← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 230 OF 276

Sashe 230

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin ce a bi ra'ayinki an bi me yasa kike wulakantani ne Amina."
Jikina ya d'an yi sanyi jin muryarsa har tana d'an rawa bai ba ni tausayi ba ko kad'an saboda nasan akan abinda ya sanya shi rawar murya din duk yanayi ne domin ya yaudare ni ya more ni kuma Hauwa ta ci ribar abinda ta shirya domin dai ban yarda da cewa Hajja ce ta turo ta mu kwana tare ba.

Na ce." Game da kudin sadakin Hajara nawa ka ba su?"
Shiru ya yi mini yana girgiza kansa tabbacin ya kai 'kololuwa wajan Jin haushin tsakin da na yi masa wanda ni ma ban san lokacin da ya fita ba tsabar haushinsa da nake ji ne.

Na sake maimaitawa ya ce." Ban sani ba."
Na ce ." Ya asalin baka sani ba, ka fad'a don Allah a baka hak'kinka ai ba lefi ba ne."
Ya ce." Ba zan fad'a ba Amina ke kina jin kin yi k'arfin da za ki nuna mini wani abu ne.''
Na ce." A a wace ni idan da irinku a wuri ban isa ba kawai dai ina so mu biya ka hakkinka ne saboda kada nan gaba a yi mini gori."
Ya yi shiru bai tanka mini ba can kuma ya ce." Yanzu za ki ba ni ha'kkina ko kuwa?"
Na ce." Wane hakki?" don har ga Allah ban zanci hakkin kwanciya yake nufi ba ."
Ya d'ora duka hannuwansa biyu saman kirjina yana fad'in." Wannan dai mallakina ne ke kan ki ba ki da karfin ikon da nake da shi a kansa.

Idan na d'ora hannu a kai ki tankwa'be kina neman rahamar Allah kuwa?"
Ya fad'a yana dam'kar d'aya da k'arfi cikin mugunta gasu tubarkallq sun sake kumburi dalilin abinda nake d'auke dashi sun cika sosai.

Na sake tankwa'be hannun ina fad'in." Allah Ya hallice ni da abina a jiki ka ce ka fi ni iko da shi abincin yarana ne masu zuwa."
Ya kuwa gigice yana fad'in." Abincin mu dai, wallahi ba ki isa ba, abincinmu ne da ni da su."
Na juya da kaina gefe ya matso ni sosai yana yi mini magana.

Na girgiza kaina tare da cewa." Ba zai yiwu ba sai Hauwa ta tafi ka yi hakuri ni tunda cikin nan ma ya tsufa na daina jin wani abu
Ya ce." Ni kuwa a cikinta nake koyaushe kin matse ni da yawa Amina ba kya gudun hakkina ya kama ki uhum! mu d'an yi soyayya kad'an kafin Hauwa ta shigo sai mu kwana tare kada ta ce ba a yi mata daidai ba."
Na ce." To bari kawai idan ta shigo sai ku yi soyayyar gabad'aya."
Ya sake rikicewa yana cewa." Ya ki ka tsara yanda zai kasance."
Na rasa da wane mizani zan auna maganarsa.

Ya na tsara yanda zai kasance me yake nufi.

Na gane kawai a rikice yake maganarma ya fad'e ta ne cikin rashin hayyaci.

Ina sane na 'kyale shi ya dinga abinda yake so ba don komai ba sai don na nuna mata cewa kowace mace da irin tata kissar.

Gidana kuma ta zo sai abinda ta gani.

Wajan sha biyu da wani abu muka sauko kasan ni da shi bayan ya samu gamsuwa da abinda ya buk'ata.

Yaran sun yi bacci duka a saman kujera tana zaune zuru da tibi a kunne duk ta muzanta ganin sakkowarmu ta yi kasa da kanta fuskata a had'e kamar ma kuka ta yi.

Na wuce d'akina ban tsaya a falon ba na ji yana cawa da ita." Tashi yaran su je su kwanta.

Amina bude musu daya d'akin, shi Khalil ya zo mu kwana tare a d'akina."
Dakinsu Baba Tabawa da Yusra kenan anan suke kwana na bud'e kamar yadda ya buk'ata.

Ita da shi suka fara tashin yaran.

Na yi shigewata d'aki a raina ina fad'in." Ki zauna da ni a gida daya ki zama 'yar aikina Hauwa, zan kuma ga abinda gobe za ta haifar ni daku ne gabad'aya.

Na rufe kofa tare da cire kayan jiki na sanya na bacci na yi kwanciyata ban sake sanin wainar da suka toya ba ba.

Da asuba gari ya d'an fara haske ina saman dadduma ya shigo ya jira na kammala muka shafa addu'a a tare.

Na gaishe shi babu sakewa na ce." Zan je gidanmu idan an jima zan kuma tafi da yara."
Ya yi d'an jim kafin ya ce." Babu damuwa amma ya za a yi da abin kari kada su tashi a bacci ko."
Na ce." Za ka iya bayarwa a sayo abinda za su ci ba ni jin zan shiga kicin gaskiya wanka zan yi na shirya."
Ya ce." Wace banzar magana ce wannan Amina ni zan sayi abinci bayan ina da shi a gidana, ban yi wannan lalacewar ba."
A takaice na ce." To sai ka shiga kicin din ka yi da kanka kada dai ta shigar mini kicin."
Ya dinga kallona cike da takaici ya ce." Jiya ba na gaya miki cewa zan raba muku gidan ba me yasa kike da neman fitina ne Amina.

Ya kamata duk abinda ki ke ji a ranki ki ajiye a gefe mu fahimci juna gabad'aya mu gyara kuskuranmu Hauwa bakuwa ce anan gidan."
Na ce." Bakuwarka dai ai ni ban gayyace ta ba."
Ya sake had'e rai yana fad'in." Kina yin abubuwan da suke nema su wuce gona da iri fa.

Ko babu
Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
dangantaka ta aure a tsakanina da yarinyar akwai dangantaka ta jini sannan uwar yarana ce kiyayyar ki a kanta ta tsananta."
"Humm kawai na ce tare da tashi na bar shi zaune bandaki na shiga.

Koda na fito baya d'akin na yi tsaki cikin raina na fara shirya jikina zuciyata cike da abubuwa ma su yawa.

Wajan takwas na fito falon yaran sun shirya ko ita ta yi musu wanka oho suna zaune a falo gabad'aya har da Baban nasu ita tana kicin domin fitowata na ji kamshin k'wai na tashi raina ya baci sosai. amma sai na daure na cigaba da amsa gaisuwar da suke jero mini.

Shi kuma ya zura mini ido da alamar na gaji da wannan abubuwan da suke faruwa.

Kai tsaye kicin din na nufa na same ta tana soya dankali da k'wai ta d'ora ruwan tea yana ta k'amshi citta da kaninfari.

Na cika da mamakin karfin halinta.

Kai tsaye gas din na kashe ta yi sakato tana kallona.

Na furta." Ba ki da hurumin yi mini yadda ki ke so a gidana Hauwa ko ni na gayyato ki ne, me ya sa za ki shigo mini kicin har ki saki jiki kina soye-soye."
Ta d'an yi murmushi tana fad'in." Amina manya ai kya bari mu gaisa ko?"
Na ce." Dube ni nan Hauwa ba ni buk'atar gaisuwar na ce miki tambayarki nake dalilin da ya sanya ki shigo mini kicin."
Ta yi 'yar dariya cikin raini ta ce.

" To Hajiya masu gida ki goya ki kai gidanku."
Ta ajiye cokalin hannunta ta kama hanyar fita zalo-zalo na ce." Sakarai kawai."
Ta juyo a fusace tana cewa." Amina ai ba a sakarai d'aya sai dai sakarkaru biyu."
Na ce." Hakane da ke da ta Bauchi ko?"
Ta zura mini ido da matsanancin mamaki tasan dai inna Uwani nake nufi
Sai ta rushe da kuka mai karfi." Amina ni ke zagi, inna Uwani ce sakarai mahaifiyata." Ta fadi maganar a daidai lokacin da ya shigo kicin din ta dinga wani irin kuka hawaye na kasa tsere a kumatunta.

Yana tambayarta ta yi shiru ta kasa magana ta jingina jikin wardrobe.

Can ya juyo kaina ganin yadda fuskata take ya sanya shi fad'in." Me ya faru ke ba kya jin magana da rarrashi ko?"
Na ce." Ni na ce Hauwa ta zo gidana?" Na katse shi ta hanyar yi masa wannan tambayar.

Ya ce." Gidanki ne ko nawa?"
"Gidanka ne amma kaima na fi ka iko dashi wallahi duk zan iya da ku."
Ya gyad'a kansa kamar zai rushe da ihu ya ja hannunta suka fita bata sake tanka mini ba tunda ya shigo sai ta yi shiru kawai tana kuka.

Wai na goya gidan na kai shi gidanmu.

Magana ta gaya mini a fakaice ashe babu dadi.

Ita da uwarta duka sakarkaru ne na fad'in su yi yadda za su yi da ni.

Na same su gabad'aya har yaran sun tsuru-tsuru na wuce daki ban sake kallonsu ba.

Muna waya da Usaini ya shigo da wani irin b'acin rai a tare da shi ya cire wayar daga kunnena ya sanya a aljihunsa.

Na zuba masa ido babu fargaba domin nasan ta gaya masa na ce da mahaifiyarta sakarya.

"Tunda ki ka iya zagin Inna Uwani Amina za ki iya zagin mahaifiyata yanzu kin kyauta kenan abinda ki ka yi daidai ne mace ta zo gidanki ki yi mata irin wannan cin zarafin iyaye fa aka ce miki duk iyashegen da ki ke ji da shi ina fa da yadda zan yi a kanki na kyale ki ne ganin kina da juna biyu ba ni tsoron kowa mace ni nan da ki ka gan ni sai mahaifiyata."
Ya fad'i maganar kamar gaske da 'kumaji har da zare mini ido.

A raina na ce a banza ai ba zaka iya fad'an ba Alhaji.

Na dube shi sosai tare da fad'in." Da farko daka tambaye ni maganar abin kari ban munafurceka ba na ce a a ba zan yi ba, akwai masu yin abinci a gari ka bada kudi a sayo musu mai yasa za ka ce ta shige mini kicin ko ajiya ta yi mini ne?"
Ya rasa abinda zai ce mini can kuma ya gyad'a kansa yana fad'in." Tunda kuke rashin hankalinku ban ta'ba jin lokacin da Hauwa ta zagi wani naki ba abin ya wuce kaina ya tsallaka iyaye kuma duk lalacewar inna Uwani ai idan da mutunci da sanin daraja uwace a wajenki."
Na ce." Tunda haka ta gaya maka na zage ta mu tafi a haka kawai idan kalmar sakarai ce zagi to zan sake maimaitawa ai iyaye ba su fi iyaye ba."
Jikinsa ya yi sanyi sosai ya juya ya fita bai sake yin wata magana ba.
Chapter 230 · 0% Book details