← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 276

Sashe 74

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina dariya na ce." Haka ma Anti Yagana ta fad'a ni kuwa jinku nake yi ni nasan wanene shi, amma kin san wani abu ya ba ni tausayi ni kaina wallahi ba ki ga yadda ya sha wahala jiya ba saboda dukan da ruwa ya yi masa ya lafke zazzabi mura tari da ciwon kai da kyar muka rintsa ga uban sauro da zafi a d'akin."
"Humm! ki bari dai ya k'wace miki za ki yi kuka wallahi."
"Ba wani kuka da zan yi Sahura ha'kuri da juna muke yi ni dashi fa kuma kune kuke ganin kamar ni nake cutarsa, mu bar maganar nan haka sis tunda kin kasa fahimta amma ina so ki san da cewa amaryarsa na d'auke da juna biyu d'azu yake gaya mini."
"To shine me? kema Allah Ya ba ki naki rabon ba shikkenan."
"Sahura ba na jin fa zan yarda na sake haihuwa haka kawai ba zan yanki tikitin wahala da hannuna ba."
A takaice ta ce." Shikkenan ai." Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewa cikin takaici take ta ce." Wanki fa nake yi ki ka kira waya zan kashe."
Na ce." Da daddare wanki Sahura?'
"Ina da me yi mini ne?''
Ta ba ni amsa a kufule?"
Na ce." Ki had'a ki bayar zan biya."
"A a, ni menene amfanin lafiyata."
Na ce." Na ga alama rigima ki ke nema Sahura a ina zan samu mai kunshi ne?''
"Muna da su anan sosai."
Na ce." To ko za ki turo mini ita ta zo ta yi mini."
"Idan hakan ya yi miki sai na turo ta."
Na ce." Duk abinki dai ba zan yarda na yi fad'a dake ba Sahura."
Ta ce." Dama kin ji na ce miki mu yi fad'a, ai gaskiya d'aci ne da ita."
Tafad'a tana d'an jan tsaki.

Na ce." Ai na ji shawararki shiyasa ma na amince zan cigaba da zama dashi gashi har ina neman mai kunshi haihuwa ce dai na ce ba zan yi ba."
"To kada Allah Ya sa ki yi, idan kin samu cikin ki zubar kawai."
Ta datse kiran ba tare da na farga ba.

Dariya na dinga yi mamakinta ya rufe ni wai lallai sai ta gaya mini bakar magana alhalin ba ita za ta yi mini zaman auran ba, mai d'aki shi ya san inda yake yi masa yoyo.

To ashe da ya fita daga nan mutumin nan wurin Babanmu ya je.

Ban san abinda ya gaya masa ba, ni wajejen tara da rabi gama wayarmu da Sahura da kadan Babanmu ya kira ni ya rufe ni da fad'a har muryarsa tana rawa yana fad'in idan na janyo masa zagi a gari sai ya yi mini Allah ya isa tunda hakki na uba ya sauke mini amma ina nema lallai sai na guji aure na yi zaman kaina, muddin wannan hanyar zan bi to zai zare hannunsa daga kaina.

Ban yarda na yi jayayya dashi ba na dinga bashi ha'kuri har sai da ya huci na kuma yi masa alkawarin bin umarinsa.

Na jima ina jajanta lamarin yadda babanmu ya hasala yana nema ya yi mini baki shine abinda ya fi daure mini kai, Ina ganin da ya tsaya mun gama magana a tsakanimu zai fi ba wai ya yi yun'kurin had'a ni mahaifina ba.

Ba ni da lokacin tambayarsa akan dalilin da ya sanya ya yi mini haka hujjarsa kawai bukatarsa ta biya ta kowace hanya bai yarda da abinda ya aikata zai bata mini rai ba.

Da takaicin hakan na kwana a raina don har na yanke shawarar kiransa a waya na tambayi jikinsa amma hakan da ya yi mini yasa na share shi ban neme shi ba.

Da safe ya kira waya na d'auka muka gaisa ya fara tambaya ina maganarmu ta kwana.

Na nuna masa ban san maganar da yake nufi ba.

Ya ce." Maganar barin ki daga wannan gidan naki." Na ce." Yadda ka ce haka za a yi."
Ina ji ya sauke ajiyar zuciya tabbacin maganata ta faranta masa ya furta." Zan zo da daddare saboda gudun idanun jama'a, kamar yadda na fad'a sai mu je ki za'bi gidan da za ki tare."
A takaice na ce." Sai ka zo?"
Ya ce." Na gayawa Hajja tare muke dake kina can gidanku idan na zo sai mu je can ku gaisa ko?"
"To, kawai na ce masa.

Na kasa daurewa dai na furta." Na gaya maka duk irin abinda za mu yi ni da kai ka daina had'a ni da mahaifina menene ribarka ta yin hakan, ai ni ba na gayawa mahaifiyarka abinda zai daga mata hankali."
"Ni ma na gaya masa ne domin na rasa yadda zan yi dake, nasan shi kadai ne zai tursasaki ki bi umarina tunda ni kin raina ni, Amina ai ba zalinci a zamantakewar auranmu, to ni ma don Allah kada ki zalince ni, sakin da na yi miki kuskure ne da zafin kishi ba zan boye miki ba ina mutukar sonki wallahi akwai kuma wani bakin kishi da yake damuna akanki idan ya motsa mini ni kaina tsanar kaina nake yi balle wanda zai kusance ni.

Maganar nan ta mutu haka kada wanda ya ji, in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa muddin kin kiyaye faruwar hakan anan gaba.

Maganganunsa suka kashe mini jiki, tabbas kowane dan adam yana da dabi'a, kuma yana kuskure babu wanda ya cika cif kuma ha'kuri a rayuwar duniya ya zama dole mussaman a zama na aure.

Dukda namiji ba a cika yarda dashi dari bisa dari ba, amma a wannan karon na dan ji tausayinsa kad'an kuma kalamansa sun yi tasiri a gangar jikina ya gaji zaman lafiya yake nema.

Sahura duk da ba mu rabu da annashuwa ba jiya sai da ta turo mini mai k'unshin da kwatance ta zo har gidan tunda bashi da wahala a bakin titi yake.

Yarinyar ta iya kunshi sosai ta yi mini kafafu da hannuwa ja da baki wanda rabona da lallai tun na haihuwar baby Khadija.

Sosai na fito kamar wata amarya na bata dubu goma Yusura ta je ta rakata bakin titi.

Da ya zo bai shigo ba ya kira ni a waya ya ce na fito na same shi.

Hijabi nasa har kasa na rufe fuskata da nikab da zan fita na ce Yusura ta kulle gidan ta ciki idan na dawo sai na buga.

Can tsallake na hangi motar wata kala ce daban domin bata nuna alamun tasa ba ce wata'kila ya yi hakan ne domin kada jama'a su gane wanene tunda duk motacin da yake tu'ammalli suna da alama wannan babu wata alama sai ta lamba.

Sukairaju na jingine a jikin motar shi ma fuskarsa rufe da fece mark.

Ina karasawa ya risina mini muka gaisa kafin da sauri ya bud'e mini motar na fara ko'karin shiga yana hakimce cikin k'ananun kaya da rigar sanyi mai kauri a sama.

Kansa sunfuke da hula irin ta sanyi har kunne ya rufe idanuwansa sakaye da gilashinsa na ka'ida.

Na zauna sosai kafin Sukairajun ya shiga ya ja mota.

A hankali na furta." Barka da dare, ya jikin?"
Yana kallona ya amsa "Barkanmu dai ya gajiya?"
Shiru na yi ban bashi amsa ba, shi ma bai sake magana ba wata'kila ya yi hakan ne saboda kusantuwar Sukairaju tunda kallon da ya yi mini da farko shi ya tabbatar mini da cewa akwai magana a bakinsa.

Gudun aure littafin kudi ne.

Yi kokari ki sauke nauyi muddin kina karantawa
Gidansa na unguwar sharada kwanar ganduje wajan gidan Hajiya Mariya shi ya fi kwanta mini a raina dalili akwai alkarya a wuraran kuma daf da titi ne, bayan haka kuma ya yi kusa da wajan gidan Sahura dukda akwai 'yar tazara amma dai ba sosai ba za mu dinga samun sau'kin ganin ganin juna mussaman daga bangaranta.

Gidane iya gida wanda aka narka dukiya wurin gina shi, gini mai k'wari da nagarta da kuma ababen more rayuwa sabo ne ga dukkanin alamu ba a jima da gama aikinsa ba.

A gyare yake ko'ina sai da ba a shirya shi da furnitures ba da sauran kyale-kyalen zamani gidan ya yi mini sosai domin bai kai girman na legos ba ya yi daidai da zama babu tsoro da fargaba.

Ya ce tunda shi na zaba to shi ma ya yi masa gobe kuma zai sanya a shirya mini komai na ce to shikkenan.

Muka shishiga ko'ina muka duba muka hau saman benan ya bud'e wani d'aki a saman wanda shi kadai ne a dan shirye shi ma ba komai ba ne sai babban kafet da tuntu manya manya irin na sarauta uku, da manyan labuleye da suka kewaye d'akin.

Muka shiga d'akin yana gaya mini watani shida da suka gabata ya yi wani bako daga kasar senegal shine ya sauke shi a d'akin a dalilin tsaro da rashin yardar mutumin wai ya ji labarin najeriyar ta lalace da 'barayi masu satar mutane shine yake jin tsoron zuwa ya kwana a hotel.

Anan ya sauka tsayin sati hud'u har ya kammala abinda ya kawo shi ya tafi.

Dariya kawai na yi domin nasan mutumin yana da gaskiya najeriya ta lalace sai da ta katsan-tsanan.

Ganin ya nemi wuri ya zauna har da kishingida a jikin tuntu na ce masa yana da kyau ya tashi mu tafi saboda dare ya fara yi goma har da minti biyar ga gari na damuna, ga kuma yarinyar mutane na bari a gida ita kadai.

Bud'ar bakinsa sai kawai ya ce." Ai kin zo kenan Hajiya kayanki kawai zan tura Sukairaju yanzu ya d'auko miki." Ya fad'a babu alamun wasa.

Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Kai ma kasan hakan ba mai yiwuwa ba ne, ko ka manta da cewa na bar yarinyar mutane a gida, kuma me yasa Sukairaju zai je ya d'auko mini kaya ba ni da sirri ne, ai ba haka muka yi da kai ba.
Chapter 74 · 0% Book details