← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 264 OF 276

Sashe 264

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shiga mamaki kwarai shima jikinsa ya yi sanyi mussaman yadda ya ga hankalina ya tashi ina kuma sake jaddada masa cewa shari'a ce zata raba tsakanina da ita idan kuma bai yadda da hakan ba ya zama dole ya za'bi zama da ni ko'ita domin ba za a cigaba da tafiya a haka da ni ba ya zame mini dole na nemi mafita.

Kwanan rarrashi ya yi duk da girkinta ne sai ya kashe wayarsa ma gabad'aya domin kada ta kira shi ya rufe dakin da key ya boye shi saboda kada na fita rarrashina ya dinga yi sosai lamarin na sa'barsa shi kansa yanzu yadda yake nunawa lamarin Hauwa ya kai shi ma'kura akwai dalilan da ya sanya yake daga mata kafa wanda ni ma su nake duba mussaman yaranta Khalil dai biyayyar da yake yi mini kwatankwancinta ba ta samu ba ga Minal da take jarabar kulafucina uwa uba kuma ina duba Hajja domin duk lalacewarta tata ce idan na yi tutsu abubuwa da yawa marasa dad'i za su faru wanda za su sanya kunci da zubar hawaye a idanuwan yaran.

Wallahi kwana cur ba mu rintsa ba har sai da ya karya mini lagona da rarrashi da kalamai tare kuma da al'kawaruruka da tabbaci akan idan ta sake aikata abu makamamcin wannan da kansa zai d'auki mataki.

Sai da ya yi mata ya ji na sati d'aya bai je gidanta ba ta kuwa zama kamar mahaukaciya ta zo gidana ya fi sau hud'u ba ni ma sanin zuwanta sai dai idan na fito daga d'aki yara ko masu aiki su ce mini ta zo.

Shi kuma ba ta ma riskarsa domin yakan fita da wuri kuma baya dawowa sai dare.

A ranar da ya cika sati guda ya koma gidan wanda na tabbatar da cewa wannan ba shine iyakacin horon ba akwai wasu mabambamta yadda ya yi wannan fushin kuma sai ta gayawa aya za'kinta.

Hakan da ya yi sai ya kara sassauta mini rai amma dai duk haka cikin k'unci da takaicin abin nake don sai da na sanya aka yi mini saukar al'kur'ani can makarantar allonmu dake cikin unguwar mu duka cikinta muka yi sauka al'kur'ani mai girma a duk lokacin da masifa ta tunkaro ni nakan sanya an yi mini sauka da addu'a sannan a yi sadaka Hamusu ne ya jagoranci al'amarin sati guda aka d'auka ana sauke izifi sittin a lokacin na fara jin sanyi a zuciyata.

Maigidan ya kuma zo mini da albishirin kammaluwar ginin shagunana har ya nuna mini bidiyon wurin a waya waje ne mai darajar gaske a cikin kasuwar ta wuse market gini ingantacce na zamani mai tafe da 'kawa kamar yadda ya fadi madaidaiciyar plaza ce mai d'auke da shaguna sha biyu masu matsakacin girma kasa da sama ko'ina gwananin sha'awa ga Ac ta kowace kusurwa da manyan panal na solar haske ko ta ina yanzu shawarar yadda za a yi tana hannuna sai abinda na ce haka yake gaya mini yana lankwasar da kai da murya duk a k'okarinsa na ganin ya kashe guguwar wuta mai tartsatsi da take shirin kamawa a gidansa.

Ni kuwa na ce da shi yadda ya bada umarni haka za a yi amma dai ina so na yi amfani da 'bari d'aya sama da k'asa d'aya side d'in a bada shi haya ya ce hakan ya yi.

Bayan kwana biyu ya shigo har d'akina ya same ni ban jima da fitowa daga wanka ba ya dinga bina da kallo har sai da na tsargu na dube shi ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Ciki ki ka samu ne?" Na ji wani bala'in fad'uwar gaba domin kuwa akan ga'ba nake ina sanya ran ganin al'adata cikin kwanaki biyun nan.

Sai na girgiza kaina ina fad'in." A a mai ka gani?" Ya d'ora hannunsa saman kirjina da suke da towonsu har yanzu ba su langa'be ba ya ce na ga sun girma sosai kin d'an yi kumburi Giwa ina fahimta a duk lokacin da ki d'auki ciki kina canzawa fa har yatsunki.

A sanyaye na ce." To wallahi ba zan tabbatar ba amma don Allah ka daina kira mini shi yanzu ka taimaka mini na rantse da Allah na wuce haihuwa Allah Ya raya mana wanda muka samu."
Ya zuba mini ido fuskarsa ta canza da wani yanayi ya furta." Ni ba za ki taimaka mini ba kenan.

Na jima ina gaya miki ina son samun uwata Halimatussadiya sai ki ce na tausaya mini indai ni ban wuce haihuwa ba Hajiya kema ba ki wuce ta ba, mu riko Allah Ya ba mu mai albarka na ce ko daga haka sai na godewa Allah."
A sanyaye na ce." Ai shikkenan." Ya rike hannuna yana dan murzawa ya furta." Ki ce Amin kin ji ko Allah Ya sa shi din ne, domin a jikina nake ji hakan!"
Na dube shi ganin yadda ya zura mini idonsa ya sanya na ce ." Amin Allah Ya sa shine."
Ya kuwa sauke ajiyar zuciya yana fad'in." Na gode miki sosai Allah Ya yi albarka."
Na amsa da Amin a takaice kafin ya sake kallona a karon da babu adadi.

"A game da abinda muka sanya a gaba ni dake a yanzu nake so na ji a ina aka kwana ina so mu wuce wannan wurin ne zan je Legos ina da uzuri a can din amma ni kad'ai nake son tafiya."
Na ce." Business din da nake yi cikin garin kano na zannuwa takalma da huluna nake so na kawo shi nan din kamar yadda na gaya maka da farko amma ina so shaguna biyu na zuba supplements ina so na jarraba ana samun alheri."
Ya d'an yi jim kafin ya ce."Supplements kayan gyaran jiki na mata da kwalliya ko?"
Na gyad'a kaina idona a kansa ya ce ." Hakan ya yi Allah Ya ba ki sa'a, amma ba ki sha'awar sayar da kayan maza ina nufin irin wanda muke sanyawa tunda harkar huluna ta kar'be ki sai ki sa hannu anan din domin mu ga abinda Allah zai yi."
Na ce." Hakan kuwa ya yi sosai na gode da shawara Allah Ya saka da alheri zan yi ko nan gaba don ba ni tsammanin abinda yake hannuna a yanzu zai ishe ni yin duk abinda nake buk'ata.

Ya ce." Ni zan yi miki order domin shirya shagunan tunda na bada shawarar yin hakan amma har yanzu ba ki fitar da sunan shops din na'ki ba.

Ita kanta plazar akwai buk'atar a samar mata da suna na mussaman ko?"
Nan fa d'aya wallahi na manta shaf kuma dai da kunya na ce masa sauran shagunana suna d'auke da AminatuAminu collocation ne.

Tun lokacin da na fara bud'e shagon d'inki na sanya masa A-A fashion designer hakan na nufin AminatuAminu sai Kuma da na bud'e shaguna tukkuna na bud'a sunan kowa ya gane abinda nake nufi kuma har zuwa yanzu wannan tambarin ne a jikin duka shops dina sai dai a sabunta idan ana so a sake 'kawata lamarin.

Ina so a ko'ina ya cigaba da tafiya a haka domin cirewa customer's d'inmu shakku da kokwanto.......

Masu karatu ku ba mu sunan da ya kamata a kira shop's din Amina na Abuja don Allah kada a yi rashin adalci.......

Plazar dai na yi mata suna da (GIWA PLAZA) shin ta cigaba da amfani da AminatuAminu tunda da shi a kasanta.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP #700 VIA 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*173*
Har yanzu idanuwansa na tsaye a kaina jikina ya k'ara yin sanyi kasala ta mamayeni bakina ya mini nauyin da na kasa ce masa ga yadda nake so komai ya tafi daidai da abinda na gina shekara da shekaru ai da kunya da nauyi duk da yanzu babu shi a raye a duniya amma mafiakasari mazan mu na yanzu ba sa rasa abin kishi koda ga wanda ya mutu ne mussaman da na riga na fi kowa sanin halinsa mutum ne shi mai zazzafan kishin tsiya.

Kawai sai na tsinkayi maganarsa yana fad'in." Za mu cigaba da kiran shops din da AminatuAminu ne ranki ya dad'e?" Ya fad'a yana dago fuskata da tafin hannunsa.

Na dube shi cikin wani irin yanayi ya aka yi ya san abinda yake d'auke kenan a jikin banner da logon shugunana tunda ban ta'ba daukarsa na kai shi ba kuma ban ta'ba nuna masa bidiyon abinda ya danganci harkokina ba.

Ya d'an yi murmushi yana fad'in." An gaya miki shashashan namiji kike aure Amina.

Bari ki ji abinda ba ki sani ba tunda na aure ki idona akan harkokinki yake da cigaba da fad'uwa duk ina samun labari mussaman na samu lokaci Hamusu ya jagorance ni ya nuna mini shagunanki a cikin kasuwar kwari yana kuma gaya mini irin yadda nauyi da hidima suka yi yawa akan ki akwai abin mamaki ne a anan don miji ya bibiyi sha'anin matarsa.

Tunda kina shakkar ki nuna mini ciki da wajenki ni na bibiya domin samun nutsuwa kuma na yi miki murna da farinciki kin zama mace mai kamar maza a cikin maza kashi dari kin take hamsin sauran sakarkarun su d'auki hamsin domin jajurcewarki akan neman halak ba kowane namiji ne zai iya abinda ki ke yi ba a yanzu kuma ina yi miki fatan alheri tare da addu'ar Allah Ya sa ki fi haka."
Tun da ya fara maganar kaina yake a sunkuye d'agowar da zan yi sai ta yi daidai da zubowar hawayen da ya taru a cikin kwarmin idona suka fara sauka saman kumatuna bakina ya dinga rawa magana nake so na yi amma gabad'aya ya gama d'aure ni da jijiyar jikina na rasa shin godiya zan yi masa ko kuma rungume shi zan yi."
Ya d'an 'bata fuska yana fad'in." Kina ba ni mamaki wasu lukutan Amina shin ni din kuwa ina da abinda zan biya ki bisa abubuwan da na samu ta dalilinki.

Kada ki manta da cewa babu wani arziki madaukaki anan duniya mai sanya farinciki da annashuwa face na haihuwa tabbas Allah ne yake bada ita bayan na yi godiya a wajensa wajibi ne kema na yi miki bisa samun sanyi idaniya da kuka ba ni.
Chapter 264 · 0% Book details