← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 234 OF 276

Sashe 234

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi kuka kamar kamar me har sai da ta karya mini zuciya haka muka rabu da tsananin tausayin halin da take ciki a raina.

Watarana sai labari in sha Allahu rabbi.

Ni kadai na sake kwana a gidan hakan bai dame ni sosai ba tunda dama na saba da hakan tuntuni kafin zuwan Baba Tabawa.

Mun yi waya da Hamusu yana gaya mini lefe ya hadu na ce ya kai musu can gidanmu su gani shima angon ya duba idan akwai abinda yake so ya kara a ciki to kafin ya kawo mini ni ma na gani
Mintina kad'an da gama wayarmu shi kuma ya kira na d'auka cikin ko'karin daidaita muryarta.

Ya amsa sallamar da na yi na ji yana fad'in." Muna Abuja gabad'aya da yaran yau Hauwa za ta tare a gidanta akwai gidana jikin massalacin da na gina wanda Kamalu ya dinga limanci shekarun baya kin gane shi ko?"
A takaice na ce."A a." Ya furta." Yana cikin estate din na mu can gaba.

Nan zata cigaba da zama ke kuma ki zauna a wanda muke ciki yanzu."
Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." To."
Ya d'an yi shiru kafin ya ce." Idan kin kammala Uzurin bikin naki sai ki sanar da ni ko?"
Na ce." Ba ni tsammanin zan dawo ko bayan bikin sai na haihu tukkuna."
Ya yi shiru yana jina bai ce komai ba.

Na ce." Ka ji abinda na ce ko?"
Ya nisa kafin ya furta." To na ji." Ya kashe wayar bai ja maganar ba.

Dariya ta su'bce mini ganin ya zama wani sukuku da shi ya daina ja'ina ni kuma na fad'i hakane kawai domin na tunzura shi tunda haihuwa da saura nan gaba kusan wata biyu kuma ba ni haihuwa a wata tara sai na goma ya shiga nasan ya amsa ne kawai ba wai don ya amince ba sai don gudun tashin hankali da alama shiri yake nema.
****
To komai ya yi farko yana da k'arshe haka zalika duk abinda aka sanyawa rana sannu a hankali zai zo a yi a kammala mun yi bikin Usaini cike da annashuwa da walwala an yi komai cikin rufin asiri kuma duk abinda yake na al'ada an yi wa amarya.

Gidanta na sanya a shirya mata shi sosai da kayan d'aki daidai gwargwado.

'yan uwan mamansa da Ummansu Hadiza Sahura ta jagorance su d'auko amarya domin ni ko kai kayan lefen ma ban samu sararin zuwa ba saboda hidima da gajiya sai da tare da kwana uku tukkuna na sanya Ayuba ya d'auke ni a mota ya kai ni gidan.

Ta rugunme ni kuwa tsam a jikinta tana murna tana fara'a irin wadda ta saba.

Ita dashi Usainin duka sun ba ni mamaki ganin yadda suke jifan junansu da kallon soyayya kamar dama can suna son juna aka yi auran.

Na jima a gidan tare da su domin tun safe nake har yamma na nuna mata abubuwa da dama tare da sanya mata lambar wayata a cikin sabuwar wayar da ya sayo mata na ce duk abinda ya shige mata duhu ta kira ni ta gaya mini.

Sai da na yi magriba tukkuna na kira Ayuba ya zo ya d'auke ni.

Muka yi sallama da begen juna.

Kwana biyu hankalina ya kwanta gajiya ta fara warwarewa Ayuba na bawa kudi ya sayo kayan abinci komai da komai na umarce shi zuwa gidan Fati kamar yadda na yi mata alkawari lokacin da ta zo mini.
****
To tunda muka yi waya kwanaki biyu da tafiyarsu bai sake nema ba har aka ci biki aka cinye babu wata magana da ta ratsa tsakaninmu tun bayan wadda muka yi da a k'arshe na ce masa sai na haihu nan tukkuna zan cigaba da zaman abuja.

Ban fad'a da niyyar hakan ba kawai tsokana na yi niyyar yi amma ganin ya share bai ce komai ba ni ma na sake gyara zama duk da cewar dai hankalina yana kan yarana amma nasan za su samu kulawa wurinsu Baba Tabawa tunda ya d'auke Hauwa daga gidan.

Da yamma sai ga kiran Nusaiba muka gaisa sosai tana tambayata yaushe zan dawo ta zo har sau biyu sai masu aiki da yara har ta na yi mini Allah Ya sanya alheri ta ji labarin na yi biki.

Ina jin dadin yadda yarinyar take girmama ni sosai na ce mata ina nan tafe a kusa in sha Allahu.

Muka yi sallama cikin mutunci.

Duk dai a daran ranar ina duba wayata sannu hankali na ga ya d'ora status ban ta'ba ganin ya d'ora hoton soyayya ba kai hotonsa ma ba d'orawa yake yi balle na iyalinsa ko na yara.

Jefi jefi dai yakan d'ora abu nai muhimmanci walau bangaran business din shi ko kuma tunasarwa tun bayan katin d'aurin auransa da ya d'ora satikan da suka wuce kuma shima bai fi da minti ashirin ba ya goge a lokacin da yake cikin rashin nutsuwa kafin ya samu mafita sai shakarun da suka wuce lokacin auransa da Hajiya Maryam nan zan ce naga hotona barkatai a status dinsa.

Sai kuma yau da ya d'ora hotona masu yawa.

Na farko farko nasa ne dana Samira Yayar Hauwa matarsa ta fari tun na kuruciya lokacin da suke soyayya.

Sai kuma na Hauwa da yaranmu gabad'aya na k'arshe ita dashi ne a sabon gida aka yi musu ya rungumeta ita kuma ta zagaye hannunta a k'ugunsa suna dariya gabad'aya.

'Kasan hoton ya sanya alamar heart da farkon sunansa da na ta.......Nan da nan na ji wani tashin hankali ya yi mini dirar mikiya na nemi yawu na rasa a bakina wani kishi mashahuri ya turnuko mini.

Idan ma da gayya ya yi domin ya dyaga mini hankali tabbas ya samu nasara domin lokaci guda na ji tashin hankali tunanika masu yawa suka fara bijiro mini a kaina wato suna can suna cin amarci a sabon gida har da hoto gashi nan katafaran falo wanda ya ji kaya na alfarma, da bai samu nasarar yin sabon aure ba ai gashi ya tare a sabon gida da matarsa suna sha'katawa har da rungume juna da d'aukar hoto cikin nisha'di da annashuwa.

Na ji tamkar an d'auki tabarya an rarrad'e mini kafafuna na ajiye wayar ko datar ma ban kashe ba na kwanta ina ko'karin sarrafa zuciyata dangane da yadda take hantsilawa tsabar kishi da tashin hankali.

Da na ce sai na haihu zan dawo ashe hakan wata dama ce na bashi domin ya huta.

Can kasan zuciyata na ce mini kada abinda ya yi ya dame ki Amina tunda ta wannan sigar ya b'ullo ku cigaba da tafiya haka har kin manta da halinsa kenan
idan bai sake yi miki maganar ba ki yi masa shiru bari ki haihu anan lafiya cikin 'yan uwa.

Abinda zuciyata take gaya mini kenan.

Wani sashe kuma na'kin amincewa da hakan domin kuwa gabad'aya hankali da tunani na yana can idan har na bari muka ci gaba da tafiya a haka Hauwa za ta yi mini dariya buk'atarta ta biya.

'Ko dai ita ta d'auki wayar tasa ma ta dora hotonan domin tasan lallai zan ga ni." Zuciyata take sake gaya mini haka.

Na girgiza kaina ko Hauwa ba ta d'ora hotonansu ba shi ma zai iya d'orawa domin ya jefe ni cikin damuwa, tunda duk ya bi hanyoyin da zai lallasa ni bai samu sa'a ba ya biyo ta wannan sigar.

Na sake shiga Whasap din hannuna na rawa ban ma san me zan duba ba kawai sai na ga an goge hotonan ma gabad'aya babu su.

Na sake shiga damuwa da nazarin hakan shine ya d'ora ko Hauwa domin ni a ka diora tunda an lura na ga ni sai aka goge wannan shine amasar, amma har yanzu tunanina ya kasa tantance mini wanda ya yi hakan a tsakaninsu.

Na jima ina addu'a samun sau'kin zuciya kafin na yi shirin kwanciya na kwanta gabad'aya ba ni jin dadi jikina da zuciyata.

Kiran sa ya shigo wayata da ban kai ga kashewa ba.

Na ajiye ta katse ban daga ba ya sake kira ta katse.

Ya kira ya fi sau biyar ban d'auka ba dana ji bacci yana shammatata ma sai na kashe wayar gabad'aya na yi addu'a cikin ikon Allah bacci ya d'auke ni......
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...

BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*157*
Ko da gari ya waye ban kunna wayata ba saboda takaici zuwa yanzu na tabbatar da cewa shine ya d'ora status din saboda ya ba ni haushi kamar yadda ya yi mini a wancan karon lokacin auransa da Hajiya Maryam.

Idan na ce ban ji haushi ba na yi karya abin ya ta'ba mini zuciyata sosai kuma ban sake gazgata matsanaciyar k'aunar da nake yi masa ba sai yanzu da nake ji har yanzu zuciyata ba ta daina zafi ba.

Tare muka yini da Sahura muna tattauna batutuwa masu yawa har take ba ni labarin irin saranda da sadudar da Idiris ya yi abubuwa da yawa sun kamace masa kudin da ya samu sun k'are tuntuni domin gabad'aya bai san yadda za a yi ya juya su su ru'banya ba birni ya dinga yi da auran da babu ribar komai sai ta haihuwa.

Na bata shawara sosai akan ta ajiye duk malamanta ta tallafe shi tunda har ya yi nadama ya kuma bata ha'kuri ai an riga an zama d'aya yaransu uku a tsakani don ma ba mai haihuwa ba ce da tuni sun fi haka.

Na kuma ce mata a duk lokacin da matarsa ta haihu suka ba shi d'ansa ko y'arsa ta kar'ba ta ri'ke ta had'a da yaranta gabad'aya domin da d'a da dukiya ba a yi musu mugunta domin ba kasan wanda zaka mora ba.

Wata'kila tsananin rabo ne ya sanya shi auran wanda idan ma ba a yi shi ta fannin da Allah da annabi ba za a iya samun rabon ta hanyar da Allah Ya haramta.

Sosai jikinta ya yi sanyi a wannan karon ba ta yi jayayya da maganata ba kuma da alama ta d'auki shawarar da na ba ta.
Chapter 234 · 0% Book details