Sashe 226
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu na farko da za a yi shine idan yaro ya nuna irin wad'annan abinda na lissafa da farko ayi maza a kai shi asibiti domin auna shi don tabbatar da lafiya mu kuma a matsayinmu na likitoci daga lokacin muke fara namu taimakon da shawarwari ga iyaye akan yadda za su kula da yaronsu don kiyaye tashin ciwon a kai kai."
Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya kafin ya nisa cikin nutsuwa." Ya cigaba da cewa." Allah Ya gafarta Malam ban zo nan wajan domin katse sunnar manzon rahama ba face bada shawara a matsayina likita amma ina ji Malamai da yawa na fad'in cewa akwai maganinta mu dai a likitance wannan matakin muka d'auka domin dakushe k'ara yawaitar haihuwar masu dauke da wannan lalura."
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin ya yi gyaran murya a nutse ya furta." Babu wata cuta da Allah bai yi maganinta ba Iliyasu ban katse maka hanzari ba kuma ban raina sanin da Allah ya yi muku ba a matsayinku na masu taimakawa.
Kafin na bawa Alhaji Tajo auran yarinyar Hajara na nemi zabin Allah na kuma yi istahara akan lambarin a kuma duk sanda zan wayi gari nakan tsinci kaina cikin farinciki don ganin zuriata da ta abokina za ta had'u waje daya domin haifar da wata zuriar da ba za mu iya iyakance adadinta ba.
Mu bar wa Allah da ni daku gabad'aya mu yi imani da tauhidi cewa babu mai kashewa da rayawa face shi wannan karamin dalilin da kuka zo gabana da shi ba zai zama silar da za a warware wannan alkawarin ba da ya zama saura k'ankanin lokaci a d'aura shi.
Ba mu isa mu hana Allah abinda ya shirya ba domin duka a can baya tun kafin mu kan mu mu zo duniya iyayenmu suke auran juna ba tare da wannan binciken na nunawa Allah iyakarsa ba.
Iyaye suka haife mu lafiya lau babu ciwo ko kad'an mu ma muka rayu lafiya muka auri matayenmu babu ciwo kuma suka haifar mana da zuria masu tarin yawa da ba su d'auke da wata lalura makamaciyar wannan don haka wannan magana da kuka zo mini da ita ba za ta dakatar da ni daga abinda na niyyata ba a yau idan har Alhaji Tajo ba kai zaka nuna mini cewa ba ni da alfarma a wajenka ba."
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! abinda yake ta fad'i kenan a cikin ransa zuciyarsa na wani irin dokawa da tashin hankali da damuwa.
Babu fa wani dalili da zai sanya shi yin rayuwar aure mai nisan zango da yarinyar nan dalili kuwa shine yana da burin kara samun haihuwa.
Tabbas Allah ne mai yin yadda ya so idan ya so zai iya bashi lafiyayyun yara da yarinyar ba kamar yadda yake hasashe ba amma rashin nutsuwa da lamarin ya sanya masa fargaba yarinyar ba tsararsa ba ce gabad'aya koda an daura masa aure da ita ba ya tunanin zai iya had'a shimfida da ita balle har ta kai ga ta d'auki ciki suka shiga cikin zullumi akan abinda za a haifa mai lafiya ne ko mara lafiya.
Amina ta riga ta zama k'addararsa shine dalilin da ya sanya yake ji a zuciyarsa wannan dalilin ba zai sanya ya rabu da ita ba kuma zai iya cigaba da zaman aure da ita.
Amma dai a yanzu ba ya tunanin zai sake yarda ya auri wadda jininsa da nata bai daidaita ba.
Maganar Malam Nuhu ta katse tunanin da yake yi ya ji shi yana cewa..........
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*152*
Suka juya gabad'aya suna kallonsa a lokacin da ya fara magana kamar haka.
" Ya kamata a k'ara duba wannan uzurin da suka zo da shi Allah Ya gafarta Malam nasan da wahala Alhaji Tajo ya d'auki aniyyar tozartaka a irin wannan ranar da gabad'aya ta zame mana abar alfahari da farinciki mussaman da muka tabbatar da cewa wanzuwar lamarin shine abinda ka fi buk'ata a yanzu domin sake kulla zumunci mai karfi tsakaninka da abokinka Alhaji Ibrahimu Allah Ya yi masa rahama da gafara."
Suka amsa da "Amin gabad'ayansu kafin ya sake nutsuwa sosai ya cigaba da cewa zahiri wannan lalura da suke magana akanta akwaita kuma har yanzu tana k'ara yaduwa a wasu wuraran da ba su d'auki abinda ya zo a zamanance da muhimmanci ba.
Malam ko dai ka manta shekarun baya ashirin da biyu da suka wuce muka dinga dawaniya da mai sunan Inno har Allah Ya d'auki ranta a asibitin Murtala na cikin garin kano wanda sai a lokacin ne gabad'aya muka san ga cutar da ta zama ajalinta."
ABINDA YA FARU.
Shekaru ashirin da bakwai can baya Malam Nuhu ya auri matarsa ta fari Lantana wadda a yanzu ba ta raye ta rasu dalilin farfadiya tunda tana da mutanan b'oye sa'i da lokaci sukan tashi.
Auran soyayya suka yi a cikin kauyen nasu kamar yadda al'ada take duk da wannan lalurar tata ta farfadiya hakan ya zauna da ita tunda yana sonta shi kansa mahaifinsa ya bashi gudumuwa kwarai wajan yi mata magani idan ciwon ya tashi.
Da ta samu ciki sai wahalar da take sha ta sake ru'banya tunda kowa ya san yadda masu wannan ciwon suke shan ba'kar wahala a duk lokacin da iskar ta buge su a kan titi ne ko a kasuwa ko a gida sun dinga katantanwa kenan da jikinsu suna malkwadewa tare da taune lebensu da kumfa dafara mai hade da jini.
Suka dinga bige ta a kai akai don babu wanda ya tsammaci za ta haife wannan ciki da yake jikinta lafiya saboda yadda take jigata.
Cikin ikon Allah da lokacin ya zo ta haihu kalau aka samu 'ya mace wadda ta ci sunan Inno Ramatu suke kiranta da Rahma.
Tun tana yarinya jinjira ta fara nuna alamun rashin lafiya ido ya jirkice daga fari zuwa yellow cikinta ya yi kurcici sai siraran kafafu da hannu.
Da masifar kukan tsiya da zafin jiki domin koyaushe idan aka ta'ba jikinta radau ake jikinsa.
Da yake kauyene a wancan lokacin da babu wayewa sosai kamar wadda suke ciki a yanzu sai duka daga can b'angaran iyayenta dana shi Malam Nuhu suka alak'anta lalurar da yarinyar take yi akan shafar aljanu dalili uwarta tana da su kuma sun tashi sosai a lokacin da take d'auke da cikinta a jikinta..
Suka dukufa wajen yi mata jike-jike na maganin gargajiya daga can b'angaran malamin kuwa yana yi mata rubutu da tofi ana bata tun tana jaririya ta saba da shan sassaken magani mai d'auke da ruwan rubutun da kakanta yake yi mata.
Har hayaki sukeyi wa yarinyar saboda duhun kai har rukiya sai da Malam D'aha ya yi mata da abin ya ci tura duk a tunaninsu aljanu ne suke tsotse ta kuma suke hana ta bacci da daddare suke firgitata tana kwanan kuka.
Duk wannan wuyar da yarinyar take ci Allah bai amshi abarsa ba sai da ta yi shekaru hud'u tukkuna cikin halin rai da rayuwa domin a duk lokacin da ciwon nata ya tashi hayaki ake yi mata aka dingi bata sassake da saiwa wadda aka dafa da jar kanwa.
Wajan cirani can Katsina uban suke hira da abokinsa yana gaya masa halin da yake ciki da yarinyarsa wannan mutumin a irin bayanin da ya yi masa ya gane cewa babu maganar iska sai dai idan wata lalurar ce shine ya ba shi shawara kan cewa ya kaita asibitin cikin gari na kano general ne na kowa da kowa domin yawanci ma mutanan kauyen sun fi morarsa har ya ta'ba bashi labari shima daga nan k'atsina garinsu ya ta'ba kai mahaifiyarsa asibitin na Murtala aka dubata har ta kwanta na tsayin sati hud'u kuma ta samu kulawa kwarai ya ce masa su jarraba yin na asibiti ko za a dace.
Koda ya dawo gida ya sanar da Malam D'aha da kyar ya amince da a d'auki yarinyar a tafi da ita a ganinsa abinda yake damunta bai had'a hanya da asibiti ba domin duka sun d'auka cewa lalurar uwarta ce ta shafe ta.
Ba a tafi da uwar ba tunda tana halin ciwo Inno kakarta ita ta goyata suka tafi dawowar da yarinyar ba ta yi ba kenan domin kwanansu daya a asibitin ciwon ya tashi da masifar k'arfi likitoci suka dinga kai kawo a kanta inaaa babu jini ya kone ta rasu.
A wannan lokacin ne likitan da yake tsaye a kan yarinyar ya zauna ya dinga yi musu bayanin musabbabin abinda ya yi ajalinta babu iska sai tsananin ciwon da Allah ne kadai yasan maganinsa.
Duka ba su gazgata hakan ba a lokacin suka dawo gida da gawar yarinyar daga lokacin ne Malamin ya ce kada a sake daukar wani daga cikin zuria'arsa a kai asibiti duk cuta akwai maganinta cikin al'kur'ani mai girma.
Shekara biyu bayan rasuwar yarinyar uwar ma Allah Ya d'auki rayuwarta sakamakon wata fad'uwa da ta yi iskokai da suke tare da ita suka bugeta a bakin kofar bandaki daga lokacin jikin nata ya'ki dad'i har dai rai ya yi halinsa.
Wannan shine abinda ya shud'e a shakarun baya kuma a iya gwagwarmayar da yake da sauraran redio hurd'a da mutane bambamta tunda a can katsina wajan da yake gudanar da sana'arsa birni ne ba kauye ba ya tabbatar da cewa duk bayanin da ake yi akan wannan lalura gaskiya ne ya gazgata itace silar yarinyarsa ta fari Rahma wanda ada can suke d'auka shafar aljanune.
Malaman D'aha ya yi shiru jikinsa ya d'an shika kadan a lokacin da yaron nasa ya tariyo masa abinda ya shud'e a cikin wasu shekaru da suka gabata.