← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 276

Sashe 153

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Alhaji Amadu ya makance da soyayyar Halisa ya zama duk bayan sati biyu daga nan abuja sai ya je Jigawa gidanmu hira wurin Halisa a lokacin itama bai kwanta mata a rai ba ta zo tana gaya mini abinda yake faruwa ni lokacin ma ban san yana zuwa zance ba tunda mun gama magana da Babansu Madina akan zai gaya masa cewa ta tsayar da wanda zata zaura kuma gaskiya ne akwai wanda suke soyayya a lokacin sai dai bai kai ga turowa ba, Amma dai gidanmu sun san da maganar mahaifinmu ma sun yi magana da mahaifinsa akan hakan.

Na dinga mamaki sosai sai dana tambayi Babansu Madina akan mai yasa bai gaya masa ba sai yace ya gaya masa ya'ki ha'kura ya ce tunda har yanzu shi wancan din bai fito ba shi ba zai janye ba.

Na kira ta zo na ce da ita duk lokacin da ya sake zuwa kada ta fito ta yi masa kora da hali domin a gaskiya ba ni son abinda za a yi shi daga baya rai yana b'aci Muna mu'amula da Maryam sosai a tsukin na tabbatar da cewar ba ta san abinda yake faruwa ba, kuma ba na son abinda zai ta'ba zumuncinmu.

Idan lallai ya zama dole mijinta ya kara aure to ya nema a wani wurin amma ba daga b'angarena ba.

Sati uku da yin wannan maganar ta sake zuwa gidana tana kuka sosai ta ce mini ya sake zuwa kuma Babanmu ya saurare shi.

Wata dabi'a ce ta mahaifinmu son bawa mai aure d'ansa.

Ni kaina don dai lokacin da maigidan nan ya fito da niyyar aurena da gaske yake domin gabad'aya ya shigo da na tabbatar da cewa mai mata Babanmu zai bawa ni. tana gaya mini sun yi magana sosai da Babanmu har ya ce ya jira shi zai yi magana da iyayen Murtala saurayin da suke soyayya idan har da gaske yake yi to ya fito a cewarsa masu son auran da gaske suna fitowa ba za a ce za a zauna jiran wani lokaci ba.

A lokacin shi Murtala din baya gari ya tafi can kudu Benin suna harkar gwangwani.

Amma ya ce mata yana dawowa zai yi magana domin a zo a kawo kudin aure.

Da ta gayawa Baban namu haka ya ce sai ya ji ta bakin mahaifin Murtala din tukkuna zai yanke hukunci.

Dole ta ha'kura ta tsaya sauraransa.

Lokacin Malam Shu'aibu bai rufe komai ba ya gayawa Babanmu cewa.

Har yanzu Murtala ba shi da taku daya wanda idan ya yi aure zai ajiye iyalinsa.

Can kudu (Benin) da yake zuwa tare da abokansa sana'a suke yi ta inada da 'karafuna da robobi, wannan shine amma tunda manemi ne arziki na Allah ne.

Shi ba zai hana idan mijin aure ya fitowa yarinya ta yi auranta ba domin tauye hakki ne a ce mace ta zauna jiran namijin da bai zama lallai ya yi mata adalci a gaba ba, tunda da yawa hakan ta faru samari su yi alkawarin aure da budurwa su tafi neman kudi idan sun samo sun dawo gida sai su ga ai sun fi karfin ajin wannan budurwa da suka bari a gida.

Wannan maganganun na Malam Shu'aibu maihaifin Murtala ya zaburar da Babanmu a cikin satin da Alhaji Amadu ya je gidan namu suka yi magana ya ce idan har da gaske yake kuma ya shirya auran ya turo magabantasa.

A tak'aice dai Amina na gaya miki da ni da Halisa sai ji muka yi an kawo kudin auran dubu dari biyun shekarun baya mai d'anko.

Kuka sosai Halisa ta zo gidana ta na yi mini kamar ranta zai fita tana fad'in ita kwata kwata bai yi mata ba tsoho ne.

A lokacin da take wannan koke-koken babu abinda nake tunani sai yadda za ta zauna da Maryam domin na fi kowa sanin yadda ta k'yamaci kishiya a rayuwarta.

Sosai na tausheta da rarrashi da ban baki har Babansu Madina ma da ya dawo ya sanya bakinsa yana ta kwarzanta mata nagartar abokin nasa yana fad'in ta kwantar da hankalinta ta yi mijin da za ta yi alfahari da shi.

Muka rarrasheta sosai ta ha'kura kwanta uku a gidan namu da yake duk gari daya muke gidan iyayenmu na kazaure gidana kuma a dutse a kwana na hudun Alhaji Amadu ya zo gidan wata'kila ya je can gidanmu aka ce masa tana nan
lokacin da rarrashi da ban baki na tursasa Halisa sauraran Alhaji Amadu suka dan jima a d'akin bakin maigidan suna hira kafin su yi sallama ya tafi ta shigo mini da kwalin waya sabuwa dal black berry mai kyau da tsada da kudi dubu hamsin wai kudin zance.

Na taya murna sosai a lokacin na kuma bata sharwari akan ta dage da addu'a domin duk lamarin da Babanmu ya kar'be shi da hannu biyu to tabbas ya yi istahara a kai ya gano alherinsa don haka idan tace zata tayar da fitina za ta fita zakka a cikinmu tunda ba ita kadai aka ta'ba yi wa irin haka ba.

Sannu hankali soyayyar Alhaji Amadu ta kar'bu a zuciyar Halisa yadda shi ma yake hidima da ita da gidanmu na tabbatar da cewa da gaske lallai auranta zai yi domin duk bayan sati biyu ko kwana goma yake zuwa wurinta har aka tsayar da maganar daurin auransu wata shida farkon watan maulidi.

Abinda ya fi tsaya mini a raina dangane da al'amarin shine yadda mu'amulata da Maryam bata raunana ba na shiga mamaki sosai jikina kuma ya yi sanyi k'warai na tabbatar da cewar duk wannan abinda yake faruwa Maryam bata sani ba domin kuwa da ta sani dole zan ga canji daga wurinta dalili kuwa shine na fi kowa sanin abinda tafi kyama kenan kishiya.

Na gayawa Babansu Madina cewa ni fa hankalina gabad'aya bai kwanta da neman auran nan ba, domin kuwa ina zargin abokinsa da munafurtar uwargidansa.

Da ya tambayeni mai yasa nake zargin hakan na ce masa naga ko kad'an ban ga canji a wurinta ba muna zumunci sosai domin ma a satin da aka sanya ranar daurin auran ta aikowa da yara kaya kowanne set biyu da muka yi waya ta ce mini sabuwar order ce shine ta d'ibar musu.

Shi kansa ya jinjina al'amarin sosai amma daga lokacin bai kara tayar da maganar ba ni ce dai abin ya dame ni a zuciyata domin sai nake ganin kamar duk ranar da ta san abinda yake faruwa za ta yi mini kallon munafuka ko kuma mai sonta kanta, ba kuma zata ta'ba yarda da cewa mijinta ne ya ga Halisa yace yana so ba za ta yi zargin cewa ni ce na had'a su.

Wallahi na shiga damuwa sosai da sosai domin kuwa ga'barar da Alhaji Amadu ya d'auka ta neman auransa ba mai kyau ba ce a ganina yafi alheri ya fito ya gaya mata akan ya 'boye mata.

Na kasance cikin zullumi da tunani a koyaushe nazarin da nake yi shine idan har Maryam ta samu labarin mijinta zai auri k'anwata wane kallo za ta yi mini.

Katsam watarana na ga text message d'inta ina dubawa na ga ta rubuto mini Aziza na gode sosai ashe tsakanina dake ba zaman amana, kema kin boye mini abinda yake faruwa, na d'auka ni dake yanzu mun zama 'yan uwana na ji don kin gaya mini mijina na neman auran k'anwarki Halisa menene ko kin d'auka zan tsananta kishi a kanta, ai abin gudu a kishiya shine a d'auko maka kwarkwasa wadda ba ka san ni ba, amma ni kam na sheda halinki kuma ina fatan haka Halisa take da kyawawan halaye idan har da akwai alheri a zamana da ita Ubangiji Allah Ya kawota cikin gidana, ke kuma na gode da 'boye mini da ki ka yi."
Jikina ya yi sanyi sosai da na gama karanta sakon data turo mini na zauna ina ta tunani da mamaki.

Dama nasan tuntuni ba ta san abinda yake faruwa ba sai yanzu da daurin auran bai wuce wata biyu da kwanaki ba sannan ta samu labari.

Hakika kowacce aka yi wa haka dole zuciyarta ta sosu Amma sai na dinga mamakin yadda ta sadada har ta samu damar yi mini text kuma cikin nutsuwa bata kalubance ni akan had'a baki muka yi da mijinta ba.

Na kwana da tunanin hakan a raina sai da gari ya waye tukkuna na kira ta a waya ta daga babu jinkiri muka gaisa sosai cikin ko'karin kare kaina na fara yi mata bayanin abubuwan da suka faru tun farkon neman auran har zuwa yanzu.

Ta dinga fad'in ai na d'auka ni dake babu rufi Aziza babban abinda ya ba ni haushi kenan yadda kike biye masa kema ki ka yi mini shiru wato sai dai kawai na ji an d'aura auran kenan kun yi mini adalci.

Na shiga bata ha'kuri da tausarta Ina nuna mata cewar ban san ta yadda za a yi na iya tunkararta da maganar ba domin ni duk a tunani na mijinta ya gaya mata.

Ta ce mini bai gaya mata ba ita ta fahimta da kanta yana neman aure da kuma ta yi bincike ta gane Halisa ce k'anwata.

Yadda muka fahimci juna sosai a wayar ya sanya mini kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyata na amince da cewa Maryam ta sakko ta kuma yi na'am da cewa kishiya abokiyar zama ce kuma hukuncin ne na Allah....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *07084653262*
Wallahi Amina duk yadda na so da ganin na sakar mata jiki kasawa na yi duk tsananin sabon kuwa da yake tsakaninmu sai ta dinga ba ni tsoro daga zarar na kalleta sai na tuna irin mawuyacin halin da Halisa ta shiga.

Duk da zato zunubi ne amma tsakani da Allah kenan na fi gazgata cewa itace ta jefi Halisa ta kuma juyar da hankalin mijinta akan lamarin gabad'aya.
Chapter 153 · 0% Book details