Sashe 99
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na kuma gane dalilin da ya sanya shi kansa yake 'boyewa saboda tabbatuwar kwanciyar hankalinta tunda ni din ta gaban goshinta ce in banda yanzu da magauta suka yi yawa amma zahiri Hajja tana sona k'warai, kuma tana son zamana da d'anta.
(Ga masu buk'atar a tallata musu hajarsu ina yi cikin farashi mai sau'ki a yi mini mgn 08089965176)
Ranar da na shirya tafiyar laraba ce wadda na tabbatar da cewa Sahura tana wajan aiki ba za ta yi yun'kurin zuwa ta dakusar da ni ba sai dai ta dawo gida ta samu Yusura da Baba Tabawa.
Akwati biyu na yi ta kayana na hada komai dana tabbatar da cewa zan buk'ata.
Muka yi waya da Hamusu na gaya masa zan je maiduguri ya cigaba da kula da komai wanda dama hakan aikinsa ne.
Bai kawo komai a cikin ransa ba muka yi sallama.
Na umarci Ayuba ya fito da mota kai tsaye gidan Sahura muka nufa aka yi sa'a Idiris yana gidan bai fita kasuwa ba tukkuna tunda lokacin da muka fito daga gida tara da rabi na safe.
Tun a mota muka yi sallama da Baba Tabawa na bata dubu hamsin na ce ta ri'ke a hannunta amma tunda na sanya mata lambata a sabuwar wayar dana saya mata duk lokacin da take da wata matsala ta kira ni ta gaya mini zan tura mata da kudi.
Ta kama hanya ta tafi gidanta kad'an da gidan Sahura.
Ita Yusra sai da muka shiga gidan tare sauran yaran duk suna makaranta a gurguje na tsaya muka gaisa da maigidan yana tambayata lafiya dai na ce masa kalau zan je maiduguri shine dalili.
Na mik'awa Yusra dubu biyar ta kar'ba jikinta duk a sa'bule na kama hanyar fita a gurguje ina cewa dashi ya gayawa Sahura zan kira ta a waya idan na isa.
Tashar kasuwar kwari na ce da Ayuba ya kaini.
Ya tsaya yana jayayya wai na fadi inda nake so na je zai kaini tunda akwai wadataccen mai a motar kuma aikinsa ne hakan idan oga ya ji labarin hakan zai yi sanadin rushewar hanyar abincinsa.
ganin yana yi mini taurin kai ya sanya na rufe shi da fad'a sosai na ce ya sauke ni muddin ba zai yi abinda na ce dashi ba.
Ganin yadda raina ya b'aci ya sanya shi jan motar bai sake magana ba kuma kai tsaye inda na umarceshi ya nufa da ni.
Muna isa na bude motar na fito.
Shi ma ya fito da sauri ya d'auko mini akwatinana.
Mota guda na d'auka domin ba zan iya jira ba.
Ban ma tsaya yin sallama da Ayuban ba na ce da direban ya shigo mu tafi.
Ina kallonsa ya koma motar jikinsa a sanyaye kuma har direba da nake cikin motarsa ya ja muka tafi shi bai bar tashar ba.
Tun a mota na kira Baban Saude dama kwanaki uku da suka wuce mun yi waya dashi na fara gaya masa halin da ake ciki ya ce mini maganar ba ta waya ba ce sai na zo tukkuna sai mu tattauna.
Na sanar dashi cewa gani nan akan hanya ya yi mini fatan alheri da sauka lafiya.
Sai daf da magriba muka isa maiduguri na sake d'aukar mota har kofar gidan Baban Saude yana tsaye a kofar gida fuskarsa kadaran kadahan har na fito daga motar direban yana sauke akwatinana.
Ya k'araso wajen da muke tare da kiran yaronshi dake wasa a can tsallake ya rugo da gudu wajan ya umarce shi ya d'auki akwatin kayana ya shiga dashi gida.
Yaron ya d'auki babbar akwatin da sauri ya nufi gida da ita.
Shi kuma ya sunkuya zai d'auki k'aramar.
Da sauri na ri'ke tare da cewa." Haba Baba bari zan shiga da ita."
Ba tare da ya ce mini komai ya saki akwatin na d'auka muka jera muna tafiya yana fad'in.
" Kin ci sa'a yau kwanana uku da dawowa kuma na kan d'auki sati ko kwana goma ban koma ba, Amina wannan lamarin naki ai abun a zauna ne domin kuwa ba karamin abu ba ne.
Ni namiji ne amma ba na goyon bayan azzaluman maza."
Murmushi na yi tare da furta." Wallahi Baban Saude tura ce ta kai bango ha'kurina ya kare akan lamarin nan, domin kuwa duk yadda na so ganin na zauna abin ya ci tura kamar yadda na gaya maka yau wata bakwai kenan rabona dashi kuma duk ya rufe hanyar da zata had'ani dashi to kaga zamana ai bashi da amfani yana da kyau ace a neme shi domin ya sanar da manyana abinda ya yanke akaina.....
Wannan badakala ta Amina da Tajo.
Allah Ya yayyafawa abin ruwan sanyi.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*65*
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Don kuskure kin yi, amma hakan ai ba zai sanya a d'auki wannan mummunan matakin akanki ba ai idan ba yana so ya jefa ki a wata masifar ba me zai sanya ya k'aurace miki na irin wannan watannin wannan ba daidai ba ne an shiga hurumin addinin Allah tabbas
akan hakan dole mu neme shi domin mu ji me yake nufi.
Sai maganar zargi da rashin daidaituwar jini gabad'aya ma auran naku ai a baibai yake babu dacewa ai ta wani gefan kema kina da hujja Amina, na kuma ji dad'in da ki ke neme ni domin sanya ni a cikin lamarinki zan yi kokarin ganin na samar miki da farinciki in sha Allahu rabbi."
Gidan Baban Saude mai yalwa ne kuma daidai gwargwado yana da rufin asirinsa don har yanzu da rayuwa ta yi tsadar nan shinkafa 'yar gwamnati ake ci a gidansa.
Taliya 'yar hausa kuwa sai dai idan sun yi sha'awa yadda yake jingine musu buhun shinkafa ta gwamnati haka yake ajiye masu kwalin taliya da makaroni na waje da sauran kayan masarufi, shi din mutum ne mai wadata iyali matsalar kawai fa'da da tsautsauran ra'ayin takura iyali domin kuwa kafin a fita unguwa a gidan Baban Saude akan jima sai dai idan da 'kwa'kkwaran dalili.
Matansa biyu kowacce da yaranta da d'akunansu ciki da rumfa ne manya.
Akwai shaguna biyu daga waje wanda ciki matasan yaransa maza suke kwana cikin gidan kuma bayan d'akunan iyalinsa akwai falle falle biyu masu grima sai kicin da bandaki biyu na fitsari da kuma na ba haya sai wadataccen tsakargida mai yalwa don har da bishiya a tsakiyar tsakar gidan.
Sayyada ce kawai take zawarci dama lokacin da anti Yagana ta je mini take gaya mini ai an sasanta anti Saude da anti Zainab sun koma d'akin mazajensu amma kafin hakan sai da aka sha daru domin shi cewa ya yi raba auran zai yi.
Sai da Dada ta yi masa jan ido tukkuna ya janye matakin da ya d'auka domin idonsa ya rufe baya duba kowa dama ai hausawa suka ce kowa nasa ya sani, shi yana duban 'ya'yansa yayin da mazajen suma suke duba wahalar da nasu yaran za su shiga muddin aka raba su da iyayensu.
Anti Saude itace babba don ta girmi ma anti Yagana amma da kad'an kuma yaranta bakwai, ita kuwa anti Zainab haihuwarta biyar daya ya rasu hud'u a raye amma duk da haka ya ce shi sai an sakar masa yaransa kuma ya tubure lallai babu d'an da zai d'auka ya yi wa wahala kowanne yaro ya koma gidan ubansa.
Gabad'aya ma sai sanya dokar kada a kuskura a sake barin yaran su shigo masa gida.
Wannan matakin da ya d'auka shi ya gigita anti Zainab tunda ita nata akwai k'ananu a ciki kuma ita kadaice bata da kishiya mijin nata ya d'auki yaran ya kaiwa yayarsa ita kuma kullum ficewa take yi kasuwa ta baza hajarta.
Anti Saude ce mai kishiya kuma yaranta sun girma sannan kuma duk maza ne.
Anti Zainab kuwa da mata a ciki.
Tashin hankalinta ta yi sosai babu shiri a 'boye ta je gidan Dada ta fashe mata da kuka tana gaya mata yadda aka yi tare da neman alfarma kada ta gayawa Baban nasu itace ta gaya mata.
Wannan shine dalilin da ya sanya Dada ta bud'e masa wuta akan lallai ya nemi mazajensu ya zauna dasu ya ja musu kunne amma banda maganar rabuwa a duba yaran domin kuwa hukuncin da ya yanke ba shine mafita ba tunda dole ai watarana za su sake yin aure kuma mazan ba 'kwan'kwasasu ake yi a ji ba.
Ita kuwa Sayyada da yake itace auta a mata kuma sunan Dada ne da ita dama tun kafin a yi mata aure 'yar lele ce tunda ya fahimci mugun miji take aure mara ciyarwa da kula da lafiya sai kawai ya maka shi a kotu akan ya sakar masa 'yarsa ya kuma fadi ko nawa ya kashe a lokacin da zai aureta zai biya shi tunda shi ya nemi sakin dama kuma haihuwarsu d'aya saboda farincikin Sayyadar ya bar yaron nata a hannunta domin kuwa kuka ta dira a gidan bayan alkali ya raba auran ta ce ita ba zata bada yaro ba.
To da yake dama 'yar lelensa ce sai ya kyaleta ya ce mata amma muddin ubansa ya zo nemansa za a bashi abinsa.
D'aki guda ya sanya a ka gyara mini tsaf har da katifa da sabon mashinfid'i da labuleye masu kyau d'akin yana ta k'amshin turaran wuta irin na tsinke.
Mama uwarginshi da kanta ta shigo ta kawo mini abinci a jere a tire na silba muka sake gaisawa bayan wadda muka yi tunda kafin na shiga masaukina sai da na shiga duka d'akunansu muka gaisa.
Ta dinga tambayata mutanan gidanmu da yaran na ce mata duk kowa lafiya lau.