← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 276

Sashe 165

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce da Sukairaju ya yi sallama a kofar gidan Malam din haka kuwa ya yi ya dinga kwad'a sallama wani magidanci ya fito cikin yar shara da fatanya a kafadarsa.

Suka yi musabaha kafin ya tambaye shi.

Ya ba shi amsa da eh gidan Malam 'Daha ne.

Sai ya nuna masa motar yana fad'in." A gaya masa ba'ko ya yi Alhaji Tajuden ne na Alhaji Ibrahimu dambatta wato abokinsa da ya rasu."
Mutumin ya washe bakinsa kafin ya nufi wurin motar da saurin gaske.

Sukairaju ya bi shi cikin gaggawa ya yi saurin tare shi.

Duk abinda suke yi yana kallonsu sai ya sauke gilashin motar fuskarsa a sake ya furta." Sukairaju matsa masa hanya mana mutumina ne."
Da sauri Sukairaju ya bashi wuri shi kuma ya k
rasa bakin motar yana ta dariya tare da mamakin ganinsa.

Ya bude motar cikin sauri ya fito ya rike hannunsa yana fad'in." Malam Rabi'u."
Ya ce." Naam Alhajin Allah dama za mu sake ganawa."
Yana dariya ya ce." Allah ya nufa gashi na ziyarce ku, na zo wurin Malam ne."
Ya gyad'a kansa yana fad'in" Ya bayan rabuwa Alhaji ya harkoki da jama'a Ubangiji Allah Ya taimaka ya kara suttura."
Ya amsa da "Amin Malam Rabi'u ya iyali fatan kowa lafiya?" Ya ce." Alhamdulillahi mata na hud'u ina da yara ashirin da biyu."
Cike da mamaki ya ce." Mata hud'u yara ashirin da hud'u Rabi'u?"
Sai ya kyalkyale da dariya yana fad'in." Kwarai kuwa Alhaji yanzu haka akwai shida mata dana aurar da su, suna d'akin mazajensu cikin aminci."
Ya gyad'a kansa yana jimanta karfin hali irin na mutanan k'auye gashi dai bashi da wani karfi irin na su amma ya ajiye mata hud'u da tarin yara."
Ya ce." Ka burge ni da gaske Rabi'u kuma kai namiji ne, yanzu dai ka yi mini jagora wurin Malam na zo mu gaisa ne."
Ya ce." Ka kyauta sosai kuwa domin idan ban mata ba yanzu ka kai sama da shekara asirin rabonka da garin nan tun marigayi yana raye."
Ya furta." Tabbas hakane domin karshen zuwan da muke yi tare da shi ne, tun bayan rasuwarsa kuma Allah bai nufe ni da sake zuwa ba."
Suka nufi cikin gidan a tare suna magana cike da jin dad'in had'uwa.

Babu girman kai ko kuma nuna ni isheshshene yanayin yadda ya gaisawa da jama'ar da suka tsaitsaya yana ta d'aga musu hannu haka suka shiga gidan da aka narka 'kasa irin ta da mai d'anko wurin gida shi.

Gidan mai yalwa ne sosai irin dai ire iren gidajen Malaman addini mussaman na karkara
har yanzu yana nan inda yake sai dai kwaskwarima da aka yi wa wasu guraran dalilin wasu daga cikin yaransa a ciki suke zaune da iyalinsu.

Amma kuma sun gyarawa mahaifinnasu bangaran nasa tunda da alama yana yin manyan ba'ki mussaman abokai ko 'ya'yansu tunda fitacce malamin addinin musulunci ne da har yanzu tafsiri da karatun al'kurninsa ke yawo a wasu gidajen redion.

Koda suka shiga wurin nasa yana zaune kafarsa ta k'wanshe da al'kur'ani kirar warshu a hannunsa yana karatu babu wata gigita ta tsufa ya gane wanene a gabansa.

Rabi'u yana fad'in." Malam ga Tajuden na Alhaji Ibrahimu na kawo maka."
Ya yi dariya irin ta manya kafin ya ce." kuna shigowa na gane shi ai ko baTajudden na Alhaji Ibrahimu ba."
Ya ce." Ni ne Malam ina fatan na same ku lafiya ya bayan rabuwa kuma?" Ya amsa da "Alhamdulillahi ya iyali ya jama'a ya harkokin ina Hajiya Halimatu?" Yana nufin Hajja kenan.

Ya ce." Tana nan lafiya lau ta ce a gaishe ka da kyau Malam."
Ya gyad'a kansa tare da fad'in." Ina amsawa na kuma ji dadin ganinka Tajuden za mu sake saduwa kafin Allah Ya yi ikonsa."
Ya furta." In sha Allahu rabbi zan dinga ko'karin ganin na kawo ziyara Malam abubuwa sai a hankali."
Ya gyad'a kansa yana murmushi kafin ya ce."Allah Ya taimaka ya bada sa'a, na gode sosai Allah Ya yi albarka."
Ya amsa da Amin suma Amin kafin wajan ya d'auki shiru Malam Rabi'u tuntuni ya fita.

Malam din ya ce." Akwai abinda yake tafe da kai ne?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kwarai kuwa Malam muna buk'atar addu'a akan komai duk da muna yi akan kanmu, amma a kwanakin nan abubuwa sun yi yawa mussaman 'bangaran iyalina a taimaka mana da addu'a Allah Ya warware mana."
A nutse ya ce." Za a yi in sha Allahu akwai buk'atar ka tsananta addu'a akan kanka, daga nan zan sanya al'majirai yin saukar al'kur'ani tsayin kwanaki bakwai sai ka yi sadaka, Allah Ya warware."
Ya amsa da "Amin Ya Malam na gode sosai Allah Ya kara girma."
Ya furta." Za ka shiga ka gaisa da mutanan gidan ko?"
idan kin san kina karanta book din nan ba ki biya ni hakkina ba to Ina binki bashi.

Ya yun'kura domin tashi Yana fad'in." E, zan shiga Malam zan yi magana da Rabi'u akan abin sadaka sai mu ga yadda za a yi."
Har ya juya zai fita ya dakatar da shi ya tsaya sai ya ce." Ya iyalin Tajuden su nawa ne yanzu yaranka kuma nawa?"
Ya ce." Allah shi gafarta Malam su uku ne yara kuma ina da biyar rayayyu d'aya ta rasu."
Ya ce." Alhamdulillahi Alhamdulillahi Ubangiji Allah Ya yi musu albarka, Allah Ya raya mana su bisa tafarkin addinin islama.

Idan har kana da buk'atar cika sunnar Annabi tunda su uku ne ka zo nan na zaba maka daya daga cikin yarana biyu da suka rage mini.

Hakika ina sha'awar tabbatuwar zumuncina da Alhaji Ibrahimu.

Duk da fad'in Allah ne kuma sunna ce mai kyau amma ba wajibi ba ne, abinda magabatanmu suka d'ora mu akai kenan lallai k'arshen duniya mata za su yawaita yayin da mazan auran za su yi 'karanci ko rashin ikon ga masu niyya. masu iko idan kuna da d'aya ku kara da ta biyu, masu biyu ku 'kara da ta uku, masu uku ku k'ara ku yi hud'u domin dakile mas'aloli masu yawa.

Idan har ka niyyata tunda kana da iko kada ka manta ka zo nan zan had'a ka aure da nutsatstsiyar yarinya ko ba daga cikin yarana ba."
Cikin wani yanayin ya furta." To shikkenan Ya Malam idan da yiwuwar hakan in sha Allahu zan zo sai a san yadda za a yi na gode sosai, Allah Ya saka da alheri"
Ya amsa da "Amin cikin nutsuwa yana yi masa fatan alheri da sauka lafiya.

Yana fita ya ciko karo da Rabi'u a tsaye ya ce ya yi masa jagora cikin gidan domin su gaisa.

Ya dinga mamakin yadda gidan Malam 'Daha
ya cika da tawagar yara 'yan mata da masu tasowa maza da mata sai iyayen tukuwane kangama-kangama dama can sanin da ya yi masa mutum ne mai arzikin gona ki a k'auyen don haka matsala ta abinci ba zata ta zama barazana a gare su.

Malamin mahaifinsa ne kuma akwai abota sosai sai dai kowa tsarinsa daban.

Mahaifinsa ko a can baya yana da wayewa sosai ta fannin boko da kuma addinin daidai gwargwado Hajja ita kad'an ta rayu bai ma ta'ba yun'kurin karin aure ba har ya rasu su biyu ya haifa.

Shi kansa bai taba tunanin zai iya ajiye mata uku ba domin yadda ya tsara rayuwarsa tun daga kuruciya Samira kadai ta ishe shi, sai gashi Allah Ya na ta juya lamarinsa.

Har gajiya ya yi da amsa gaisuwa domin dai daga sashe sashe ake zuwa gaishe shi.

Rabi'u ya riko hannunsa suka fita duk da haka wasu daga cikin yaran sai da suka biyo bayansu.

Bakin motarsa kuwa jama'a ne a tsaye Sukairaju yana ta fama da su.

Daga bakin kofar gidan Malam din suka tsaya a dan gajiye yake fad'in." Rabi'u kana da asusun ajiyar kudi ko?"
Ya ce." E, da akwai sai ya fito da wayarsa ya mika masa yana fad'in." Bismillah yi sauri sanya mini lambar a nan zan tura abin sadaka a bawa Malam sannan abinda ya yi saura ka yi amfani dashi a kuma sallami iyayenmu da k'annanmu da suke cikin gidan a ba su su sha ruwa."
Ya kar'bi wayar da sauri yana fad'in." To Allah Ya saka da alheri mun gode Allah Ya kara arziki Alhaji."
Bai ce komai ba har gama ya mika masa waya ya kar'ba a tsaye a wurin ya tura dubu dari biyar sannan ya bashi wayar a gain ya ce ya sanya masa lambar wayarsa domin su dinga gaisawa."
Ya kar'ba a karo na biyu ya sanya masa lambar shi kuma ya yi serving da Malam Rabi'u Bunkure.

Da haka suka yi sallama cike da girmama juna.

Sai da suka fita daga karkarar tukkuna Sukairaju yake tambayarsa ina suka nufa domin shi duk a tunani shi zai sake kwana a kono din ganin bai fiye son tafiyar mota ba.

Ya ce." Mu d'auki hanyar gida kawai yau komai dare a gidana zan kwana Sukairaju na huce gajiyar gabad'aya."
Aikuwa da azama ya d'auki hanyar garin abuja kamar yadda aka bashi umarni.

Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya d'an gyara zaman shi a mota yana nazarin maganar Malam 'Daha wai ya zo cikin karkara ya nemi aure domin cika ta hud'u.

Gabad'aya ma shi yanzu babu wannan lissafin a tare da shi bai sani ba ko nan gaba.

Gabansa ya fadi lokacin da ya tuna iya rigimarsa Amina tunda suka yi sallama jiya sau daya suka yi waya da daddare kafin ya kwanta ya kira ta domin gaya mata ba zai dawo ba sai gobe.

Yana duba wayar ya ga kiranta ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya sanya wayar a kunnansa Amina ta tsaya masa ransa sosai shi kansa ya tabbatar da haka...
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*TALLAH!* https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.
Chapter 165 · 0% Book details