← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 276

Sashe 194

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun d'an jima tare da shi suna tattauna mas'aloli da yawa kafin su tafi.

Shi ma ba su jima da tafiya ba ya tashi yana fad'in zai shiga ya kwanta gidan tunda yana da wajensa na mussaman a gidan wanda ya shirya shi domin yin rayuwa da matarsa ta farko Samira Allah bai kaddara zama ba.

Ina Uwani ta kasa yarda mu had'a Ido ban san dalili ba daga zarar na daga kaina ana hira sai ta yi saurin sunkuyar da kanta kasa na dinga tunani akan abinda yasa take yin haka.

Har dai abin ya zo yana ba ni dariya babu mamaki tana jin kunyanta ne da tsoron kada na tona mata asiri a wurin yar uwata tunda yanzu an yi walkiyya asirin Hajiya Maryam ya tono to ita kuma tasan na ganta da idona tana yarfa masa ruwan rubutu mai d'auke da magani a hanyar wucewarsa a shekarun baya.

Cikin zuciyata nace jininka ma yana yun'kurin cutar da kai ina ga kuma wani daga waje wanda yake karyar so.

Ai soyayya ta gaskiya itace ka so mutum tsakani da Allah ka so abinda yake so, ka gaya masa gaskiya a duk lokacin da ya kauce hanya.

Ka k'yamaci munanan ayyukan da yake yi kuma ka yi kokarin nuna masa hanyar daidai.

Babu wata soyayya ta gaskiya da za ta sanya ka illatar da wanda kake so ta hanyar son rai wannan zalinci ne a so ba cikakkiyar k'auna ba.

Muna nan zaune wajan daya da rabi Yusi ya dawo daga makaranta suna da lakca da sassafe ya fita ba don ya so ba.

Muna gaisawa yana tambayata ina Baba.

Hajja ta ce ya fita harabar gidan Sukairaju zai nuna masa inda yake.

Aikuwa ya tashi ya fita da sauri anan ya bar tarkacensa na makaranta ya fita da sauri bai damu da tsokanar da ake yi masa ba.

Ni hakan bai ba ni mamaki ba tunda na dade da sanin matsananciyar soyayyar da take tsakaninsu.

Shi Kamalu baya ma garin gabad'aya a jiyan da yamma suka tafi Abuja wurin wannan malamin professor Ma'kari.

Da yammacin ranar dai ya tura Sukairaju can gidanmu na sharad'a da kayan shi a can ya d'ebo masa duk abinda ya zama lallai zai buk'ata a son ransa mu tafi can mu biyu Hajja ta ce a a mu zauna anan din na tsayi sati tukkuna ko sati biyu idan ya so idan ma abujan za mu koma shikkenan.

Ganin haka sanya ni sanar da Sahura tunda ni ma ina da kaya a can ta sake d'ebo mini.

Na kira Hamusu na ce masa ya sayi yaduka masu matsakacin kudi kala bibbiyu ya bayar da d'inki Sukairaju da D'ahuru da kuma Ade ya san biyu Ade din ne bai sani ba na ce shi ma ba shi da tsayi sosai Amma dai duk ya fi su ki'ba da kad'an.

Na tausaya musu da zama da kaya daya babu dadi kamar akwai cutarwa.

A daran ranar na fara ko'karin yi masa amfani da rubutu da magungu
an da malamin ya ba shi tunda ya jadadda mini sosai kuma a gabansa.

Babu matsalar zuma ya had'a da ita gangariya ce farar sa'ka wannan da safe ya ce ya sha kafin ya ci komai.

Da za mu kwanta ne a lokacin da za a shafa na shafawar a duk jiki na ga shegantaka ya cire jallabiya har da gajeran wandon ya zauna a haka na ce babu kyau kallon tsaraicin mutum ya ce ai yana jin lokacin da malamin ya ce sai babu komai a jikinsa za a shafa rubutun har yana kara jadaddawa ya ce ki shafe mini ko'ina na jikina.

Ya kwanta abinsa babu kunya ba tsoron Allah da jin nauyin abinda ya yi.

Na jima kaina a sunkuye da rubutun a hannuna.

Ba wai shafawar ce matsala ba yadda zan kalle shi a haka shine damuwar na tashi na je na kashe fitila na dawo da lalube na zauna na fara shafa masa a haka a cikin duhun.

Bai yi yun'kurin yi mini komai ba har na gama bai kuma yi magana ba a takaice na ce." Na gama.'' Ya lalubi wayarsa ya kunna hasken yana ko'karin tashi zaune na d'auki wandonsa na ciki na bashi ya sanya sannan yasa jallabiyar ya koma ya kwanta.

Sai da na yi wanka da alwala tukkuna na kwanta gefansa wanda duk a tunanina bacci yake yi.

Ya janyo ni sosai ya rungume tsam.

Haka muka kwana bai yi yun'kurin yin wata mu'amula ta aure da ni ba sai dai duk juyi zai sake rike ni a jikinsa ya sanya bakinsa wuyana ya sumbuta da haka har asubahi ta yi muka tashi kusan a tare......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Littafin kudi ne akwai complete 2k a Telegram normal What'sapp group kuma 1k akwai a arewa pen domin biyan kudin karatu......0542382124....Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*131*
A ranar da muka wayi a gari a gidan Hajja muka dinga kar'bar mutane mabambamta ciki har da su anti Yagana Babanmu da Sahura wadda ta kawo mini kayan dana ce ta d'ebo mini.

Babanmu dai bai wani dade sosai ba ya tafi babu yadda ban yi da shi ba akan ya zauna ya huta ya kuma ci abinci sai asa direba ya mayar dashi gida ya ce a a tafiya zai yi ba zai zauna ba.

Ina jin dadin yadda yake ko'karin kama mutunci da kuma girmansa ba ya ta'ba yadda ya yi abinda zai zubar mana da mutunci gabad'aya.

Yini muka yi tare da su anti Yagana Ummansu Hadiza da Sahura ana ta hirar duniya Ummansu Hadiza dai ta yi shiru kanta a kasa sai dai ta yi d'an murmushi yanayinta gabad'aya babu dad'i zantukan da su anti Yagana suke yi akan Hajiya Maryam da irin zagi da tofin alatsinen da suke yi mata shine ya dan dameta wata'kila tunda itama tana ta'ba harkar bin malaman yasa ta damu tana ganin kamar anti Yagana da gayya take zage-zagen tun muna yara muka tabbatar da hakan yanzu ne da duniya ta juya mata baya ta gane babu sarki sai Allah ta daina, to babu kudin yi ma a yanzu amma ba zan ta'ba mantawa ba ita har zannuwanta take sayarwa ta tafi wajen malami.

Sai yamma Garba ya d'auke su a mota domin mayar da su gida ina jin anti Yagana tana gayawa Hajja za ta sake dawowa kafin ta tafi domin da Hajjan cewa ta yi wai su zauna su kwana.

To ita Sahura da mijinta duk da har yanzu ba wai sun shirya ba ne ta dai koma amma a yadda take ba mu labari ta'ki sakin jiknta da shi har yanzu kuma shi bai fasa shirye-shiryen auransa ba da ya rage wata biyu a daura tunda budurwa ce yarinyar da zai aura.

Shine fa take gaya mata cewa za ta dawo kafin ta tafi wanda ni nasan ta fadi hakane kawai amma ba dawowar za ta yi ba.

Kwananmu hud'u a gidan Hajja mutumin ya warware sosai ya ma fara fita yana duba ma'aikutunsa nan yana kuma yin baki a kai-akai.

Ranar da muka cika sati daya a gidan Hajja da sassafe ya tafi
bunkure bayan la'asar ya dawo sai da ya yi wanka ya ci abinci tukkuna yake gaya mini wai an bashi sa'ko ya kawo mini.

Na ce sakon menene ya ce bai sani ba yana mota wata yarinya ce wai Hajara dariya na yi ina fad'in." Ai k'awa na samu a gidan.

Ya gyad'a kansa bai ce komai ba.

Can kuma ya ce gobe za mu tafi Abuja Amina hankalina na kan yara.

Na d'an yi shiru Ina kallonsa mun yi waya da Kamalu shekaran jiya tunda yana garin tare da ayarin abokansa masu neman da'awa.

Ya ce mini ya je gidan domin duba yaran suna nan lafiya lau har Hauwa ta ba shi turare.
Chapter 194 · 0% Book details