Sashe 251
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muka kwana a zaune da jiran saurare sai gefin asubahi tukkuna wani likita ya fito ya ba mu tabbacin cewa sun shawo kan matsalar da ikon Allah yanzu haka har an daura mata jini jini tana da buk'atarsa.
A lokacin ne hankalinmu ya kwanta ya ce Sukairaju ya mayar da ni gida saboda yara ni ma hankalina yana kansu amma duk da haka sai nake ganin kamar ina matsawa za a ce mini babu ita.
Babu wanda na gayawa halin da ake ciki har yaran gabad'aya.
Sai Baba Tabawa itace ta sani tunda a hannunta na bar su hassan.
Har yaran suka tafi skull ba ni da kuzari na kira shi ya fi sau biyar a safiyar yana gaya mini ta ji sau'ki bacci ma take yi shima gashinan zai dawo domin ya yi wanka.
Da 'kyar na iya yin karin kummalo na zauna a d'akina sukuku don yaran ma dana lura za su dame ni da koke-koke na ce da Mairo ta zo ta d'auke su.
Na zauna ina ta tunanin rayuwa yadda Allah ya jirkitar da hallitar Hauwa jiya kadai shine abinda ya tsaya mini a raina.
Muna ta hauka rai da rayuwa da jin dad'i duka ba a hannunmu yake ba.
Hawaye suka ziraro mini kaina ya d'auki caji da tunani da zullumi tare da nadama da addu'ar kada Allah Ya d'auki rayuwarta a yanzu ina so mu yi nisan kwana tare mu raini yaranmu.
Wajan tara da arba'in ya shigo.
Ganinsa cikin nutsuwa ya sanya ni sauke ajiyar zuciya ba mu yi wata magana cikakkiya ba har sai da ya yi wanka da breakfast tukkuna na fara tambayarsa jikin nata ya ce.''Ta ji sau'ki alhamdulillahi jininta ya hau sosai sanadin damuwar da ta tsanantawa kanta ba ta bacci ga ciwon kai mai tsanani abinda ya fita Allah ya yi ba rayayye ba ne na gaya mata tun ranar da lamarin ya faru tana ta kuka da tsananta damuwa idan da rabo ai za a samu
wani."
Na ce." Sosai kuwa in sha Allahu za a samu damuwar ai bata da amfani tunda itace ta haddasa mata shiga wannan yanayin.
Ya ce." Abinda nake so ta gane kenan, za mu cigaba da ro'kon Allah Ya kawo mana masu albarka."
Na ce." In sha Allahu rabbi."
A takaice dai sai da ta yi kwana bakwai a kwance a asibiti tukkuna ta warware sosai kullum sai na je na dubata ban taba d'auke rana d'aya ba.
Inna Uwani ta zo kwana biyu da suka wuce babu yabo babu fallasa tsakanina da ita Muna gaisawa sai dai babu wani sakin jiki da juna.
Yara ma sun je sun dubata sau d'aya masu aikina ma haka.
ranar da suka bata sallama da wuri na je ban kuma jima ba na dawo gida.
Sai dai ganinsa tsaye a bakin gate din gidan Hajiya Maryam shi da wasu 'kwarori guda biyu da jami'an tsaro abin ya ba ni mamaki da d'an tsaro duk da yana da masu tsaro a kewaye da shi da gidajensa amma ganin shi da wad'annan da kuma 'kwarorin sai abin ya ba ni tsoro yanayin da suke ciki ya nuna kamar akwai matsala.
Na hangi fitowar Nusaiba da Adam daga cikin gidan fuskokinsu dai babu nisha'di.
Sukairaju ya shige da motar ciki bayan an bud'e gate din hankalina ya kasa kwanciya ko da na shiga ciki gidan kai tsaye d'akina na zarce ban bari sun san na dawo ba.
Allah dai yasa lafiya.
Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biyani hakkina ba
Minti goma sha biyar a tsakani ya shigo ya biyo ni har cikin d'akina yana ta fad'a.
Ashe wad'an-nan k'warorin abokanan business din Nabila ne mazauna jahar lafia sun kashe wani d'an uwansu suka gudu ita kuma tsautsayi da azal ya sanya da suka kira ta a waya suka ce sun shigo Abuja za su zo su yi magana akan wata harka ta alheri ta gayyace su zuwa gida a jiya da daddare a yadda take fad'a cewa ba ta ta'ba tunanin za su kwana ba balle har ta ba su mafaka domin da suka gama tattaunawa ta yi ta yi da su su tafi suka 'ki suka wayi gari a zaune.
A jiyan da daddare akwai wanda jama'an tsoro suka sanya domin yi musu bincike da yake Ubangiji Allah baya bacci kuma cikin gaggawa yake tona asirin hakkin rai mutumin ya gaya musu ga inda mutanan suka fake nan.
Abinda ya tsananta domin har itama Nabilan na cikin tasku saboda bincike dole ya bi ta kanta tunda sun ce har da ita da kuma sanya hannunta alhalin k'arya suke yi.
Tana cikin gidan taki fitowa sai da ta ji duka tukkuna yanzu sun tasa keyarsu gabad'aya can garin nasarawa lafi'a.
Allah Ya tsare mana imaninmu.
Da ya gama gaya mini ya shige toilet domin yin wanka ya barni da tu'ajibi da mamaki wai 'ya mace ta'ki kama kanta saboda masifar son abin duniya.
Ba a hana mace yin kasuwanci ba amma a yi mai tsafta da aji da kuma ilimi.
Gashi dai sun dilmiyata cikin case dinsu bayan su kansu sun san bata da hannu a ciki.
Wannan shine
abinda ya yi rayuwar Hadiza illa kenan.
Ya fito daga toilet din yana cigaba da fad'a tare da jaddada mini cewa ba zai ta'ba sanya hannunsa a cas din ba tunda ba shi ya aiketa ba hanya yake nema dama tunda rayuwar da ta d'aukarwar kanta kenan shikkenan babu ruwansa abinda dama ya sanya shi barin ta a gidan a zaune saboda yaran sun buk'aci hakan ne shikkenan gida za a rufe idan Salim ya tashi aure yana da ra'ayin gyara wani bangare daga ciki sai ya zauna da iyalinsa tunda sun ce ba sa so a sayar kuma ba sa so zuba y'an haya.
Adamu zai ba shi za'bi zaman kano gidan Hajiya Ayya wurin kakarsa ko kuma zama anan wurinmu duk wanda ya zab'a daidai ne.
Ko da ya tambaye shi kuwa yaro ya ce kano gidan Hajiya Ayya ko gidan Hajja.
Ya ce gidan Hajja ya fad'i hakane saboda Yusi ya ce zai yi waya da kakar tasu domin sanar mata da halin da ake ciki.
Lamarin nan na jima yana ba ni mamaki da tsoro duniya ta lalace yanzu mutum akan abinsa dukiyarsa sai a halaka shi tunda bincike ya tabbatar da cewa akan kudinsa ne suka kashe shi gashi dai tare suke su uku kuma kowa ya sansu a tare amma an wayi gari sun kashe shi.
Abin tausayi da jimantawa ita Nabilan da Allah ne kadai zai fitar da ita.
Shiyasa ko abota za ka yi kasan da irin wad'anda za ka yi.
Saurin yarda da sakin jiki ga mutumin da baka sani ba sai ya janyowa rayuwarka barazana.
Allah ya k'ubtar da ita tunda babu gata ta ko'ina ba uwa babu uba, yan kudin nata da take nema ba su isa su fitar da ita daga wannan masifa ba ga yaranta biyu duk maza sun zama yan samari wata'kila ganin sakarcin da take yi ne ya sanya ubansu kar'be su suna can jos din tunda a can ne ta yi auran kafin ta fito.
Yau kwanaki biyar kenan da fitowar Hauwa daga asibiti Hajja ta zo dubata a gidana ta sauka sai da ci abinci tukkuna ta huta sannan muka nufi gidan tare tunda ni ma tun bayan an sallamota daga asibitin ban sake duba ta ba.Kafin mu isa gidan Hajja na jaddada mini jikin Gwaggo babu dad'i kwanakin nan itama tana fama domin ta kwanta a asibiti na kwana uku kafin a sallamota ban ji dad'i ba kuwa ba a gaya mini ba Hamusu bai sanar da ni ba haka zalika ma Yusi.
Raina ya baci sosai amma ban nuna mata ba tunda babu halin kalubalantarta.
Duk da saura kwanaki mu shiga ramadan hakan ba zai hana ni shirin zuwa dubata ba jikinta ba ta d'an jima a tsaitsaye tana ciwo ashe har da kwanciya a asibiti gashi masu aiki na shirin tafiya umara kamar yadda maigidan ya yi musu alkawari a farkon farkon watan azimi.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*166*
Sosai na yi dana sanin bin Hajja zuwa gidan Hauwa da ina da masaniyar abin da zai faru.
Wannan shine dalilin da ya sa da yawa wasu daga cikin mutane ba su son yin auran zumunci a tsakanin yaransu koda kuwa akwai soyayya mai karfi a tsakanin yaran akan samu suka da kalubale daga wurin dangi kowa na fad'in albarkacin bakinsa akan zumuntar da za a had'a ta aure wadda ake da burin ta d'ore ta ginu ta kuma kara karfin zumunci tare da albarkar haihuwar yara.
Mafiakasari shi auran zumuncin bai fiye yin armashi ba wani tun daga farkon k'ulla shi ake fara cin karo da rigingimu mabambamta wanda ka iya janyo rabuwar kai da tashin hankali tare da zama a teburin sulhu idan ma ba akai zuciya nesa ba har hukuma kan iya shiga domin kawo sasasanci dalili daga kowane bangare yana ganin ba a yi masa daidai ba.
Wannan tashin hankalin ya sanya da yawa iyaye suka gwammace su aurawa na waje yaransu domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali duk da cewa rikicin aure da matsaltsalunsa abu ne da ya zama ruwan dare ko da babu dangantaka a tsakani a duniya a ka hadu har aka kulla auratayya matsala na faruwa iri-iri tunda dama kafatanin auran ha'kuri ne jin dad'insa kad'an ne.
Amma dai da sauki akan ace abu biyu ne suka hadu waje daya dangantaka ta jini zumunta mai karfi kuma da dangantaka ta aure sai abin ya zama wani iri iyaye su shiga idan an kai magaryar tu'kewa lamarin ya yi tsamari a tsakanin jini d'aya a
samu rabuwar kai da zargin juna daga kowane b'angare duk domin kiwatar kai bisa zargin zalintar juna.