Sashe 270
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya tsira mini ido kafin ya cigaba da cewa." Tunda kin dawo da ita sai ki gaya mata zamanki take yi babu yawuna ba kuma ruwana da ita."
Jikina ya yi sanyi ganin ta hanyar da ya 'bullo kuma hakan bai yi masa ba kenan haushi ya ji.
Na daure na furta." Ba ni da na dawo da ita ba Hajja ce."
Ya d'an harare ni yana fad'in." Duk abinda ki ka aikata mahaifiyata ta sanar da ni.
Ita dai kin yi mata gwaninta kuma ta yi miki addu'a amma ni sam ba ki burge ni ba."
Na yi shiru ina kallonsa kafin ya cigaba da cewa." Tunda kudin cizonki suke yi mai zai sanya ba ki sayi fili kin yi k'aramin massalaci ba hadiya ga mahaifiyarki ko ki yi rijiyoyi na ruwa ko kuwa ki kai gidan marayu sam baki burge ni ba wallahi idan ma don ni ki ka yi bai ban sha'awa ba.
Shiru na yi na kasa tanka masa saboda jin haushin gwaliyar da yake yi mini.
Ganin ban ce komai ba sai ya cigaba da sakin maganganu na gaji da sauri na daga masa hannu ina fadin." Ni don Allah na yi ai ba don na burgeka ba tunda Hajja ta yi farinciki kuma hakan ya yi mata daidai alhamdulillahi maganar ta mutu haka don Allah."
Ya tashi zaune sosai yana kallona kafin ya ce." Magana ba zata mutu ba tunda ba ni na ce Hauwa ta dawo ba na gama yanke hukunci a kanta."
Na ce." To tunda ka gama yanke hukunci a kanta sai kawai ka aiwatar ni ina ruwana idan ka saketa ka tabbatar da cewar zaka auro wadda zata kula da yaranta ni ma nawa kadai zan ri'ke shikkenan karshen magana.
"
Na yun'kuri na tashi na bashi waje.
Washe gari har d'akina ya biyo ni ina toilet ina ta kalato amai irin na sassafe majina ce kawai ke fita wani abu ya tsaye mini a wuya yana kaikayi.
Ya leko toilet din ganin halin da nake ciki sai jikinsa ya yi sanyi ya rike mini hannu har na gama na wanke bakina muka fito zuciya sai hantsilawa take yi.
Muka zauna ina ta sauke numfashi shi kuma ya tsira mini ido sosai a hankali ya furta" cikin ne ko?"
Juyar da kaina na yi ban bashi amsa ba saboda har yanzu haushin abinda ya yi mini jiya nake yi
Ya lalubi wayarsa dake cikin aljihu jikinsa na dan rawa still hannunsa na ri'ke da nawa lambar wayar Dr Sailuba yake nema.
Na kar'bi wayar na ajiye saman dirowar gefan gado ya kusance ni sosai cikin taushin harshe ya furta." Ki gaya mini mana menene ba ki so a kira Dr Sailuba kin tabbatar ne?"
Na d'an saki ajiyar zuciya Ina fad'in." Shine na tabbatar tun lokacin da ka fara hasashe tunda kuwa hakane ka ga babu amfanin kiran likita ni ba yarinya ba ce.
"
Ina rufe bakina ya zame kasan kafet sujuddur Shukur ya yi.
Na zuba masa ido yayin da goshinsa yake kasa yana mika godiyarsa ga Allah sai jikina ya yi sanyi sosai anya kuwa ya ta'ba d'okonta da ciki kamar wannan da aka samu yana murna duk lokacin da muka samu ciki amma dai wannan abin ya yi yawa. cikin raina na ji nima ina son cikin da kuma ina addu'a akan Allah Ya cika mana burinmu na samun d'iya mace mu a
sanya mata sunan Hajja Halimatussadiya.
To ko da ta dawo sai da ya gama shan 'kamshinsa tukkuna don sai da ta kwanta hud'u da dawowa sannan ya je gidanta kuma kafin ta dawo din na ga ta kira shi a waya ta gaya masa zata dawo ni dai addu'ata Allah Ya sa kada ya gaya mata cewar ba shine ya bata kudin ba ni ce don nasan ba 'karamin aikinsa ba.
Sati biyu ya kara akan dawowarta ya tafi Legos domin daman dawowartata ce ta sanya shi jinkirta tafiyar ya tabbatar mini da cewar ba zai wuce wata biyu ba zai dawo.
Tunda ta dawo bamu hadu ba dama can tunda aka raba mana gida ita ce mai shigo mini bana zuwa gidanta sai da dalili mai karfi zuwana biyu kacal lokacin da ya yi ciwo da lokacin da ta yi 'barin ciki.
Sai dai duk ranar juma'a nakan ce da yaran su je su gaisheta suka dan zauna a can dalili Ladidi mai aikinta na hillatarsu da tatsuniya da labarin kanzon kurage su kuma akwai son haka idan sun dawo gida suce mama ta ce a gaisheki.
Hadiza kam takan zo mini sa'i da lokaci mu yini tare tunda tare suka tafi da Sukairaju itama cikin kad'aici take hakan ya sanya nake tura mata yaran ranar alhamis bayan sun dawo daga boko sai Masa'udu ya kai su idan sun dan jima ya je ya d'auko su.
Cikin wannan yanayin Nabila ta fito tare suka zo mini ita da Nusaiba wai sallama ta zo yi mini za ta koma jos da zama dalilin abinda ya samu rayuwarta duk abinda ta mallaka ya salwance da kyar Allah Ya bayyana gaskiyar cewar babu hannunta akan abinda ya faru.
Wallahi ta ba nii tausayi sosai ta yi wani irin baki fatar nan da aka kwailayeta ta toye ta yi dabbara-dabbara daka gani ta k'are mata babu kud'in cin abinci ma balle na sayan man bleaching duk wannan gayun babu shi ta susuce ma gabad'aya.
Rayuwa kenan shiyasa duk abinda mutum zai yi ya sanya tsoron Allah a ciki.
Kasuwanci ba za a tsarkake shi ba ya ki Haram yaki halak ko ta halin kaka sai an yi kud'i tunda an shiga hurumin Ubangiji kuma ai ba za a ga daidai ba.
Wasu daga cikin kayana na tsinto mata masu kyau set biyar na hada mata da mayafai da hijabak sannan na ce lallai za ta ga sakona a kurkusa..
Kafin su tafi kuwa kuka ta yi sosai da sosai tana ta ba ni ha'kuri har na gaza gane hakurin me take ba ni domin dai gabad'aya cikin nadama da danasani take tunda duniya ta yi kuli-kulin kubura da ita.
Bayan kwana biyu da zuwansa kuwa na kira Nusaiba a waya na ce ta turo mini details din Nabilan tana turo mini na sanya mata dubu dari biyu ciki.
Sannan dama ina da lambar wayarta tun farkon haduwarmu lokacin rasuwar Alhaji Amadu muka yi musayar lambar a lokacin jininmu ya hadu domin ni da ita ne muka dinga tiri-tiri da Hajiya Maryam din akan 'kin cin abinci.
Kuma bayan Hakan muna d'an gaisawa a wancan lokacin har idan ta yi status na bude na gani idan abin murna na yi mata murna haka zalika idan abin jaje nan ma na jajanta.
Katsam na daina ganin status dinta nan na tabbatar da cewa ta yi block dina ne tunda lokacin aure ya kullu tsakanin maigidan da 'yar uwarta sai ta rufe ni, a lokacin abin ya yi ta ba ni mamaki da daure mini kai
Na kira ta muka gaisa na ce ta duba na tura mata sa'ko kamar wadda na bawa miliyan biyu ta dinga yi mini godiya har muryarta tana rawa tsabar kyautar ta yi mata dadi.
Lokaci bayan lokaci Kamalu kan kira ni bidiyo call mu jima muna hira yaro ya yi wani girma da wata haiba ta mussaman wata irin nutsuwa da annashuwa nake tsintar kaina a ciki a duk lokacin da nake kallonsa ina kara tahamdi ga Allah madaukakin sarki.
Watansa uku ya dawo kamar yadda ya fad'i lokacin cikina ya shiga wata na biyar amma bai fito ba ya dai bi jikina kwankwaso da breast sun sake girma sai dai Ina jin ciwon mara kafa sa sauransu har gida Dr Sailuba take zuwa ta yi mini awo ta kuma ba ni maganganun da suka da ce.
Wai shi a tunaninsa idan ya dawo zai ga ciki ya fito sosai na ce masa cikin bai ma cika wata biyar ba ai bai yarda ba sai ma ya fara zargi babu shi ya rasa sukuni ko kad'an hankalinsa bai kwanta ba sai da dr Sailuba ta yi masa cikakken bayani ya ce a je a yi scanning a ga mai za a haifa tunda nake samun ciki bai fiye matsawa ba yakan ce duk wanda Allah Ya ba shi yana so amma abin mamaki wannan kam yana dawowa ya daga mini hankali dole na shirya Hadiza ta yi mini rakiya domin yin scanning din kamar yadda ya buk'ata Ashe itama tana 'kunshe da nata cikin ban sani ba bayan an gama yi mini aka yi mata cikin ikon Allah ni mace ita namiji satikan cikinta sun haura nawa ta riga ni samu amma dai tsiraranmu kadan ne za ta riga ni haihuwa wata'kila kafin ta yi arba'in na haihu.
Sosai na tayata farinciki domin can baya gidan Alhaji Halilu ta yi ta samun matsalar lalacewar ciki har dai suka rabu bata haihu ba a wannan matakin da muke ciki da shekaru suka fara nisa ko biyu ta samu sai ta godewa Allah.
Mijinta ne ya kai mu bisa bin umarin maigidan shi dai tun a mota yake ta annasuwa ya rasa ina zai sanya rayuwarsa ganin result din cikin matarsa namiji kuma cikin koshin lafiya ita dashi gabad'aya sai suka ba ni tausayi.
Kwanaki goma da yi mini scanning muka tafi umara ni da shi a cewarsa yana da kyau mu je mu yi godiya tare da addu'a akan Allah Ya tabbatar mana da abinda hasashe domin kuwa komai yana iya canzawa gashi ya jarabtu da son haihuwar 'ya mace mai sunan Mamansa.
Mun yi addu'a sosai wadda ta shafi kowane bangare satin biyu muka dawo gida.
Rayuwar ta cigaba da gurgurawa sannu a hankali ban san dai me yake tsakaninsa da matarsa ba domin tunda ta dawo ba mu had'u ba kunya ta hana ta zuwa inda nake sai dai sakon gaisuwa idan yara sun je.
Shi kuma yana ta zagari tsakanin gidana da gidanta duk wadda take da girki zai je ya kwana.