← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 276

Sashe 162

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu za ki cika she ladanki ina so ki nuna mini kwanzonki a wannan daran mai albarka."
Na dube shi duk ya kanainayeni.

Na ce." Wane k'wazo zan nuna kuma?"
"Ya dago da sauri yana fad'in." Ki cinye ni a wasan gabad'aya hajiyata."
"Umm" Kawai na iya cewa jikina duka ya shika.

A hankali ya mik'a hannunsa ya kashe fitilar gefan gadon da ta d'an haske d'akin.

Sai ya yi duhu sosai.

Ya rike ni da kyau tare da d'an tura ni na kwanta ya yi mini rumfa shikkenan daga lokacin ni ma na kwarkwace muka zama kamar tuburarrun mahaukata.

Da safe da wayar Hajja ya karya.

Ga yanayin yadda yake amsa mata magana ya sanya mini kasala.

Suna gamawa ya dube ni yana fad'in." Zan je kano yanzu Amina Amma ina sha Allah zan dawo yau idan kuma wani dalili ya sanya ni kwana zan kira waya na sanar dake in sha Allahu."
Na ce." To shikkenan." Na yi shiru ina kallonsa yana kimtsawa.

Na dai kasa daurewa da nace ba zan sake sanya musu baki ba, amma na gaza ha'kuri na ce." Ka ga abinda nake ta guje muku kai da Hauwa ko?"
Ya dube ni yayin da yake sanya links a hannun rigar da take jikinsa ya ce." Ai dole dama za a zo wannan ga'bar na sani, kada ki damu ni babu abinda zai faru sai alheri ni dama ai ban ce ina sonta ba, sune suka dage za kuma ta san ni ta yi wa wannan wulakancin ai."
Na ce." Kenan a ganinka itace mai lefi kafi ta gaskiya, ko da suka dage suna son auranka ka fad'i tsakaninka da Allah da annabi cewa kai ma baka sonta."
Kai tsaye ya furta." Wallahi Samira nake so ba Hauwa ba Amina, ai na gaya miki tuntuni Samira da ita na fara soyayya nasan menene so, Allah Ya k'addara ba mu zauna ba ta rasu.

Hauwa kam ba ni yi mata soyayya fitacciya gaskiyar magana"
Na ce." To mai yasa ba zaka maye gurbin soyayyar da kake yi wa Samira zuwa ga 'yar uwarta ba, ka ji tsoron Allah wallahi yanzu da bakinka kake furtawa baka sonta.

Amma mai yasa kake rayuwar aure da ita har ku haihu, menene bambacin Samirar da Hauwa tunda duka uwa daya Uba daya suke."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Da bambamci Amina, babu dalilin da zai sanya ni maye gurbin son da nake yi wa Samira akan Hauwa, me yasa lokacin da ta rasu ta'ki maye gurbin 'yar uwarta, na fa san komai Amina, don haka ba ki da ruwa akan wannan abinda yake faruwa tsakaninmu.

Ba a yi macan da za ta yi mini wannan iskacin ta kwana lafiya ba."
Na ce." To ai zumuncin da yake tsakaninku za ka duba."
Ya furta." Ita ta duba zumuncin ne?"
Na yi shiru ina kallonsa.

Ya girgiza kansa kafin ya bud'e ma'adanar da yake ajiye gilasansa ya d'auko daya ya sanya kafin ya kwashi wayoyinsa ya zuba a aljihu.

Ya dube ni sai kuma ya kama hanyar zai fita na bi bayansa ina fad'in." Za ka tsaya ka yi breakfast ko?"
Ya ce." A a yanzu wurin Momi zan shiga mu gaisa na wuce kawai zan ci abinci a can gidan Hajja in sha Allahu."
Muka sauko a tare ina fad'in." Shikkenan to don Allah a ce ina gaishe da Hajja da kyau tare da su Kamalu." Ya furta." Za su ji, zan gaya musu sa'konki in sha Allahu sai na dawo." Ya fice da saurin gaske.

Na juya na shiga d'akina jikina duk a mace.

Ubangiji Allah Ya sa mu ji alheri.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
"Yanzu don Allah Hajja abinda Hauwa ta yi shine zumunci? nasan duk wannan fad'an da ki ke yi akan hakan ba zai wuce ace kina gudun lalacewar zumunci ba.

Amma ki yi nazari akan wannan abinda Hauwa ta yi Hajja ko mahaukaciya fa ta san d'anta ki ga yadda ake yi musu ciki akan titi A
Amma su haihu a yi ta dambarwa da su wurin 'karbar jaririn daga hannunsu.

Sannan kin ga yadda dabbobi idan sun haihu suke tattalin abinda suke haifa ai ko babu dangantaka ta jini a tsakaninmu da yarinyar bai kamata ta yi mana haka ba.

Wannan wulakanci ne da rashin mutunci da kuma rashin tarbiya."
Hajiya Saratu ce take wannan maganar cikin yanayi na damuwa da bakincikin abinda yake faruwa.

Hajja ta d'an gyara zamanta tana fad'in." To tunda gashi nan a zaune sai mu ji menene dalili saboda ai k'arfe d'aya baya amo! ba wai ina goyuwa da bayan Hauwa akan abinda ta yi ba, ban ji dad'i ba kuma bata kyauta ba amma wata'kila duk ta yi hakan ne domin huce fushin abinda ya aikata mata.

Ai ya nuna mata iyakarta ni ma kuma ya nuna mini ba ni da wani muhimmanci dangane da rayuwarsa tunda har zai iya yanke irin wannan hukuncin ba tare da ya nemi shawarata ba.

A ganina kome Hauwa ta yi masa ta ci albarkacin jini da dangantaka ko."
Ta girgiza kanta tana cewa." Hajja Hauwa fa bata da kunya ba wai ina 'kin ta ba ne a a halayenta munana sun rinjayi kyawawan domin duk mai zuciyar imani da tausayi ba zai aikata abinda ta yi ba a yanzu kamar yadda na gaya miki ko daga waje Tajo ya auro Hauwa ba mu cancanci wannan iskancin ba."
Sai ta dube shi tana fad'in." Ka na jin mu baka ce komai ba, wai shin mai ya yi zafi ne tsakaninka da Hauwa da har ka saketa ko kana so ka nuna mini cewa ni ban isa ba ko kuma na ce ka d'auki hanyar lalata zumuncin da yake tsakanina da 'yar uwata da ta rage mini a duniya."
Ya ce." Hajja a yi hakuri amma ina ganin zan ha'kura da Hauwa kawai domin wallahi ban da tayar mini da rikici babu abinda take yi a gida."
Ta ce." Akan wane dalili shine abinda na tambayeka, kai yanzu baka ji kunya da nauyin gaya mini hakan ba da wane ido zan kalli Uwani.''
Ya yi shiru bai ce komai ba.

Sai ta cigaba da fad'in." Ka gaya mini mai ya had'a ku da har ta yi wannan fushin ta ajiye jariri d'anyar haihuwa ta gudu, duk abinda za ka ga uwa ta aikata haka ba k'aramin abu ba ne ."
Cike da b'acin rai ya shiga warware mata duka matsaltsalun da suka dinga faruwa wasu ta san da faruwarsu wasu kuma bata sani ba mussaman akan rikicinta da Maryam da kanwarta duk ya gaya mata abinda ta dinga yi har sakin ya ratsa.

Ta ce." To ai kai ma kana da lefi me yasa za ka raba su da yaransu hakan bai isheka ba ka had'a da duka da cin mutunci don haka ta gayawa uwarta ni ma ta gaya mini shin jaka ce ita da zaka dinga dukanta ko ka manta cewa diyar wani ce itama, kana so ka aurar da yaranka a dinga dukansu."
Ya ce." Wallahi Hajja sau daya na mare ta, amma ni ba ni dukan iyalinsa sharri ne kawai irin nata."
Ta ce." To marin ma kada a sake yin sa ban yarda ba, dukansu amana ne aka bamu bakidaya Hauwa ko ba ta ci darajar komai ba sai ta ci albarkacin zumunci da haihuwa ai ta zama kai ka zama ita haihuwa uku ba wasa ba ce."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." In sha Allahu ba za a sake ba.

Falon ya d'auki shiru na wani lokaci kafin ta ce." Menene matsayin auranta a yanzu?
Chapter 162 · 0% Book details