← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 276

Sashe 138

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin kudin aure na kudi yar uwata kada k8 karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." Aikuwa ka ce mata mun gode sosai." Suka juya za su fita sai na ce." Kai Khalil dawo ku shiga ku gaida Mamanka mana." Ya ce." To.

D'akinta suka nufa tare da Usaina tana bin sa zugwi-zugwi a baya.

Na sauke ajiyar zuciya bayan shigewarsu na juyo kan mai lallan cikin nutsuwa ta gaishe ni na amsa ina fad'in." Wane iri za a yi mana ja ne ko baki?"
Tana fito da kayan aikinta daga cikin wata 'yar jaka ta ce." Duk biyun Ina yi wanda kuke so za a yi."
Na ce." To a yi mini duka ja da bakin.

Amma dai ba na son dogon zama.

Ta ce." In sha Allah daga nan zuwa magriba komai ya kammala."
Khalil ne ya zo ya gifta ni yana goge fuska.

Da sauri na ce." Kai menene ." Bai ce mini komai ba ya wuce yana dafe idonsa.

Kawai na ji fashewar kukan Usaina cikin gwarancinta tana ce wa." Mama ta dake shi a fuska."
Da wani irin yanayi na ce ." Mai ka yi mata?"
"Ba komai." Ya fad'a da sauri ya kama hanyar fita kamar ma a tsorace yake Usainar ta bi bayansa itama da sauri.

D'akin na shiga na ji motsinta a bandaki tana ta kakarin amai.

Can na bita sai da ta gama tukkuna ta wanko fuskarta ta fito koda ta gan ni a tsaye a bakin kofa ba ta ce mini komai ba ta nemi gefan gado ta zauna.

Laulayin ne ya dawo mata sabo da kuma hatsaniyar nan da muke ciki gabad'aya duk yanayinta ya canza ga wani uban haske da ta yi fau sai wasu k'ananun kuraje da suka feso mata a fuska.

Na ce." Wai ba ki da lafiya dama Hauwa."
Tabe bakinta ta yi kafin ta girgiza kai ta ce." Amai ne ya takura mini wallahi cikin 'yan kwanakin nan, amma in banda shi babu abinda ya dame ni."
Na gyad'a kaina a sanyaye na ce." Allah Ya bada lafiya." A takaice ta amsa da Amin.

Na ce." Khalil ya fito yana kuka Hauwa ba kya neman zaman lafiya ko, kin fi kowa sanin abinda mutumin nan ya tsana a rayuwarsa a daki yaran nan mussaman shi Khalil din daga gaisuwa kuma sai duka fisabillahi , ai ba shi ya yi miki ba."
"So na ke a yi ta take ai, shiyasa na dake shi.

Ni ma ai iyayene suka haife ni.

Ya dake ni a fuska kwanaki yanzu kuma yana dukan zuciyata da iyakacin karfinsa.

Bai isa dai ya canzawa towo suna ba."
Shiru na yi Ina nazarin maganarta kafin na ce." Duk wannan bai ta so ba, za ki dasawa yaron nan k'iyayyarki da jin tsoronki a cikin ransa. zai kara yin nesa dake tunda tsakaninku duka ne da kyara da hantara, don girman Allah ki daina."
Hannu ta daga mini sai kuma hawaye suka k'wace mata ta ce." Kin san irin rad'adin da nake ji a zuciyata kuwa Amina ? wai Yaya Tajo shine yake fifita wata bare wadda ba su had'a dangantakar komai ba akaina.

Na haihu dashi Bata haihu dashi ba.

Jinina ne shakiki.

Ita kuwa a duniya suka had'u, amma ya tozarta rayuwata a kanta.

Wallahi har na mutu ba zan yafewa matar nan da alhalinta ba."
"Kai!

Innalillahi! don darajar Allah Hauwa maganar nan ta mutu haka na rantse da Allah ta ishe ni.

Ki gyara tsakaninki da shi kawai ki daina duba wata dangantaka namiji ne za ki ga abinda ya fi haka fa."
Shiru ta yi ba ta ce komai ba, na ce." Ga mai lalle ta zo za ta yi mana, ki fito falo."
Ta dube "Kin ga na yi kama da wadda za ta yi wani lalle yanzu?"
Na ce." Kwarai kuwa, ai ke ya kamata ma ki yi kitso da lalle domin jan hankalin mijinki ku daidaita har ya janye abinda ya ratsa tsakaninku."
Ta ja tsaki tare da gyara kwanciyarta tana fad'in." Kada Allah Ya sa ya janye wallahi babu abinda zan yi, ai ke ce matar gida.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl
Momyn Hajara GHT supplements
Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah
Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya
Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah
Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal
*95*
Na gyad'a kaina ba tare da na sake yin wata magana ba na juya na fita daga d'akin gabad'aya zuciya sam babu dadi, abin nata kuma ya fara ba ni haushi ya daga gyara kayanka sai ba'kar magana.

Ai duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubar da ruwa.

Ni ban ce Hauwa shigar rigima ba domin tun lokacin da na ga ta dage tana ta tsalle akan hatsaniyar nasan lallai da akwai abinda zai faru.

Ta sha gaya mini ita ta gaji da auran to yanzu kuma an sake ta tana kuka.

Ni tausayinta ma nake ji wallahi ga ciki ga rashin zaman lafiya da miji dalilin da ya sanya kenan nake tausarta ta yi hakuri akwai takaici kwarai da gaske da ciwo namiji ya nuna baka da wani amfani a wurinsa domin dai sakin da ya yi mata ko a kwalar rigarsa bai damu ba ya dasa mata k'unci yana gefe yana cigaba da gudanar da rayuwarsa.

Wadda take yi domin ita tana can hankalinta a kwance mijinta yana neman hanyar da zai faranta mata da tun farko ta yi amfani da shawarwarina da duk hakan bai faru ba ta lallaba ta zauna a dakinta.

Yarinyar ta iya lalle sosai tana da zane mai ban sha'awa ganin kamar ta d'auki mai wahala da jinkiri ya sanya na ce ta takaita domin ba ni son zama shine dalilin ma da ya sanya ban fiye yin k'unshin ba.

Baba Tabawa ta kammala aikinta ta fito ta zauna a falon muna hira jefi-jefi har yarinyar ta kammala tsaf ta had'a kan kayanta.

Na ce." Ai kina da acct ko?"
Ta ce." E, ina dashi amma Momi ta ce da ni kada na kar'bi komai."
Cike da mamaki na ce." Saboda me?" Tana murmushi ta furta." Da farko antina ce take mata lalle sai ta yi aure ni ma dama tana koya mini shine na kar'bi sana'ar duk k'arshen wata nake shigowa cikin estate din nan naku akwai wad'anda nake yi wa bayan Momi din.

Mun saba k'warai da ita ta yi wa antina komai haka zalika ta samawa babban yayanmu gurbi a daya daga cikin shagunanta dake garin nan, gashi nan har ya yi aure shekara daya kenan matarshi ta haifi mace ya sanya mata sunan momi din wato Maryam muna kiranta da Sahiba."
Da murmushi a fuskata na ce." Duk da haka dai ai ni ma alheri zan yi miki ganin irin yadda ki ka b'ata lokaci wurin yi mini ado da zananan henna mai kyau, shin ko ba kya so mu saba ne?"
Dariya ta yi kafin ta ce." Kai anti wannan ba komai ba ne akan wanda nake yi don na ji kin ce na takaita ne shiyasa amma da wanda zan yi miki sai ya fi wannan tsaruwa."
Na ce." Wannan din ma ya burge ni sosai na gode miki, amma ai ko turare kya kar'ba ko."
Ta yi kasa da kanta tana murmushi.

Ni ma murmushi nake yi can kasan zuciyata kuma ina tunanin idan har mutane za su dinga yabonka tun kana raye tabbas babu abinda zai hana ka sha'kar rahamar Allah idan ka gushe! wato ita dai Momi ko'ina alherinta zagayawa yake yi duk wanda ala'ka ta had'aka dashi muddin ya santa to alherinta zai fara gaya maka.

Muna nan zaune muna hira da ita budurwar wadda take gaya mini sunanta Lad'ifa iyayenta yan asalin jalingo ne aiki ya kawo mahaifinsu nan abuja amma k'aramin ma'aikaci ne..

Ta duba agogon da yake tsintsinyar hannunta na dama wanda nake hasashen tana d'aura shi ne domin duba lokaci a sa'in da ta d'aurawa mutam lalle da kwance shi.

Ta ce." Yanzu sai a cire tunda ya samu awa biyu cikakku.

Dama dalilin da ya sanya ban tafi ba kenan.. ta d'auko wata leda babba da cokali mai dan fadi daga sama cikin nutsuwa ta fara cire lallen kafin ta d'aye salatif din zanen ya fito d'au ya yi bala'in kyau da kamawa.

Baba Tabawa fadi take yi "Ashe haka kike da cin lalle Amina amma ba kya damuwa da yi."
Na ce." Duk da haka dai ai lallensu daban yake suna yi masa hadi na mussaman."
Da kaina na cire na hannun ya tafi da ni sosai nan da nan na ga ba dawo mace har ina jin dadin duba hannuna.

Na ji tana ce wa." Sai gobe zai sake fitowa sosai." Tsaf ta goge mini kaf ta shafe duk inda lallen yake da wani abu sannan ta sake had'a kayanta a karo na biyu.
Chapter 138 · 0% Book details