ya faru amma shidin ma sai ya bi ya balbalta da buhun masifa yace mata duk wann lfinta ne data ta sakalta meenal dayawa yace Musu sam basuda hakuri, idan kuma tana son cin nasara akan khaleel toh tay kkri ta dinga controling in actions din meenal inba haka ba idan tasake taba halisa tasaka har khaleel yakaisu kara toh case din nan zaizo yà musu wuya.

Haka hr suka rabu zuciya ba dadi bata ma tambayesa akan hotel da motar da aka kaita masaukin datakeci ba
Chapter 292 · 0% Book details