← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 308 OF 312

Sashe 308

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan tunda tafara nakudar taso Allah ya dau ranta Bayan da ta haihun kuma babu abunda takeji face matsanancin nadama da damuwa bata bacci sam ga jaririn ba lafiya dan dan duk sanda ta dau jaririn tagansa xak zak kaman alhaj shafiu ta amayo saita tuna yadda tay rayuwa ta walaknta rayuwarta akan abun duniya da niimar aure wanda duka biyun saida mijinta mahmud ya batasu isasshu bata taba godewa ba, dama can hausawa saida sukace wanda bai gode ma niimar Allah ba zai godewa azabarsa, gashi batay sharar masallaci ba tazo tanayin na kasuwa, bacin zuciya dai shine tabbatacen halakar gangan jikin mutum.

shema Tana cikin damuwar nata rayuwar amma dataga na Meenal batasan sanda ta rushe awajen da kuka ba babu abunda take furtawa sai Allahumma aajirni fiii musibati innnalillih wa inna ilaihi rjin meenal harda tsafi, harda zancen kashe mutum? Lamarin meenal din sosai ya razanata, bibiyar labarin ta dingayi she came to understand that Babban matsalar meenal yafara ne daga mahaifyarta

ranan cikin dare shema tay kuka tay kuka har muryanta saida ya dena fita ba akan komi tay kukan na sai akan nata iyayen.

Ganin Itafa Allah yay mata gata ya bata iyayene na gari da suka tarbiyantar da ita suka nutsar da ita suka nuna mata dede da ba dede ba. Lamarin meenal yasaka shema ta Dada shiga mayucin hali na matsancin kukan nadama da tuba da rokon Allah yafiya da rahama akan abunda tama iyayrnta na cin amana da toxarta.

Ata bangaren su halisa kuwa bayan da aka gama sharia a Washe gari aka shirya uztaz aka kaisa india for advance treatment dake haryanzu bai farfado ba amma yana raye his chances are increasing day by day... Hadiza jasmine kowa dayaga abunda ya faru a kotu duk jikinsa yay sanyi kowa na adduar Allah ya kawo masa sauki anashi rayuwar sabida tun daga kan lamarin shema har izuwa na meenal darasi ne babba ga kowa dan abubuwan da suka fara sun taba rayuwar kusan kowa.

After 6 months
********

Rayuwa ya fara dawowa kowa normal cikin waynn watannin su halisa sunyi tafiye tafiye sunje india dake acan Uztaz ya samu lafiya sukabi suka gaida dr Aseem da famlynsa shima. Snn khaleel ya kaita gidansu a somali tay hutun sati biyu kafin yazo ya tafi da ita saudi arabia suka cigaba da rywan auren su acan dake tana da ciki
Yanzu fadila da Anita ke kulawa business dinta na nigeria after 4 months of complted rest kafin uztaz ya jonasu yanxu sun dawo kmr yan uwan jini da fadila har kafin nan ta wuce spain bakin nata aiki tare da shuaib itama

acikin watanni shidan Kusan watanni hudu masu kyau su halisa sukayi a saudi arabia yana aikinsa acan yana kula da matarsa batare da sun dawo nigeria ba

Ata bangaren su mahmud kuwa kusan bayan haihuwar shema da sati biyu zuwa uku hafsa ta haifa masa da namijin shima aka samai suna muhammad Ameer
Shagali harda mahaifyar
Shema saida tat tattaki daga bauchi tazo taay musu kwana uku akayi komi na suna da ita

Zuwanta ne da suka samu tattaunawa me tsayi da iyayen mahmud suke jin cewa tana neman yarta shemaun amma matsalar kawai shine mahaifin shema
Da haryau bai sauka ba
Saidai tana da yaqinin cewa inta samu shema komi zaiyi sauki.

Haka suka saka ana ta musu adduan Allah ya bayyana musu ita dan duk bincikenta tace musu bata same labari akanta ba.

ata fannin shema Cikin watanni shida da suka shuden banda wahala da kuncin rayuwa babu abunda take cin karo da shi dan tsabar jinyar jaririnta dtakeyi abunda zata saka abakinta ma saida ya gagareta yaron na ciki wata biyar da sati Allah ya amshe abunsa.

Ranar da Abun ya faru da kafafunta ta tako tundaga asibiti da gawan yaronta a kirji ta iso gida ta samu an kulle gidan da kwado..

Hannu ta dora aka hawaye na zuba mata tana furta Allah na tuba Allah na tuba kukan datakeyi yahaeo hanklin nebonta yafoto ya bata takardan cewa me gidan ne yace mata ta tafi ga kayanta ma ya aje mata su.

Haka ta amshi takardan babu yadda zatay ta goyo gawan yaron ta fita neman wanda zasu tayata a binneshi.

Tana tafiya da goyo akan titi tana hawaye kana ganinta kaga wacce take cikin damuwa batama sanin inda take dosa kawai neman masallaci take inda zta kai damuwarta koda ma arabata da gawan yaron nan tukun tasan inda dare ya mata.

Ahaka harta fara tunanin komawa gaban iyayrnta inma mutuwa zatay gara ta nemo gafararsu koda bazasu yafe mata tasan dai ta nemi gafararsu..

Tana tsaka da wann tunanin taji karar babban mota abayanta ana mata horn garin firgitowa baya ta fadi kasa cikin tubaya sai motar ta tsaya bata ma ga wacce ta fito ba saida taji qamshin turarenta snn taji duniyar ya tsaya mata cakkkk ganin hadixa ce.

Tunda suka hade idanunsu waje guda basu iya saukewa ba har saida hadizan ta dagata sama suka tsaye atsaye suna kallon junansu da mamaki kowa idanunta na zubda hawaye

yau kwanan hadiza uku kenan agarin sunzo harkan siyasa da mijinta
dama kuma can tana rike da lamarin shema aranta
ita hadiza sam ba bakuwar zafi bace, bata dauki rayuwar nan wani abu ba, her heart and life is soo simple, shiyasa daga tay kuskure inhar ta gane tay abu marar kyau zakaga ta amshe gyaranta akan lkci.

Tun a lkcin bikin halisa dataga sakon shema tausayinta ya tsaya mata aranta saidai tsoro ne ya hanata yin komi akai face saida lamarin meenal yazo ya sake daga mata hankli taji gara ta nemi shema wata rana taga halinda shema take ciki koba komu su musulmai ne, kuma sun more junansu, rauni da kuskure kusan halittan dan adam ne. Inde taga akwai chance na yafewa da taimakawa shema gani take ba wani abu bane awajenta dan tay hakan. Shiyasa suna zuwa wann garin da mijinta tay amfani da information din da yar uwanta haneefa ta bata akan shema tazo yankin datake tanata nemanta ahakan ma da kyar ta sameta ayau din.

Idonsu cikin na juna zuciyar hadiza yaa mugun karyewa data yadda wahalaa da kunci yadaka shemau ta dawo, sunanta ma dakyar hadizan ta furta dake shemaun ce ta fara durkushewa kasa cikin rauni tana kuka ta dauka gizon hadiza take gani

Tunda ta durkushe kuka take tana cewa na cuceki hadiza, na hainceki, naci amanan yardan dakika min..hasada da kwadayi ya hallaka ni, ya rabani da rayuwata da kawance na hadiza kiyi wa Allah kimin aikin gafara.

Haka mutane suka fara taruwa suna kallonsu sabida irin kukan da shema take tana rokon hadiza gafara, a raunane hadizan ta tsuguna ta rungumeta batare da tace mata komi sukay ta kuka. Daga bisani ta saketa ta jawota suka bar wajen izuwa wani hotel nan ne shema ta gayama hadiza duk wani abunda take ciki tun tana da auren mahmud bata boye mata komi ba.

Hadixa tay kuka hartana sheshheka dan sosai labari da nadamar shema ya girgizata bama kadan ba.. abu na farko da suka fara aka binne gawar...sann aka bataa masauki, bayan kwana biyu da suka samu nitswa suka zauna suka tattauna me tsayi.

Shema tagama karaayaa da rayuwa amma haka hadiza ta bata karfin gwiwa tace mata bawa baya cire ransa akan niimar ubangijnsa as long as tana raye akwai wann chance din nafara gina rayuwanta daga farko. Snn hadixa tace mata tay kokari da bata zubda cikin ko ta kashe danta ba, hakan yana nuna cewa tana da imani dan haka ta cire rauni ta farfafo da imaninta ta nemi gafarar iyayenta ta fara rayuwanta akarkashinsu a fresh.

Atakaice dai da kyar shema ta qamsu da hakan badon komi ba saidan tsoro, kunya da nauyin da zuciyarta yake ciki akan abunda ta aikata

Dan haduwarsu da hadizan yasaka tadan wanke daudar jikinta ta dawo kamar mutum aka bata abinci tana ci akai akai bayan sun yi sati hadixa ta rakota suka dawo lagos daga nan suka fara neman iyayenta, har suka same su anan bauchi.

Hadixan ce ta rakota har gidan iyayenta kusan kwanansu uku shema tay tana aikin neman gafarar su da kyar da wuya kafin nan suka barta ta shigo ciki kafin suka amsheta
Ahakama baban nata bawai ya gama sake jiki da ita bane. Mahaifyrta ne kawai ta sauya mata gabaki daya, tafara jan ta ajiki yanxu sosai kusan kowani rana saita mata nasiha akan rayuwa duk wani alheri da mahmud ya musu tasha mamaki sosai.

Cikin halisa na shiga wata takwas suka dawo nigeria domin ta haihu anan tay wankan gida

Wajen sunan vicky suka hadu dukansu su ukunsu ita da vickyn da hadiza
After a long while bayan abubuwan nan duka sun faru, Baby girl kyakkawa vicky ta haifa an saka mata suna Isabella wajen suna aka sha shagali har dare suna tare inda hadixa ta kawo musu bayanin abunda ya faru afanninta da shema

Dukansu saida jikinsu yay sanyi sosai. Halisa ta yabi halayyar hadiza na tausayi, imani da yafiya, sosai vicky tay hawaye dan itace tafara cewa zata taimaka ma shema da financial assistance dan ta tada rayuwanta tunda duk sunsan dawowar kawancensu kamar dacan da su shemau abu me wuyane sabida kowa yanxu yana da rayuwarsa kuma sun dauki darusa masu yawa masu nauyi dan har akan meenal saida suka tattauna Halisa ce ta gaya musu cewa hjya nadiyan has been seriously sick ana batun za'a kawota asibiti once her case its aproved.

Kowa ma jajantawa dan ayanxu babu sauran wani fushi ko haushi Cikinsu babu wanda yake iya jin wani abun aransa game da yan uwansun face tausayi da adduar samun saukin rayuwa

Labarin meenal dake zuwa shine babu wanda ya taba zuwa dubata tunda aka kaita wajen babu wanda ya lekata haryau har kwanan gobe daga ira sai halinta sai tunaninta tun tana raya masu muni harta fara tuna kalar kuskuren da ta aikata.

Bayan sunan Vicky da wata guda harda sati Halisa ta haihu agidan surakunanta a lagos da tsakar dare dake tun dawowarsu jikinta yay nauyi agidansun kawai take zama.

Khaleel ne ya amshe haihuwar shikadansa tana kuka yana hawaye yana tarairayer har ya zaro yaransa guda biyu daya mace daya namiji
Chapter 308 · 0% Book details