Sashe 273
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai shegen k'iwa da rashin yarda saboda tsabar bala'i lallai Sahurar ba zata huta ba ko uban da ya haifeta bata yarda dashi balle danginsa ta ma'kale mata na dinga mamakin wannan lamari kwatankwancin abinda Minal take yi mini yanzu ko wurin aiki da ita take zuwa Hajja kuwa sai 'kara mata karfin gwiwa take yi tana fad'in kada ki sare kada ki gaji wata'kila zata ji kan ki da d'a da dukiya ba a yi musu mugunta.
Muna tare da su tsayin kwanaki uku babu irin batutuwan da ba mu tattauna ba abinda Hauwa kuwa ta aikata ya yi bala'in ba su mamaki amma jin irin hukuncin da maigidan ya yanke a kanta ya sanya zuciyoyinsu suka yi sanyi.
A ranar da suka shirya tafiya wasu bakin suka dira Hamusu da Usaini kowanne da iyalinsa sai kuma Yusi da Saminu.
Hajja kuwa ta samu 'kawa 'yar gidan Usaini mai sunana kenan itama suna kiranta da Minal ta dinga tsokanarta da faratu haske ne da ita kau har ta so ta fi ubanta haske Hajiya Saratu na tsokanar Hajara kamar ba goyonta ba, ita yarinyar ashe mahaifiyar Ummansu Saminu ta d'auko domin duka hasken fatar ta gada musu duk da ta tsufa amma tana nan kar kar da ita Fulani ne na asali.
Kwana biyu da zuwansu Yusi yake gaya mini Kamalu daf yake da dawowa gida domin sun yi magana da shi a cikin satin da ya wuce na ce bai gaya mini ba duk da kuma mun yi magana da shi kwana hud'u da suka wuce ya dai tabbatar mini da cewa daf yake da ya kammala abinda ya kai shi amma bai fada mini ranar da zai dawo ba, amma ba na mamakin kan cewa ya sanar da maigidan tunda kusan ya fi sakewa da shi fiye da ni.
Kwanaki biyu a tsakani suka tafi Hajiya Saratu ma ta riga Hajja yin gaba domin ta ce ita zata zauna ta kwana biyu tukkuna har na ji Yusi yana tsokanarta wai sai ta taso sun tafi haka yake janta da tsokana irin wadda ma bai yi wa Gwaggo irinta ba tsakanin Yusi da Hajja akwai amana da kuma 'kaunar juna har da rantsuwa wai gidan babu dad'i idan bata nan ta ce masa ba wasu kwanaki za ta yi da masu yawa ba.
Shi kam babu halin zama makaranta ga kasuwa ba ma shi da ishashen lokaci na kansa.
Hajja ta sake sosai da jikokinta tana jan su a jiki da wasa da dariya har dai suka sake tunda sun gano cewar kakarsu ce wadda ta haifi Babansu idan suna gidan karad'insu kad'ai ake ji a falo tana ta biye musu Baba Tabawa na yi musu dariya.
Minal ce take ma'kale da ni da Mufida suna dawowa daga makaranta a wasu lukutan ko uniform ba ta zuwa ta cire za ta same ni a d'aki ta'ba nan ta'ba can ta yi ta han'koro ita lallai sai na bata k'anwarta.
Cikinsu har khalil babu wanda ya taba daukarta sai dai gani daga nesa Babansu ya ce ko za a ba su sai ta kara wayo tunda ga abinda likita ya ce kuma alhamdulillahi ta yi lafiya tana shan nono sosai ta yi baccinta na rana da dare babu kuka mai zaburarwa sai dai tak'aitacce dalili duk wasu sharad'ai ina bi yadda muka yanke ni dashi rainonta yana hannuna duk rintsi babu buk'atar taimakon masu aiki gudun yin abinda zai sa'ba da lafiyarta.
Yau kwananmu talatin da tara ya kama saura kwana daya kacal mu yi arba'in ina toilet na din ga jin kukanta a gaggauce na fito da sauri na riski Minal kane-kane saman gado tana ta cakumarta da wannan rawar kan nata.
Tsawa na yi mata irin wadda ban ta'ba yi mata irinta ba ta kuwa zabura da sauri ta juyo tana kallona wanda ya yi daidai da shigowar Khalil na cigaba da Fadin." Ba ki jin magana ko, na ce ki bari zan baki ita ba yanzu ba tukkuna."
Ta cire hannunta da sauri daga kan towel din Khalil da sauri ya dube ni yana fad'in." Mama me ta yi mata?"
Shiru na yi ban ce masa komai saboda kwanaki ya daketa akan haka alokacin da ta taba yun'kurin aikata abinda ta yi a yanzu.
Na nufi yarinyar da sauri na dauketa aka ci sa'a kuwa ta yi shiru tana lumshe idonta baccin za ta koma.
Ita kuma ta sauka daga gadon tana ra'be-ra'be tana kallon Yayan nasu na kalleshi ina fad'in kada ka daket....ban kai ga rufe bakina ba ya kwada mata wani mari ta kwallara kara a ki'dime ta yo wajena.
Na rufe shi da fada sosai.
Ya fara fadin." Mama yarinyar nan sai ana dukanta fa wallahi rawar kanta ya yi yawa haka ta ga 'yan uwanta na yi tuntuni ake fad'in magana d'aya amma ta'ki ji ta zo ta cakumeta alhalin ba ta da lafiya."
Na sassauta sosai ina fadin." To na ji amma dukan da ka yi mata ya yi yawa kada ka sake ka ji ko?"
Ya gyad'a kansa yana sauke numfashi ita kuma dadi take yi." Mama ki yi hakuri." Na ce na ha'kura ai amma kada ki sake."
Ta daga mini kanta tana jan hanci.
Da gaske ta sangarce shekara tara fa yanzu ya kamata ace ta rage lalata shi kuma yanzu jin sa yake yi babba a cikinsu duk wadda ta yi shirme zare idonsa yake yi bai dai ta'ba dukan su Hassana ba sai dai muzurai da tsawa idan ya ga sun yi abinda bai da ce ba.
Ya nuna mata hanyar fita da hannu ta gane abinda yake nufi aikuwa sumi sumi ta fita.
Na ce Kai ba ka jin tsoro ta gayawa babanku kasan 'yar gaban goshi ce.
Ya d'an yi murmushi yana fad'in ai Mufida ta ture mata fada yanzu itace akan karagar mulki."
Takaitaciyyar dariya kawai na yi na cigaba da jijjiga yarinyar a hannuna.
kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Ya zauna kusa da ni a nutse zamansa ya sanya ni nazarinsa sosai yana da damuwa tuntuni na fahimta kawai shiru na yi.
Ya ce." Mama ko zan iya sanin abinda ya shiga tsakin Mamanmu da Baba don Allah ki gaya mini da na tambayi Hajja ta ce mini babu sauran zama a tsakaninsu ma'ana babu damar da za a gyara ta dawo, ki yi hakuri don Allah ki sanar da ni rufe mini bashi da amfani mahaifiyata ce na yarda amma k'wakwalwata ba zata manta da abubuwan da suka dinga faruwa ba tun da k'ananun shekaruna na gane dabi'unta ba su da kyau na yi iyakacin bakin kokarina wajan ganin ta gyara an zauna lafiya amma hakan bai samu ba.
Jikina ne ya mutu da jin abinda yaron ya zo mini da shi.
Yaro karami da tunanin manya idan yana manyance abin har mamaki yake ba ni wallahi sai na yi saurin yin kasa da kaina
To na ce masa me in banda abin Khalil Hajja ta sakaye masa saboda abu ne mai muni a ce ya ji abinda uwarsa ta aikata.
Amsar ai tana wajan Babansu tunda shi ya aikata ba ni da abinda zan ce.
Ya gaji da magiyarsa ya tashi ya tafi domin abinda nake nanata masa shine ni ma ban san komai ba.
BAYAN WATA UKU
Bauci
"To tunda kina ganin akwai yiwuwar haka sai ki jarraba ki gani ni dai ba ni da wata dama yanzu Hauwa gabad'aya ma cikin nadama nake a halin yanzu dalili ban san da wace fuska zan kalli yar uwata ba abinda ki ka aikata bai yi mini dadi ba ko kad'an gashi saboda ke sakarai ce kin dawo gida hannu rabbana in banda wannan kudin da ya baki wattanin baya ina takardar kamfanin da kike ta masifa akan ba kya so kun rabu rabuwa ta har abada babu kome kamfani kuma yana hannunsa har yanzu tunda dai bai baki shedar mallaka ba kin yi a banza sakarai shashasha duk shawarwarin da k'awaye da abokan arziki suke ba ki kin watsar kowa ya gaya miki ta wannan hanyar ake ya'kin kwatar 'yanci a gidan miji shikkenan ai sai mu zauna ni dake ai mu tsotsi tsamiya kin raba da ni da 'yar uwata
Hauwa gashi abinda duk muke han'koro bamu samu ba idan kun yi auran kisan wuta kin biya wanda za ku kulla yarjejeniyar shin kina da tabbacin zai sake ki, ki koma gidan Tajo.
Shi din ai ba mahaukaciya ce ta haife shi ba, ta wace hanyar za mu bi koda hakan ta kasance muga bu'katarmu ta biya?" Inna Uwani ta kai k'arshen maganarta cike da damuwa mai tsananin gaske.
Ta nisa yayin da take ko'karin korar damuwa da wasi-wasin zuciyarta ta ce ." Zai yiwu Inna don mun gama magana da Yaya Naziru mijin Sadiya na ce zan bashi miliyan uku idan mun yi aure wata biyu zuwa uku sai mu rabu.
Maganar komawa dakina ai mai sau'ki ne in sha Allahu zan koma kuma zan yi kokarin ganin na gyara na zauna lafiya da ita da shi don yanzu gabad'aya hankalina na gidan da yarana shikkenan Amina ta zama ita kad'ai yaran ma sun zama nata saboda na riga nasan na yi sallama da yarana Inna kamar fa ba ni na haifesu ba."
Sai hawaye shaaaa! suka fara kasa tsare a kumatunta.
Ta takure jikinta sosai ta jingina bayanta jikin wata tsohuwar kujera dake falon nasu tana kuka mai tsuma zuciya.
Ta ce." Hauwa ba ki da kunya da ta ido yanzu Nazirun za ki aura da wane idon za ki dubi Sadiya duk abinda za ki yi fa ki yi tunani akai shima Nazirun kwad'ayin me yake yi ne, ki je ki nemi wani a waje wanda babu dangantaka mana.
Ta dago kanta tana kallonta kafin ta ce." Shine kawai nake ganin zai cika alkawari Inna tunda ai rashin ba shi goyon baya ne a wancan lokacin ya sanya ya nemi auran Sadiya Inna kada ki manta fa tsohon saurayina ne.
Kuma ya gaya mini kudin nan da zan bashi zai dora akan kasuwancinsa da ya yi rauni tunda zahiri yanzu Sadiya ta fi shi samu tana aiki tana kuma business ni kaina na sha yin order a wajanta.