Sashe 217
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gurguje muka gaisa da masu hidima da gidan ya bude mini motar na shiga na zauna ina addu'a a cikin zuciyata ya shiga mazauninsa shima kafin ya kunna motar daga can maigadi na ko'karin bude gate din gidan....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*146*
Gida a kawo Fadila tunda haihuwar fari ce kuma dai gidan nata ba shi da wani spece inda Allah ya ta'kaita nasa ne ba ya haya ba ce wai hausawa suna fad'in guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni.
Duk da haka ya yi kokari tunda d'aki uku ne da kicin da bandaki sai dai dak'unan duka ba ma su yalwa ba ne.
Haihuwa da lafiya akwai anya farinciki yarinyar tana zauna da babyna a hannu tana bashi nono na cika da mamaki kwarai da gaske wai yau Fadila ce ri'ke da jinjiri har tana shayar da shi gani ni uwarta gotai-gotai da ni ban gama haihuwa wato idan da Kamaluna ma macace haka za mu jera haihuwa da shi duk da Fadila ta gir
me shi sosai amma dai da mace ne a yanzu da ake yi wa yara auran wuri wata'kila da tuni na aurar ni ma
Yusuran Sahura ma tana can da nata tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe wai a haka ma ta yi 'bari na wata hud'u.
A washe da safe Sukairaju ya d'auki hanyar komawa gida bayan ya karya kummalo.
Yawan shige da ficen da ake yi a gidan dangin mijin yarinyar da danginmu suna zuwa ganin jarari Hakan bai ba mu damar 'kebewa sai a daran ranar dana kwana biyu a gidan tukkuna muka zauna muna tattauna al'amura masu yawa.
Nan na gaya mata irin abubuwan da suke faruwa tsakanina da Hauwa da shawarar da na yanke sannan da auran da yake shirin yi a tsukin kwanakin nan tunda ya ce satin na sama suka yanke za a daura aure.
Ta dinga mamaki tana fad'a kamar ta ari ba ki wai shi bashi da bakin da ba zai ce ya yi wa yarinyar girma ba ai ana barin halas don kunya wannan babbar asara ce da jin kunya idan har ya amince aka daura masa aure da yarinyar da ko shakka ba ta yi ta ji jinkanya da shi.
Abin ya dinga ba ni dariya ganin yadda ta hakikance da gaske tana ta fad'a tana cewa girmansa ya zube a idonta tunda ya shigo da son zuciya dama can yana so idan ba haka ba daidai gwargwado ya yi wa malamin alheri mutumin ya rushe masa gida ya zamanantar dashi tare da sabunta tsangayu irin na zamani aikuwa ya yi abin a yaba masa kuma idan biya zai yi akan hidimar da ya yi masa ya biya shi mai zai sanya kawai a d'auki yarinya a bashi ya kuma sanya hannu ya kar'ba har yana cewa don babu yadda zai yi ne wannan karya ce tsantsa da yaudara.
Da muka wayi gari ma ta tashi da mita shiga fita dari sai ta yi maganar tana cewa kin yi daidai ya kawo yarinyar su zauna da Hauwa a gidan ke ya canza miki wani idan ma ba zai yarda ki zauna a gidanki na kano ba ai yana da iko anan abujan sai ya samar miki da wani.
Irin wad'annan masifun ne ya sanya wasu mazan ko basu da wadata suke rabawa matayensu gida to balle shi da yake da suttura da wadata tunda har abinda Hauwa take yi ya'ki ya'ki cinyewa kawai ya rabawa kowa mazauni sai a samu zaman lafiya.
Na ji dad'i sosai ganin yadda wannan karon anti Yagana ta goyu da bayana na saki raina sosai ina jin sasaauci Kuma ban kunna wayata ba yau kwana biyu kenan wanda nasan yana can yana ta lalubena a wayar bai samu ba.
Sai da na yi wanka na karya kullumalo tukkuna na fito falon na sami yarinyar tare da kawayenta na makaranta sun zo ganin jaririya suna ta tsokanarta sai suka ba ni sha'awa muka gaisa ina yi musu dariya cikin raina ina cewa duk yadda za ta kai ga baku labarin nakuda ba za ku fahimta ba sai ta riske ku tukkuna.
Anti Yagana tana ta gyara kaji a kicin nace." In ban da abinki anti Yagana ai sai ki kira ni na taimaka miki."
Ta ce." Ke ma ba lafiyar ce dake ba Amina na gode Allah ni da ya hore mini lafiyar wannan hidimar ta same ni Dada ciwo ya dabaibayeta nasan da ita za ta zo ta zauna mini"
Na ce." K'warai hakane shirin da na yi yanzu zan tafi can babban gidan ne na duba jikinta zan dan zaga dangi mu gaisa."
Ta furta.
Hakan yana da kyau."
Kujera na ja na zauna na kama mata aikin Muna gyara kajin a tare na ce." Na lura yaron nan da yake auran Fadila yana da zuciya wallahi gashi nan komai ya yi na al'ada."
Ta gyad'a kanta tana cewa." K'warai Kam tunda ta haihu yake hidima domin da ta fara nakudar ma bai iya kaita asibitin gwamnati ba kudi ya fitar ya kai ta wanda za a bata kulawa wallahi sai da ta haihu ya kira ya gaya mana."
Na furta." Irin wad'annan matasan ya kamata ace an d'auki aure an ba su masu zuciya da dogaro da kansu da kuma ko'karin ri'ke iyali daidai gwargwado."
Daya daga cikin yan matan kawayen nata ta fito tana fad'in.''Mama ana kiran ki wayar ki." Ta mika mata wayar na riga ta kar'ba domin hannunta gaja-gaja yake fa jinin kajin da take gyarawa.
Ina duba fuskar wayar naga sunan Alhaji Tajuden da haka ta yi serving lambarsa
Na daga tare da sanya mata a kunne ina ji yana gaisheta da mutuntawa kamar yadda ya saba itama ta amsa cikin nutsuwa har tana tambayarsa yara ya ce duka suna lafiya sannan ya yi mata barka da arziki kafin ya fara tambayarta ina nake ya yi ta kirana a waya baya samuna.
Ta dube ni kafin ta ce masa gani nan a zaune.
Sai na ji yana cewa da ita ta gaya mini na kunna wayata akwai muhimmiyar maganar da za mu yi.
Ta ce masa to in sha Allahu suka yi sallama.
Ta d'an dube ni a sanyaye tana fad'in." Na ji shi a sanyaye yana magana babu nutsuwa Amina kada dai ki ce da biyu ki ka zo nan garin kar ki ce da ni yaji ki ka yi akan wannan matsalar domin idan bacin haka ai ban ga dalilin da zai sanya ki kashe wayarki ba."
Na ce." E, to ba yaji na yi ba amma dai Ina tsammanin ba ni komawa Abuja kai tsaye daga na bar nan kano zan sauka gidana na sharad'a tunda ya'ki fahimtar abinda nake nufi."
Ta gyad'a kanta tana cewa." Ba ni son hakan ya haifar miki da wata matsalar Amina amma ni kaina a son raina nafiso a raba muku muhalli sai hankalina ya fi kwanciya.
Na furta." Duk mai hankali da tsinkaye abinda zai duba kenan matsawar muna zaune a inuwa guda da Hauwa ba za a taba samun zaman lafiya ba Shima ba zai huta ba tunda ni dai na zame mata ciwon ido anti Yagana wallahi har mamakin yadda Hauwa take zafafawa kanta a kaina ni kuma ba ta raina kwata kwata ban kuma dauketa a matsayin kishiya da zata daga mini hankali ba.
Kawai yanzu nutsuwa da kwanciyar hankali nake buk'ata shiyasa na ce ba ni buk'atar zama da ita a gida daya."
Ta furta." Hakane akwai hujja mai karfi a tare dake ni ma ina bayanki amma yanzu tunda ya ce ki kunna wayarki za ku yi magana ki kunna din mu ji mai zai ce."
Na ce." To shikkenan zan kuna."
Sai da muka gama aikin gyara kajin tukkuna ta d'ora a wuta na wanke hannuna da omo sannan na koma d'akin na d'auki wayata na kunna minti goma sha biyar a tsakani ya kira na daga a nutse na yi sallama ya amsa na gaishe shi nan ma ya amsa babu annasuwa.
Kafin ya d'ora da fad'in." Yarinyar Minal tun bayan da suka dawo daga makaranta ta samu ba kya gidan kwanta zazza'bi ya rufe ta ya hau ya sauka har takai da sai da aka yi mata karin ruwa Amina ida ta rasu wallahi ba zan yafe miki ba."
Gabana na d'an fad'uwa na ce." Ban gane abinda kake nufi ba."
Ya ce." Kin ji abinda na fad'a Amina ai kin san ba ki da gaskiya shiyasa ki ka kashe wayarki tsayin kwana biyu."
Na ce." Mayya ce ni ma shiyasa na kama kurwar Minal na taho da ita nan maiduguri to don Allah idan ta rasu ka d'aure ni har igiya ta yi rara."
Ya ce." Abinda za ki ce kenan?"
Na ce." To me zan ce maka ka ce yarinya bata da lafiya saboda na taho da kurwata idan ta mutu ba za ka kyale ni ba to ka d'aure ni don Allah shine abinda za ka yi."
Ya kashe wayarsa jin yadda na bud'e masa wuta idan ba rashin mutunci ba kawai ya kira ni yana ko'karin gaya mini magana ni na d'orawa yarinyar ciwo wane irin bala'i ne wannan ne."
Tsabar takaici da damuwa ban iya zuwa dubiyar Dada ba a ranar saboda jikina ya riga ya gama mutuwa da rashin lafiyar yarinyar da kuma abinda ya gaya mini a kan hakan.
Can wajen sha d'aya ya sake kira na na daga ban ce masa komai ba na ji yana fad'in.'" Za ku gaisa ko?'' Da yaran yake na ji muryar Usaina tana kiran Mama na ce." Naam Usai ina Hassana." Ta ce gata nan." Minal fa?"
Ta ce." Ta yi bacci ta fad'a muryarta tana rawa.
Na ce." Ya jikin nata."
"Da sau'ki ta fad'a kamar za ta fashe da kuka.
Na ce." To ba ni Hassana itama mu gaisa ko Ina Khalil?''
Ta ce." Yana 'kasa da Hassana." Na ji maganarta.