Sashe 132
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Menene na damuwa don an ce mata matsafiya ashe da gaske matsafiyarce to ka gaya mata jinina dana yarana wallahi tallahi ya fi karfinta sannan wallahi ita dai ba takai maccen da zan yi wa hassada ba sai kuma abu na karshe wanda nake so ka sani cewa ni Amina Tajo ba a gabana yake ba balle har raina ya sosu domin hankalinsa ya karkarta can wani gefe, ai ita soyayya guda d'aya ce tun ta 'kuruciya kuma tuntuni na bada ita a wani wuri har abada kuma wani namiji ba zai ta'ba samunta ba a wajena."
Tsaki ya ja cikin kame-kame ya ce." kuna abu sai ka ce jahilan farko.
Duk da wanda ya ji wannan sakarcin da kuka yi ba zai yi muku kallon girma da mutuntawa ba."
Da sauri na ce." Ahaf to mu din mun gaya maka cewa muna so a yi mana kallon girma ne.
Ai ba mu iya abu don duniya ta yaba mana ba.
Riya ai babbar masifa ce da take saurin cinye dukiya da imani, Allah muke so ya yaba mana ba wasu jahilai b...
kashe wayarsa ya yi da sauri bai bari na k
rasa maganarta ba.
Ban damu ba, ni ma na ajiye tawa wayar zuciyata kamar ta tsage saboda tsananin tashin hankali da mamaki!
To ni ina ruwana da har sunana ya fito a rigimarsu asalima lokacin da suka fara bana wurin mai yasa ita Nabila ta yi jimilla ta had'amu mu biyu.
Shin da yawun ita Momin hakan ta faru ko kuwa.
Wannan amsar ba ni da mai bai ni ita dole sai shi ko ita Nabilar da ta kira shi a waya ta sanar da shi abinda ya faru.
kafafuna suka dinga kyarma tsabar rud'u da al'ajabi wannan masifar fa ita na dinga gujewa saboda yanzu har ga Allah ba ni son abinda zai daga mini hankali domin zuciyata ta jima tana shakar damuwa da rikici da tashin hankali.
Bayan haka kuma Ina tuna irin alkawarin da na yi wa Baban Saude ba ni so ya ga kamar na sa'ba maganarsa shiyasa nake ta ko'karin ganin na danne Hauwa domin kada lamarin ya yi tsamarin da zai kwa'be.
Ni dai aka yi wa da yarana, na yanke hukuncin da nake ganin shine daidai da abinda ya dace a rayuwarmu shikkenan magana ta mutu idan zai lashi takashin matarsa ko a kwalar rigita shi ya ga zai iya.
Cike da mutuwar jiki na ja jikina a hankali na zauna gefan gado gabana na bugawa da karfin tun d'azu a lokacin da
Hauwa da Nabila suke musayar yawu nake jin marata na murda mini kad'an kad'an.
Yanzu kuma sai abin ya kara tsananta gabad'aya ma saboda rashin nutsuwa da kwanciyar hankali na mance cewar akwai ciki na wata hudu da sati daya a jikina.
Na daddafa a hankali na shiga toilet na tsuguna da zummar fitsari jini ya biyo baya.
Gabana ya yi tsananin buguwa wanda ya yi daidai da karuwar zubar jinin saman wandon da ke jikina.
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! kalmar da na fara ambata kenan na tashi da kyar fafafuna na rawa na mayar da pant dina na fito tsakiyar d'akin na tsaya ina dawurwura alamun zubewar ciki ne ba wani abu ba.
Jikina na gyara cikin gaggawa na fito falo Hauwa tana d'aki sai Baba Tabawa a falon da yara sun zagayeta tana basu labari.
Kai tsaye d'akin na bi Hauwa tana kwance saman gado da wayarta a hannunta har yanzu babu sukuni a tare da ita ta tashi zaune tana kallona kafin ta ce." Ina kuma za ki je na gan ki da hijabi."
Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Na ce." Hauwa babu lafiya 'bari zan yi wallahi yanzu haka maganar nan da nake yi miki jini ne yake zuba asibiti zan je.
Ta yun'kura ta tashi da gaggawa tana fad'in." Bari na sa hijab muje Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Da sauri na fita daga d'akin jin yadda wani abu mai nauyi ya fado cikin pant dina.
D'akina ana shiga da gaggawa na zarce toilet na yi sauri na tsuguna abun ya fado kafin wani mashahurin jini ya biyo baya da tsananin ciwon k'wankwaso da gwiwa.
Bangon bandakin na dafe tare da rintse idona da k'arfi na kira sunan Allah ina jin shigowar Hauwa d'akin da yake ban rufe kofar toilet din sosai ba kawai sai ta shigo ta kamani itama sunan Allah kawai take kira tana fad'in." Shikkenan gashinan ma ya fita cikin sau'ki sannu bari yanzu na tura Masa'udu ya je pharmacy ya sayo miki wasu magungu
a ba sai mun je asibiti ba in sha Allahu, Allah Ya takaita miki wahala duk abinda ya yi saura zai fito cikin salama idan an yi amfani da maganin."
Ban damu da jin abinda ta ce ba tunda na san aikinta ne.
Ni kaina dama ba ni son zuwa asibitin dalili ban shirya ya ji yanzu ba.
Ita da Baba Tabawa suka gyara toilet din tsaf.
Baba Tabawa dai sai jajantawa take yi har da 'yar k'wallarta tana fad'in." Namiji ne gashinan har Ubangiji ya fara yi masa hallita.
Hauwa da suke aikin tare uffan ba ta ce mata ba ta yi mata shiru kawai.
Ina zaune a gefan gadon Baban ta zo ta fita da wata leda a hannunta tana fad'in.
"In banda abinki Hauwa ya za a yi a jefa d'an mutum a masai ina gaya miki gashinan Ubangiji ya fara fitar masa da hallitarsa.
Ido na bi ta da shi Hauwa ta fito daga toilet din tana fad'in." Magana ai ta mutu Baba ki je ki kai a bunne shi tunda haka aka koya miki a makarantar islamiyarku ta mutanan da."
Na dube ta a tsanake na ce." Abinda ya fita za a binne?"
Ta gyada kanta tana fad'in." Haka ta ce, shine ta tattare ta zuba a leda wai ita dai ba da hannunta za a zuba d'an mutum a masai ba."
Murmushi kawai na yi na ce." Hauwa kin san mutanan da camfi, wasu fa har yanzu suna wanke mahaifa tsaf su shiryata da likkafani su bunne.
Ko musulunci an ce bata da wani amfani
Ta ja tsaki tare da furta." Mu a asibiti ma wallahi tattarasu muke yi a buhu a kai bola.
Bata da wani amfani face zaman da ta yi da d'anka a ciki."
Shiru ya biyo bayan maganarta kafin ta numfasa a hankali ta ce." Wallahi Amina sai na ji ina ma ace ni ce na samu wannan matsalar kin san Allah ba na k'aunar cikin nan da yake jikina zan iya zubar da shi ni ma."
Da sauri na kalleta tare da furta." Ni ai ba da gangan na zubar ba Hauwa tsautsayi ne tare da tashin hankali da kuma rashin nutsuwa ya zubar da shi, yanzu lamarinki yana ba ni mamaki da tsoro wai shin me ya yi zafi ne don Allah don Annabi."
Ta yi shiru tana kallona da wani irin yanayi na damuwa.
Na gyada kaina ina zullumi da tunanin yadda zan sanar da mai cikin ya zube ya amince kai tsaye ba tare da ya juya lamarin ba shine kawai abinda ya fi damuna a yanzu domin zai iya kulla mini sharri a wurin magabatana tunda dama yana jin haushina.
Ita kuwa na fahimci yanzu gabad'aya ta daina tsoronsa balle ta daga masa kafa
Sai da na ci abinci tukkuna ta gwada mini duk yadda zan sha magungu
an da ta bayar a rubutuce aka sayo mini sannan na kwanta ita kuma ta tashi ta fita.
Bacci ne mai nauyin gaske ya d'auke ni wanda cikinsa na kasance cikin hargitsin mafarkai marasa ma'ana.
Shigowar kira a wayata dake gefena shi ya tashe ni cikin firgici na tashi zaune wanda ya yi daidai da tsinkewar jini da k'arfinsa wanda nake da tabbacin ya huda zanin jikina kuma babu makawa sai ya shafi mashinfidin da yake kan gadona.
Wayar na d'auka na duba Hamusu ne da sauri nasa a kunnena.
Jin shi cikin nutsuwa ya sanya hankali ya dan kwanta kad'an na amshi gaisuwar da yake miki kafin na tambaye shi su Kamalu da fara'a mai yawa a tare da shi ya ce mini gamu a ciki tasha a tare dama kiran da na yi miki kenan yanzu za mu wuce gida."
Na sauke ajiyar zuciya tare da furta." Alhamdulillahi, ka gaishe mini da Gwaggo idan an jima da daddare na d'an samu nutsuwa a lokacin zan kira ka sai mu k
rasa tattauna yadda za a yi."
Ya ce." To shikkenan anti sai na jiki in
sha Allahu."
Kashe wayar na yi na ajiye saman bedlamp kafin na zuro kafafuna kasa a hankali.
Baba Tabawa ta turo d'akin ta shigo.
Sai na sauke ajiyar zuciya domin na ji dadin shigowartata.
Ta nufo ni tana fad'in." Sannu ai na shigo ya kai sau biyar ba ki tashi ba ga la'asar ta yi babu kyau bacci a irin wannan lokacin......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.