← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 276

Sashe 168

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa
*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
Kirana da aka yi a waya shi ya tashe ni wajejan goma da ashirin da biyar na safe.

Koda na duba lambace babu suna na daga tare da sallama sai na ji muryar Idiris mijin Sahura nan da nan na daidaita yanayina.

Domin zahirin gaskiya ni ma haushinsa nake ji dangane da abinda yake ahirin aikatawa.

Tabbas nasan kiran nasa baya rasa nasaba da matsalarsu.

Muka gaisa jikinsa a sanyaye ya fara yi mini bayanin halin da ake ciki Sahura ta rufe gida sannan ta tattara yara da kayansu ta kaiwa mahaifiyarsa bayan tasan bata da k'oshin lafiya.

Yanzu haka sai a shagon dake jikin gidan ya kwanta shagon da yarana suke d'inki kenan yana jadadda mini a cikinsu ya kwanta cike da alhini da damuwa.

Ban katse shi ba har sai da ya kammala tukkuna na ce." To wallahi ni dai Idiris ba ni da tacewa akan wannan lamari.

Ina ganin ka kyaleta kawai tunda tafi buk'atar rabuwar sai ka je ka yi rayuwarka da sabuwar amaryarka yara kuma ai duk sun girma babu wanda za a yi wa wahala a cikinsu."
Da damuwa ya ce." Saboda fa kusancin da yake tsakaninku ya sanya na kira ki Amina, me yasa za ki gaya mini haka ke don Allah idan na ce zan rabu da Sahura ba za ki yi mamaki ba?"
Na d'an yi murmushi babu nisha'di na ce." Babu mamakin da zan yi Idiris abinda aure na mutum biyu ne idan ka gaji da ita zaka sawwa'ke mata mana ko kuma ka nemi hanyar da za ka k'untata mata."
Ya ce." Yanzu dai don Allah ki rarrasheta wallahi ba wai don na wulakantata zan yi auran nan ba.

Ina son Sahura ina kuma buk'atar cigaba da zama da ita ki rarrasheta ki bata ha'kuri ta dawo mu cigaba da zama in sha Allahu babu abinda zai faru domin itama yarinyar da zan aura bata da matsala 'yar gidan tarbiya ce wallahi bata da fitina."
Na yi dariya ina mamakin maganarsa tun bai zauna da yarinyar ba yana shedar halayenta tabbaci kenan ba zai janye ba.

Na ce." To shikkenan zan yi magana da ita zuwa an jima in sha Allahu."
Da sauri ya furta." Zan kira ki domin na ji abinda ku ka yanke amma don girman ki tausheta ta dawo na ware mata turmi biyu daga cikin lefen da nake had'awa sannan zan bata dubu hamsin sai ta sayi kayan kwalliya."
Na ce." To shikkenan.

Da takaici na katse wayar ban tsaya na k
rasa sauraran karshen maganarsa ba.

A tunana ai Sahura tafi karfin turmin atamfa biyu da dubu hamsin, ita wahalar nawa ta yi masa tunda suka yi aure har yanzu ma cikin yi masa hidima take.

Da yammacin ranar muka yi waya da ita na gaya mata Idiris ya kira ni a waya akan abinda yake faruwa.

Kamar yadda ya buk'ata din na fara rarrashinta da kawo mata misalai ta yi shiru tana saurarena don har ina murna ina cewa ta sauko a zuciyata sai da na gama maganata tukkuna ta ce ." Ba ni buk'atar atamfofinsa ya ri'ke har da k'udin ya k'arawa amarya Amina, takarda zai aiko mini da ita yanzu zaman da nake yi kenan."
Na ce" Sahura akan kishiya dai idan ki ka kashe auranki na kusan shekara ashirin da wani abu wallahi kin ba ni kunya kuma na raina wayonki, ki bari ta shigo mana ki ga kamun ludayin zaman.

Haba don Allah ki jure mana."
Kashe mini wayata ta yi ta barni ri'ke da tawa a kunne da mamaki.

Bayan magriba Idiris din ya dinga kira wayata ina kan daddauma ina jan carki kamar yadda na saba.

Koda na duba na ga shine na ajiye wayar kawai na cigaba da abinda nake yi shi kuma bai fasa kira ba.

Hakan ya yi daidai da shigowar maigidan wanda shi ma tunda ya fita da asubahi bai sake shigowa ba.

Ya d'auki wayar yana dubawa sai ya kalle ni kaina a sunkuye kawai sai ya daga tare da sanyata a kunnansa jin muryar namiji na ji yana fad'in." Wanene?" ban ji abinda Idiris din ya ce masa.

Na ji yana fad'in." Mijin Sahura ne to bari ta kammala tana azkar ne zuwa an jima sai ka kira."
Ya yi shiru na d'an wani lokacin kafin na ji yana fad'in." Amin Ya Allah, ma sha Allah, ka kira zuwa an jima kadan." Daga haka sai ya kashe wayar ya ajiye har na kammala na juyo ina dubansa ya ce." Mijin Sahura ne ya kira ki a waya ina fatan lafiya?"
A tak'aice na ce." Lafiya ba lafiya."
Ya dube ni sosai yana fad'in." Suna da matsala ne?"
Ina ko'karin cire hijabin jikina na furta." Aure zai ka'ra shine take bore har ta tafi gida."
Ya yi d'an jim kafin ya furta." Na kan rasa inda tunaninku yake tafiya wataran Amina, daga zai kara aure domin raya sunna sai ta ta tafi ta bar dakinta menene amfanin hakan."
Cike da takaici na ce." Ai ba a ce kada ya kara ba, ya bari ya tsaya da k'afafunsa tukkuna bashi fa da cikakkiyar
sana'a, wallahi Sahura wahala take sha a hannunsa kuma ta yi masa hallaci tunda suka faru a gidan haya suke shekara kusan ashirin da uku da auransu buge-buge yake yi itace karfin kula da gidan tun kafin ma ta samu aiki a kamfaninka haka take gwagwarmaya.

Amma shine daka kawai an yi musu rabon gado ya samu miliyan takwas ko wata biyu fa ba a yi da raba musu kudin ba ya fara yun'kurin karin aure har yana tara lefe a dakinta.

Ita kuwa ta kulle gidan ta gudu ta kai masa yaransa wurin Babarsa."
Dariya ce ta sub'ce masa ya dinga yi har ina mamakinsa na d'auka ai zai cigaba da goya masa baya.

Ya ce." A lallai bai kyauta ba kuma da gaske bai yi adalci ba.

Yadda ki ka gaya mini yanzu ai ita ta yi masa hidimar da ta zarce ta miliyan takwas to me yasa tunaninsa bai kai ya saka mata da alheri ba sai da kishiya.

Bai kyauta bai kuma yi daidai ba, in banda rashin tsinkaye ai ba aure ya kamata ya yi ba a yanzu ko?"
Da sauri na ce." Kwarai kuwa abinda itama take ji wa haushi kenan zai bata turmin atamfa biyu da dubu hamsin abinda ya kara ba ni haushi dashi kenan."
Ya ce." Kin ga kira mini Sahurar yanzu na yi magana da ita."
Na zauna gefansa ya miko wayata na lalubi lambata bugun farko ta daga cikin bala'i ta fara fad'in." Amina ki kyale ni don Allah idan har kin san ba maganar arziki za ki gaya mini ba, na gaya miki na gama yanke hukunci, idan kema za ki goyu da bayan Idiris din sai nasan a wani aji zan ajiye ki."
Ina binki bashi idan kin karanta ba ki biya ni hakkina ba
Na ce." Yi ha'kuri mai da wukar sis, Yallabai ne zai yi magana dake." Ta yi shiru ba ta ce komai ba sai na mik'a masa wayar da sauri ya kar'ba a nutse ya kira sunanta "Sahura."
Ina ji ta amsa cikin ladabi." Na'am ranka ya dad'e ina yini?"
Ya ce." Lafiya lau ya kuke ina yara?"
Ta ce." Kowa lafiya lau Sir."
Shiru ya d'an biyo baya kafin ya yi gyaran murya ya ce." Kin san abinda nake so dake?" Ta ce." A'a.

"
Ya ce." Amina ta yi mini bayanin duk abinda yake faruwa, ki yi hakuri ki koma dakin mijinki ki cigaba da kula da yaranki, shi kuma ki kyale shi idan har kina da hakki sannu a hankali Allah zai saka miki.

Ni kuma zan yi miki alheri domin ki zauna a wadace cikin walwala zan canza miki gida mai kyau sannan zan baki kudi ki dinga wata sana'ar a gefe sannan ki cigaba da zuwa aikinki kina taimakon yaranki da 'yan uwa, kada don mijinki zai kara aure ki yi fushi ki dasawa kan ki k'unci yaranki su shiga damuwa ki daure na wani lokaci komai zai wuce ."
A sanyaye ta ce." Na gode ranka ya dad'e, Allah Ya saka da alheri, shikkenan in sha Allahu zan koma kamar yadda ka buk'ata."
Cike da jin dadi kuwa ya furta." Ni ma na gode sosai Sahura, zan yi magana da Jamilu sakatare na nan kamfanin naku duk abinda yake da akwai zai yi miki bayani in sha Allahu maganar abinda na ce zan baki kuma za ki gani a daran nan."
Ta dinga godiya har muryarta tana rawa.

Ya mik'o mini wayar na kar'ba a d'an sanyaye na ji dad'i sosai da ya shiga lamarin gashi har da alherinsa ko babu komai yana da lada a wurin Ubangiji.

Muka yi sallama da ita tana fad'in." Na kara yi masa godiya.

Na dube shi a hankali na ce." Mun gode sosai Ubangiji Allah Ya saka da alheri."
Bai kalle ni ba ya ce." Ba ni details dinta yanzu ."
Ya miko mini wayarsa na kar'ba na sanya masa kamar yadda ya ce.

Ya ce." Ke nawa ki ka bata gudummuwa?"
Na ce." Gudumawa kuma?"
." Dannar kirji kuke cewa ko?"
Dariya na yi na ce." Ban bata komai ba wallahi."
Ya d'an Harare ni yana fad'in." To yaushe kuwa za ta saurari rarrashinki irin wannan ana had'awa da hasafi sai ki ga an shawo kan matsalar."
Na dinga gyada kaina ina dariya lallai ne kudi suna iya sayan komai amma ban da rai da rayuwa.
Chapter 168 · 0% Book details