← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 257 OF 276

Sashe 257

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga ni har ita Hadizan cikin damuwa muke amma ni na yi kokarin ganin na kawar da tawa damuwar domin samar mata da kwanciyar hankali.

Ba wani abu ba ne yake nukurkusarta face maganganun da Inna Uwani ta gaya mata d'azu.

Bud'e baki ma da 'kyar ta iya saboda damuwa.

Babu komai ai rayuwace duk wanda ya yi wa kaddarar wani dariya watarana Ubangiji shima zai jarrabe shi da abinda zai zama abin nuni da zind'e a idanun jama'a.

A fakaice na d'an dinga jan hankalinta da wayo da rarrashi ta ci abinci tana ta nuku-nuku da hawayen dake ma'kale a kwarmin idonta.

Tunda yau ma din a gidanta zai kwana ban tsammaci sake dawowarsa ba mussaman tunda ga irin rabuwar da muka yi wajan goma da ashirin muna falo muna kallo gabad'aya har da yaran ba su kwanta ba.

Ya shigo ri'ke da hannun Sultan yana ta sauke ajiyar zuciya yaro idonsa ya yi jawur da kumburi almar ya ci kuka ya k'oshi.

Khalil dake biye a bayansu Fadi." Yake yi ga ta can Usai din je ka."
Ya kuwa tafi wajenta da sauri yana sauke numfashi.

Na dubi Khalil din ina fad'in." Me ya same shi?"
'yar dariya ya yi kafin ya ce." Wai ba zai kwana a can ba shine yake ta ihu yana kiran Usaina."
Abin ya ba ni dariya da tausayi.

Na d'an janyo hannunsa ya taso ya tsaya kusa da ni tare da dora hannunsa saman cinyata na ce." Anan kai ma zaka kwana ko Sultan?"
Ya d'aga kansa.

Na furta." Ashe kwanciyar dole kuke yi a can din ko Khalil?''
Shiru ya yi bai ce komai ba sai ma ya yi k'asa da kansa.

Hadiza ta mike tana fad'in." Bari a gyara musu shimfid'a." Ta nufi d'akin nasu da sauri.

Na ce su tashi su bita su canza kaya sannan duk su yi alwala kafin su kwanta.

Duk abinda ake yi yana tsaye yana kallonmu bakinsa ya mutu da alama ya rasa abinda zai ce.

Bayan shigowarsu na dubi Khalil Ina fad'in" D'auko Usaini ka biyo ni dashi d'aki." Dama Hasan yana ri'ke a hannuna na tashi da shi a kafa'data kai tsaye bedroom dina na nufa ba tare da na sake kallon wajan da yake tsaye ba, a haka yara za su yi hutu a wajanta na kwanaki suna yi kamar za su mutu saboda kuka ashe da babu kowa a gidan ha'kuri kawai suka yi suka zauna tunda yanzu na dawo kuma sun nuna mata basu san wata ba bayan ni.

Da nata da nawan gabad'aya don ni sai nake ganin twins ma sai su zauna a hannunta ba tare da koke-koke ba nata ba su zauna ba Minal dai da Sultan sun tsaneta wallahi abin har mamaki yake ba ni.

Ita Minal yadda take bala'in sona shine abinda yake sanya mini sanyin jiki shi kansa Uban na lura da yadda jikinsa ya mutu abin ya fi karfinsa Hauwa ta haifar mini yara Allah mai iko......
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...

BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*169*
To ban san abinda ya kasance a tsakaninsu ba washe gari dai da misalin sha d'aya da wani abun Ladidi mai aikinta ta kawo musu kayansu kaf na can wanda suka yi amfani da shi bayan tafiyata kano da kayan sallar tasu da suke a hannunta pants takalmansu da kayan kitso abin wuya da hannu kowanne da na shi da alama duk ta had'a ta yi order din wurin Sadiyar gabad'aya girkina ne a ranar bai shigo ba sai bayan magriba tukkuna ya buk'aci abin bud'e baki na hada masa babu wata sakewa don sai nake ganin kamar akwai abinda ya boye mini.

Kunun tsamiya muka yi da k'osai yadda ya kusa shanye dogon jug hakan ya tabbatar mini da cewa kunun ya yi masa dad'i k'osan ma ya ci fiye da biyar saboda sakin manya muka yi.

Ya sha zo'bon dana had'a daidai gwargwado ya kammala yana godiya ga Allah kafin ya dawo da hankalinsa gare ni
Na yi shiru ina sauraransa." Akan maganar da muka yi dake kwanakin baya kin ce kina buk'atar a musanya miki wannan kamfanin ko?"
Na gyad'a kaina a nutse na furta." E, idan zai yiwu ba wai na raina kyautar ba ne kawai dai na fi gane business din da nake yi ina ganin idan na sake samun wani reshen anan za a samu alheri."
Ya ce." Shine dalilin da ya sanya ai na sake tambayarki tuntuni nake ta shawara a kan hakan kyautar za ta koma kan Hauwa tunda ni ba ni so a tashi kamfanin ko babu komai kadara ce mai girma da ta kafu tunda a 'kalla da kafa kamfanin zuwa yanzu ya haura shekara goma sha shida duk yanzu muna kan aikin fad'ad'a waninsa ammana akwai buk'atar shi d'in a cigaba da aiki da shi.

Na mallakawa Hauwa shi ke kuma akwai tallan wasu tsoffin shaguna da aka yi mini cikin kasuwar wuse din idan mun kammala da masu shi zan sanya ma'aikata su rushe tare da sabunta shi zuwa plaza din kamar yadda ki ka buk'ata a k'alla dai za a iya samun shaguna sha biyu 'kasa shida sama shida a hankali idan Ubangiji Allah Ya sanyawa abin albarka sai ki yi wadda ta fi wannan din ko?''
Na ce." Hakane na gode sosai Allah Ya saka da alhari ya kara arziki ya kuma jikan iyaye."
Ya dinga amsa cike da jin dadi yana jifana da wani irin kallo wanda na gama fahimtar ko na menene.

A daran kam na kar'be shi sosai kuma na yi kokarin ganin na yi masa bajinta wajan ganin na bashi farinciki yanayin yadda na tallafe shi ya k'ara dilmayar dashi cikin yanayi na shau'ki da sambatu irin wanda ba a tonawa wannan lamarin ai ba zai fasu ba idan da rai da lafiya a jikin gangar jiki.

Kwanaki biyu bayan wannan su Baba Tabawa suka dawo murna a wurin yara ba a cewa komai tsalle mussaman Sultan ya rirriketa tana dariya itama ta rungumeshi bakinta kamar gonar audiga gabad'aya sun canza da wata iriyar nutsuwa alamu ibadar da suka gudanar ta samu karb'uwa a wurin Ubangiji domin fes suka dawo da wani annuri na mussaman a tattare da su.

Dawowarsu ta sake bud'e wani sabon babi na farinciki a gidan ya kasance koyaushe cikin wasa da dariya da juna mussaman da bikin sallar ya gabato Mairo ta tsefewa yara kitso an wanke tas Taburni itace makitsiya Lad'ifa mai lalle saura kwana uku sallah ta zo ta yini tana yi wa yara washe gari ta dawo ta yi mini tare da Hadiza aikuwa tasha kudi wurin maigidan mussaman da ya ga na yaran ja da ba'ki ya fito sosai ya dinga duba kafafun nasu yana murmushi ta had'a kayanta ta tafi cike da farinciki dubu dari biyu kudin lalle kawai duk da Hajiya Maryam ta saba yi mata kyauta amma wannan ta yi mata bazata domin duk zuwan da take yi mini lallen ni nake sallamarta yau sai ga shi rabonta a ya rantse, ta samu kudi da turaruka da sabulai na hada mata da gyale mai kyau.

A daran mai dinkinsu ya aiko da shi kowanne k'alla gudu leces biyu a tamfa daya sai shadda daya wadda ta ci uban aiki abin mamaki har da na masu aiki set biyu Hadiza kuma aka yi mata uku manyan atamfofi.

Sai na 'kara mata da lece daga cikin kayana dake d'inke wanda ban sanya ba.

Takalmi na bata set biyu masu tsayin dunduniya duk sabbi da abin wuya da hannu.
gaskiya babu lefi ya yi kara ya kuma nuna halin dattako domin duk wanda yake karkashina yana sane da shi yana kuma ko'karin fitar da hakki ban ta'ba tunanin zai yi wa Hadiza d'inkin sallah ba duba da ganin yadda abubuwa suka yi masa yawa ashe yana sane da ita a gidan ya kuma fitar mata da hakkinta.

Wannan shine abinda ya gudana bayan ramadan mun yi bikin sallah cike da annashuwa da farinciki tun daga kan masu aikin gidan maza dake waje da na cikin gidan su Baba Tabawa kowa ya kasance cikin nishadi da jin dad'i.

Washe garin sallah yaran gabad'ayansu gidan Nusaiba suka yini bisa jagoranci Adam sai magriba suka dawo ta had'o su da snacks da yawa da kud'i Babansu ya dinga fad'a wai me yasa za ku kar'bo mata kudi ina lefin hidimar da ta yi musu.

Na ce sallah ce ai don ta ba su kudi ba lefi ba ne.

Sun je gidan Hauwa amma ba wasu wani jima ba suka dawo itama ta had'o su da tarin chocolates masu yawa har da sa'kon gaisuwa zuwa gare ni.

Cikin raina na ce tunda kin fara dafe wasu kadarori ai fitina ta kusa zama tarihi kyautar kamfanin da ya yi mata ya taka muhimmiyar rawa wurin dakushe mata damuwa tun bayan abinda ya faru ba ta sake fito da wani salon ba ga yaranta har yanzu suna hannuna.

Salim ya zo hutun sallah tunda yana can legos yana aiki a sabon kamfanin da suka bud'e shi ya dinga fita da yaran wuraran wassani ashe lokacin da Mamansu na raye haka yake yin jigila da su duk shekara ya ce ma saboda su ya dawo domin yin bikin sallah.

Sati daya ga sallah Inna Uwani ta shigo har gida wai sallama ta zo yi mini zata tafi.

Na bata turaman atamfofi uku da kudi dubu ashirin na ce ta kara guziri.
Chapter 257 · 0% Book details