Sashe 207
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ce." Ai da so na yi ku tafi tare idan kun dawo zai sake komawa sai mu je kamar hakan zai fi."
Ta yi ya'ke tana cewa." Duk daya ne Amina ku je tare ni zan kula da yara kamar yadda jiya ya gaya mini cewa ya ba ni amanarsu za ku dawo ku same su lafiya in sha Allahu."
Kamar zararriya haka take magana a tsorace tunda tasan duk abinda zata fad'a ba gaskiya ba ne shiyasa ta kasa had'a ido da ni.''
Na ce." Hakan ya yi Hauwa dama na ce bari na shigo mu yi sallama tunda da wuri za mu tafi wata'kila kina bacci a lokacin."
Kanta a 'kasa ta ce." Hakan ya yi na gode sosai Amina sai kun dawo din.''
Na mike tsaye ina fad'in." To saduwar alheri Hauwa sai mun yi waya." Daga haka ban sake cewa komai ba na kama hanyar fita zuciyata da damuwar halin da take ciki kada fa mutumin nan ya zautata da bak'incikinsa domin duk ta shiririce wallahi........
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWA PEN*
*07084653262*
*139*
Ba na tsammanin ya yi sallama da Hauwa da za mu tafi haka na bi shi ba don zuciyata ta so abinda yake aikatawa ba sai don sanin rashin yadda zan yi da shi.
Tunda tsakani da Allah daidai gwargwado yana da ilimin addini ya kuma san abinda yake yi din ba daidai ba ne.
Na zura masa Ido kawai domin nasan muddin bai gyara ba Hauwa za ta sake tafiya gidansu mahaifiyarsa kuma ta samu labari anan sai ta gane cewa shima ya fi kyarfinta ba Hauwa ba ce kad'ai mara ji shima lamba d'aya ne.
Zuwanmu legos ya sake haifar mana da nutsuwa da kula da juna da kuma bud'e babin soyayya kamar sabbin aure duk da 'karamin cikin da nake d'auke da shi bai hana mun mori juna ba
a duk lokacin da ya zo wajena da buk'ata irin ta d'abia.
Daga lokacin na gama gazgata k'aunar da yake mini cewa babu algus ko almundahana domin duk wani nau'in kulawa ina samu da tarairaya har da kyautar kud'i miliyan biyar ya yi mini yana gaya mini na kara akan kasuwancin da nake yi domin yana hankalce da irin nauyi da d'awainiyar da nake yi a b'angarena.
Na yi godiya sosai da addu'ar k'ara samun budi da fatahi ya ce babu godiya a tsakaninmu a duk lokacin da nake da buk'atar kudi domin yin wani abu da zai kawo mini cigaba zai tallafa mini saboda yana girmama duk wani wanda yake tsaye don dogaro da kansa karin abin kuma ina ko'karin ganin na yi alheri da taimakawa wad'anda na fi su wadata.
Na ji dad'i sosai da sosai dama kuma mun yi magana da anti Yagana akan jari da zan bata ta yi sana'a ta ce mini tana so ta bude shagon jikin gidanta ta fara harkar provision da awo na ce mata harka ce mai kyau sosai kuma za ta samu alheri domin yanzu masu sayar da abinci kayan masarufi sune suke da kudi a hannu.
Abinda na yanke a raina cewa ita zan turawa kudin gabad'aya ta fara idan Allah ya sanyawa kasuwancin albarka sai ta zama babbar dila ta bud'e manyan shaguna.
Sai dai abinda yake dan damuna shine shin kudin da ya ba ni zai bawa Hauwa ko kuwa.
Ina sonsa ba kuma zan yi farinciki da cewa ranar lahira ya tashi a cikin sahun mazan da za a yi musu azaba dalilin fifita bangare daya na daga cikin matansu.
Kuma daidai gwargwado Hauwa ta kar'bi kuskuranta yau satin mu uku a Legos idan ba ta kira ni a waya yau ba to gobe za ta kira ni mu gaisa a sati sai mu yi waya biyar ko hud'u mun yi vidiyo call sau d'aya da ita kuma ban hangi nutsuwa da kwanciyar hankali a tare da ita ba.
Abinda na fahimta shine kamar tana kamun kafa da ni akan mijin nata wanda ni kuma nasan ban isa na sanya shi ko na hana shi ba tunda ga abinda ya yi wa mahaifiyarsa na yaudara ya nuna mata kamar ya ha'kura ashe akwai abinda ya ajiye a ransa na ramuwar gayya.
Na dinga nanata masa kan cewa yadda ya ba ni kudin nan Hauwa ya bata hakkinta ne.
Na farko da na gaya masa shiru ya yi mini bai ce komai ba ya cigaba da sabogoginsa tunda ya ce mini yana shirye-shiryen bud'e sabon kamfanin na suminti ne wanda suka yi tarayya da yaran Alhaji Amadu abokinsa Salim da Adam da Nusaiba.
Yana so ya fara sanya Salim din cikin harkokin da yake gudanarwa domin ya tsaya da kafarsa a matsayinsa na namiji babba da ake sanya rai a nan gaba zai zama wani abu.
Mahaifinsa Alhaji Amadu harkarsa kenan sayar da siminti da sauran abinda ya danganci gini gidaje to shine yake so ya d'ora yaronsa a kai.
A k'alla dai sai da na yi masa maganar Hauwa ya kai sau shida tukkuna ya tanka mini da tashin hankali ya rintse idonsa yana gaya mini babu ruwa da duk abinda yake yi na dawo masa da kudinsa idan ba na so tunda bai isa ya yi mini kyauta na ce na gode ba sai na yi masa gyara saboda na mayar dashi jahili Wanda ba shi da addini.
Na kuwa bud'e wuta ni ma na ce ai gaskiya ce kuma d'aci ne da ita ban iya munafurci ba kuma zan yi masa shiru ya danne mini baki da kudi mu zalinci wata ba domin ba ni so na mutu da hakkin kowa.
Ya ce idan akan Hauwa nake yi masa rashin kunya sai ya saketa kowa ya huta.
Na ce masa dama hakan ya yi shi zai kara tabbatar mini da cewa babu wanda ya isa.
Magana ce mai harshen damo ya tsargu sosai daga ranar da muka yi haka ya daina kula ni tsayin kwana uku muka yi ba ma magana gashi Muna kwana a d'aki daya a gado daya sai da ya juya baya ni ma na juya nawa.
A ranar na hud'u ne muna bidiyo call da Hauwa na ce mata ta had'a ni da yaran mu gaisa na yi hakane domin na daidaita alakar da take tsakaninsu..
Aikuwa da azama ta tashi ta fita falo alhamis ce babu islamiyya ta yamma ina zaune ina kallonta ta shiga dakinsu tana Kiran sunan Khalil.
Ya zo ya zauna a gefena ban ce masa komai ba shi ma bai ce mini komai ba amma dai tun shekaran jiya na fahimci jikinsa ya d'an yi sanyi ya rasa yadda zai yi ya rarrashe ni ya kuma nuna zai gyara kuskuransa.
Daya bayan d'aya muka dinga gaisawa suna ta tsalle da dariya mussaman Minal sai washe baki take yi.
Ya yi gyaran murya yana fad'in." Ni ba bu wanda yake nema ko?"
Jin muryarsa ya sanya suka dinga kiran sunansa." Baba" Baba.'' Ya kar'bi wayar ya haska musu fuskarsa sai dariya suna kiran sunansa yana amsawa cikin nishadi yana cewa ni babu wanda yake nema na ko?"
Usai ta ce." Baba yaushe za ku dawo?"
Ya ce." Mun kusa in sha Allahu ana zuwa makaranta ko?"
Suka ce "Eh.'' Ya gyad'a kansa yana fad'in." Muna nan dawowa in Allah Ya yarda."
Hauwa ta kar'bi wayar daga hannun Khalil tana hasko fuskarta ta ce masa "Ina yini?'' Ya amsa da sakin fuska har yana tambayarta yara."
Cike da jin dadi ta ce." Gasu nan ai suna ta kewa" a Takaice ya ce." Mun kusa dawowa amma ke ba ki yi kewar ba."
'Yar dariya ta yi kamar an yi mata dole ta ce.'' Sosai na yi kewar ku gabad'aya."
Ya yi murmushi a hankali ya ce." Duk ranar da na yanke mana dawowar zan sanar dake."
Da jin dadi ta furta." To shikkenan." Ya mik'o mini wayata na kar'ba muka d'an yi magana da ita akan yaran sannan muka yi sallama tare da bata sakon gaisuwa wajan masu aikin gidan.
Na kashe wayata na ajiye ban dube shi ba na sake hade raina sosai domin har yanzu ina jin haushin bala'in da ya yi mini sai kace 'yar cikinsa daga kawai an ce gaya kayanka.''
Ya riko hannayena duka biyun na dube shi amma ban saki fuskata ba.
Sai ya sanya hannunsa d'aya a kumatuna yana ta'be mini fuska da hanci yana d'an murza mini fatar le'be.
Tankwa'be hannunsa na yi ya sake mayarwa ya cigaba da ta'bule mini kumatuna da hanci na sake cire hannunsa a karo na biyu.
Ya sauke ajiyar zuciya a 'dan sanyaye ya ce." To ki yi dariya mana tunda na yi magana da ita?''
Juyar da kaina na yi gefe ban ce masa komai ba.
Ya matso sosai yana fad'in.
Ki yi dariya my love menene haka umm!
Na ce." Wallahi ka ba ni haushi sosai wai me kake ji idan kana gaba da mutum ne babu kyau fa kuma ba abin burgewa ba ne saboda kawai na baka shawara ka gyara sai ki dinga fad'a mini magana zagi na ne fa kawai ba ka yi ba."
Ya d'an yi shiru na wani lokaci kafin ya furta." Na gyara daga yau idan hakan zai kasance farincikinki shikkenan ko?"
Shiru na yi tare da ta'be bakina ya juyo da fuskata yana fad'in." Mu yi soyayya ko?''
Ban ce masa uffan ba ya d'ora kansa a saman kirjina tare da zagaye k'unguna da hannayensa yana sakin ajiyar zuciya.
Tun daga ranar Hauwa take yi mini vidiyo call a ranakun da yaran suke gida ta had'a ni da su mu jima muna hira.
Wannan dabarar ta kara mata kusanci da su kwarai da gaske na ji dad'i sosai kuma ina sa ran nan gaba duka za su manta da abinda ya faru su d'auketa a matsayin uwarsu kamar ni.
Ranar litinin da daddare muka yi waya da ita take gaya mini ai maigidan ya sanar da ita cewa za mu dawo alhamis nan da kwana uku kenan.
Na ce mata eh haka ya gaya mini ni ma.