← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 276

Sashe 189

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na bashi adduoi sosai na kuma yi masa da kaina domin samun mafita da warware wa.
jiya suka zo nan da matarsa ya yi mini bayanin dukkanin abinda ya faru bayan rasuwar matarsa Maryam wadda itace musabbabin kwantar da shi tunda aikin da ta sanya aka yi akansa ni kaina ya tsorata ni ba don komai ba sai don ganin irin d'aurin da aka yi masa bayan lokacin da Ubangiji ya d'iba masa bai cika ba.

Na jima ina aikin warware asiri iri iri wannan ya ba ni mamaki ya kuma tsoratar da ni k'warai da gaske, kuma an cire tsoron Allah wajen aikata shi.

Ya yi shiru yana duban inda yake kwance tare da girgiza kansa tabbacin da gaske abin ya bashi tsoro da mamaki kamar yadda ya fad'a..

Hajja ta ce.'' Ni ai a zatona abokan kasuwanci ne ko wasu da ba sa kaunarsa suka jefe shi tunda kasan yadda duniyar take."
Ya girgiza kansa yana cewa iyalinsa ce Hajiya halima kin san ku mata wani lokacin da son kai kuke da kuma mugunta.

Ba dai a tara sani da Allah wata'kila ta ji a jikinta za ta riga shi mutuwa ne sai ta yanke shawarar yi masa d'aurin rai da ajali idan ta rasu a cikin biyu ko ya bi bayanta ko kuma ya kwanta kamar dai yadda yake a haka yana numfashi amma bai san a duniya yake ko a lahira ba."
Shiru ya ratsa kafin ya cigaba da cewa jiya na kwanta bacci bayan na yi sallar istahara akan lamarin domin kara tabbatarwa Ubangiji Allah Ya nuna mini ita ko ba ita ce 'yar fara mai karamin jiki ba da doguwar fuska?"
Hajiya Saratu da sauri ta ce." K'warai itace malam suffarta kenan."
Ya gyad'a kansa cikin jajantawa yana fad'in." Rahama sai ta Allah a wajen da take domin irin shirkar da take yi Allah Ya la'ancesu.

Ba za mu yanke hukunci kai tsaye a kanta ba amma tunda har son zuciya da mugunta ya sanya ta kafurta kanta ta iya yadda da juya zancen Allah wurin neman biyan buk'atarta tabbas alkawarin Allah baya ta shi."
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Na warware duk d'aurin da ta yi a kansa da yaransa zai tashi da izinin mai buwaya.

A yadda ta so shine ko ya tashin ya zama mutumin-mutumin kamar gunki tunda da ayar nan ta (Summunbukkum!) aka yi aiki akansa bayan ita suka had'a (Makisinafiyiabada) ayoyi ne masu zafi wurin dakusar da duk wani karsashin dan adam idan aka juya su ta gefan zalinci.

Ita kuma wannan kwalbar ya fad'a yana nuna musu ita ya cigaba da cewa." Kowacce laya akwai sunan mutum guda a ciki.

Amina Hauwa Kamalu Yusuf Khalil Hassana Usaina da kuma Minal.

Mallaka ce aka yi akan wad'annan sunayen da na zayyano da kuma jefa soyayya a zuk'atansu.

Hajja na kuka tace fad'in." To me ya yi mata ni Halimatu na ga da iyalinsa ta same shi.

Tsananin abotar da take tsakaninsa da Alhaji Amadu ya sanya da ya rasu ya aureta ni ma na bashi goyon bayan yin hakan tunda ya gaya mini a rubuce aminin nasa ya bar masa wasiyyar yin hakan.

Me ya yi mata da zafi irin haka da za ta yi masa wannan mugun asirin."
Ya ce." Son shi take ainun kuma macace mai zafin kishi abinda na fahimta kenan."
Hajiya Saratu ta ce." Mun gode sosai Malam Ubangiji Allah saka da alheri, yanzu ya yanayin jikin nasa." Ta fad'a tana kallon wajen da yake.

Ya ce." A nan za ku bar mini shi daga nan zuwa sati guda zai warware in sha Allahu rabbi zai tashi ya cigaba da gudanar da al'amuransa."
Alhaji Sa'idu ya ce." Malam abin nan ya jefe ni a rud'ani ba kad'an ba.

Ashe akwai irin wad'annan matan marasa Imani da tsoron Allah wallahi idan ana fad'a ba ni gazgatawa."
Ya ce." Akwai su da yawa muna ta fama da su.

Ita wannan nata akwai razani k'warai domin tana iya bada jinin adam akan biyan buk'atarta tana aiki da ba'kar iska kuma suna iya neman jinin kowacce irin hallita.

Kuma suna nan da yawa.

Abinda dai na fahimta ga sha'aninta shine macace mai zafin kishi da mugunta.

Kamar yadda na gaya muku da farko ni ba na bugun 'kasa akan neman sanin abinda Allah rufe bai bayyana ba.

Istahara irin wadda Annabi ya koyar ita nake a duk dare kan wata mas'ala da aka kawo ta gabana idan na kwanta bacci Allah Ya akan nuna mini abinda yake faruwa.

Iya fahimtata soyayyar da take masa ne ya sanya ta aikata masa haka saboda kishin ko bayan ranta kada wata mace ta more shi wannan shine
abinda ya halakar da ita har ta k'etare iyakar Ubangiji."
Hajja na girgiza kai tana fad'in." Kin yi kyawun dan maciji Maryam kin ci amanar mijinki, kin ci amanarmu da muka so ki muka kaunace ki, kuma duk inda muka zauna muke fad'in alherinki.

Kin zalinci Tajo da iyalinsa kin mutu ba ki nemi gafara ba zahiri ba mu yafe miki ba maryam "
Tasa gefan mayafi ta goge hawayenta cikin damuwa.

Ya ce." Matarsa ta zauna nan har tashon kwanakin dana d'auka in sha Allahu komai zai wuce kamar ba a yi ba."
Hajiya Saratu ta ce." To shikkenan Malam yadda ka ce haka za a yi Allah Ya saka da alheri amma za mu dinga zagayowa muna duba shi ko?"
Ya ce." Hakan yana da kyau in sha Allahu."
Muka fito daga d'akin a tare da d'an sasaauci ba kamar lokacin da muka shiga ba cikin tsananin tashin hankali.

Hajja ta fara rigima wai itama sai ta zauna.

Da kyar da jibin goshi Alh Sa'idu suka rarrasheta kan cewa ta yi hakuri su tafi idan ya so duk bayan kwanaki biyu sai su dinga zuwa.

Sai da suka yi sallar Azhar suka ci abincin suka yi shirin tafiya lokacin malamin ya yi b'aki ba su samu damar yin sallama da shi ba.

Tunda ba kasafai ake shiga wurinsa ba sai ya yi izini.

Da magriba yarinyar nan Hajara ta sake kawo mini dambu cikin langa tana fad'in.Matar yayansu ce ta ce a kawo mini tunda na jiya ya yi mini dadi.

Godiya na yi mata sosai na daure na ci ba don yana yi mini dadi irin na jiya ba sai don korar yunwa.

Ba ni son na kwanta ban sake ganinsa ba.

Na fito tsakargidan suna zaune iyayen da yaran.

Ban san ina su Sukairaju suke ba nasan dai tunda gidan karamci ne za a kula da su.

Ina so ya je ya d'an yi mini sayayyar cikin kasuwa ko dogwayen riguna ne na yi na yi na kira Sahura a waya ta'ki shiga ina so na ce mata ta je can gidana ina da kaya ta debo mini sai ta kawo mini ba a samu network mai karfi a gidan sai an fita waje a tsakargidan kuma idan ya hau sai ya sauka haka yake yi.

Ina tsaye da waya a hannu Malam Rabi'u ya zo yana gaishe ni na amsa cikin dan jin nauyi domin yanayin yadda yake risina mini na sanya ni jin kuny.

Ya tambaye ni ko ina da buk'atar eani na ce masa ina son na yi magana da Sukairaju.

Tare muka nufi wajan da aka sauke su.

Ya fito ganina a tsaye ya risina na ce." Garin nan babu network mai karfi kasan gidan Sahura ko?''
Ya ce." E, na sani."
Na d'an yi shiru ina kallonsa gabad'aya shima baya nutsuwarsa botiran rigarsa duk sun zube idonsa ya yi ja da alamun bai samu bacci ba..

Na ce." Gidana na can kuntau can ta koma da zama."
Ya gyad'a kansa yana kallona na ce." Ku je tare da ita can gidana na sharad'a za ta debo mini kaya sai ka kawo mini akwai mukkuli a hannunta."
Ya ce." In sha Allahu zan yi wanka yanzu na tafi amma ya jikin oga, mun tambayi Malam Rabi'u ya ce mana da sau'ki ."
Na ce." Da sauki alhamdulillahi amma ku taya shi da addu'a domin ita ya fi buk'ata a yanzu."
Ya ce." In sha Allahu Hajiya amma a wane hali yake ciki yanzu ya tashi ne muna ta so mu shiga mu duba shi ba a ba mu dama ba ."
Na ce." Yana dai kwance har yanzu yadda kuka d'auke shi Sukairaju."
Sai ya yi shiru yana kallona cikin damuwa.

Na juya ina fad'in.'' idan ka je ka dawo sai ka sanar da ni."
Na samu Rabi'u a soro a tsaye na ce." Ko za a yi mini iso wurin Malam zan shiga."
Da sauri ya ce.

Eh amma yana d'an wani aiki yanzu zuwa an jima idan ya kammala zan sanar da shi sai ki shiga ko"
Na ce." To shikkenan na gode sosai.

Ciki na shige gabad'aya jikina a sab'ule har in dai Hajiya Maryam ta samu nasarar nakasta mutumin nan ya tashi da wata tawaya ta cuci mutane da yawa wad'anda suka dogara da Allah suka kuma dogara da shi, halin da Sukairaju ya shiga yanzu abin jajantawa ne da tausayawa, to balle kuma yaransa da wad'anda suke makusantansa....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.
Chapter 189 · 0% Book details