Sashe 125
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hauwa kawai ta tafi gidansu kafin na gama yanke hukunci ta san matsayinta, tunda har za ki iya d'aukar fillo ki toshe mini hanci don na mutu ai lamarin babban ne a wurina Hauwa ta samu nasarar tayar mini da husuma ni kuma zan d'auki matakin da ya dace a kanta."
Gwiwa a sanyaye na kashe wayar ina kallonta babu damuwa a tare da ita tace." Ai na gaya miki Amina mutumin nan kaf dabi'unsa sun canza muddin akan lamarin matarsa ne yakan iya cin mutuncin kowa."
Na ce." Babu da inda za ki je." Ta yi shiru tana kallona ina laluban wayar Hajja bugu daya ta daga.
Cikin rawar murya na gaisheta ta amsa tana fad'in duk kuna nan lafiya ko Amina."
Na ce." Lafiya lau Hajja don Allah ki yi masa magana matsala suka samu da Hauwa shine ya ce wai ta tafi gida."
cike da mamaki ta furta." Hauwa ta tafi gida akan wane dalili?"
Shiru na yi ban ce komai ba.
Cike da kulawa ta ce." Amina ki gaya mini menene yake faruwa kin ji ko kada ki rufe mini komai.''
Hawaye suka silalo mini na ce." Hajja Hauwa ba ta yi masa komai ba wallahi, asalima ma matsalar ni ta shafa saboda kawai ta gaya masa gaskiya shikkenan yake jin haushinta."
Ta ce." To gaya mini wace matsala ce, ni zan yi maganinta, Hauwa kuma ki gaya mata kada ta fito."
"In sha Allah, gata nan a kusa da ni, na hana ta fitowa."
"To hakan ya yi ina sauraranki." Tafad'a cikin nuna damuwa.
A nutse na fara gaya mata tun daga farko abinda yake faruwa har zuwa yanzu da ake wannan rikicin.
Hajja ta jima cikin alhini da takaici kafin ta ce." Ki yi hakuri a matsayinki na babba kuma uwa.
Amina tabbas ko ba ki fad'a ba nasan idan za a tona zuciyarki to tanan cikin kunci da b'acin ran wannan lamari.
Ki jure lallai kuma ya zama dole a yi wa tufkar hanci saboda gudun abinda zai afku anan gaba na rashin dadi.
Zan nemi shi zai kuma zo nan inda nake akan maganar nan domin ni kaina ban yarda da hakan ba.
Sannan duk abinda zai yi muku kada ku saurareshi.
Ki jadaddawa Hauwa cewa da yawuna ban amince ta fito ba.
Ke kuma ki yi hakuri kin ji ko, nasan abinda da ciwo a zucci amma in sha Allahu gaskiya za ta bayyana kanta.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta
Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl
Momyn Hajara GHT supplements
Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah
Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya
Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah
Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal
*87*
Muryar Masa'udu ta katse tunanin da nake yi. na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Kai mu jabi park."
Cike da bin umarni ya ce." An gama.
Motar ta yi shiru ni da yaran duka muna cike da zullumi mussaman Yusi da nake hankalce dashi yana goge hawaye a fakaice.
Ban tsawatar masa ba domin kuwa ban san mai yake ji a zuciyarsa ba, amma zahiri wannan shine iya gatan da nake ganin zan yi musu a duniya.
Ba zai yiwu a ce koyaushe rayuwarsu ta kasance cikin kyara da hantara ba.
Sun fara kaiwa munzali na girma a wannan lokacin ya kamata ace mun had'u ni dasu mun gina gobe dalili watarana za su yi aure su tara iyali suma.
Sannan zuciyata ba za ta iya cigaba da jurar ganinsu cikin kaskanci ba, arziki Allah ne yake bayarwa su fita su nema kowa ya tsaya da k'afafunsa.
Cikin ikon Allah motar dana sanya su ta yi lodi saura bai fi mutum hud'u ba.
Cike da dauriya da ko'karin kara musu kwarin gwiwa muka yi sallama na ce lallai idan sun sauka Kamalu ya kira ni tunda da waya a hannunsu.
Ban gushe daga wurin ba har sai da na tabbatar da tashin motarsu sannan na sauke ajiyar zuciya na gyara zaman nikab din da yake fuskata tunda ban fito ba sai da na sunkufe jikina ta ko'ina dalili ba na so a gane wata ala'ka da za a yi yamadidi da ni, kuma safiya ce tashar babu wadatar mutane da yawa sosai.
Kai tsaye na nufi wajan da Masa'udu ya ajiye mota.
Yana ganina ya taso daga inda yake ya bud'e mini na shiga na zauna sai a lokacin na ji wasu gagariman hawaye masu radad'i sun k'wace mini.
Wato ni kuma haka kaddarata take, ina ro'kon Allah Ya ba ni ikon cinyeta ya kuma saukakawa yaran nan rayuwa ya basu hakurin maraici.
Ina komawa gidan na samu Hauwa da Momi zaune a falo, amma babu cikakkiyar sakewa a tsakaninsu Hauwa ta yi zaman gadara da ki ce kule na ce miki cass domin kuwa fuskarta tamkar kunun tsamiyar da ya kwana a rufe.
Kusan a tare suka amsa sallamata.
Kwarai da gaske na yi kokarin danne abinda nake ji a zuciyata game da al'amuran dake faruwa.
Na nemi wuri na zauna babu yabo babu fallasa nake kallonta ina sake nazari akan al'amuranta.
Ta tsuke sosai ta yi fayau abinka da mara jiki da gasken ne bata da lafiyar domin alamu sun nuna babu wani kuzari da karsashi a tare da ita.
Ita ta fara gaishe ni a tsanake na amsa ido na a kanta ina sauraran abinda take tafe dashi ta gyara zamanta kad'an tana kallona sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali
Ta ce." Amina na shigo nan ne saboda ke domin mu tattauna abubuwan dake faruwa da yaranmu, Allah Ya ga zuciyata ban shigo cikin rayuwarku da wata niyya ta cutarwa ba, kuma ban had'a kai da Salim domin ya ci mutuncin Kamalu ba, asali ma abinda yake aikatawa ba ni da masaniya sai bayan ya aikata din nake samun labarin." Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya a karo na biyu kafin ta cigaba da cewa."
Yana da kyau a matsayinki na uwa mai hankali ki yi nazari mai kyau Amina idan hankali ya 'bata fa nutsuwa da dattako ake sanyawa domin nemansa bai kamata ace kin d'auki munanan shawarwarin da ba za su zama silar gyar........Hauwa ta katse ta cikin fusata." tana fad'in "Ai dama ban ce kin shigo gidan nan domin ni ba Maryam, ko kuma kin ji na ce miki kin shigo ne da mummunar niyya.
Kin tsargu ashe ai shi mara gaskiya dama kullum cikin zullumi Hajajju ki dube ni da kyau ki ga ni, a waye nake k'warai babu wata kinaya da za ki yi mini kafin ki san Amina da yaranta ni na santa na kuma zauna da ita.
Idan har mijinki ya gaya miki cewa da hannuna wurin matakin da Kamalu ya d'auka bai yi miki k'arya ba, ga ni a zaune ai ina jiran hukunci tunda ku kun iya take gaskiya da gangan."
Cikin rashin sukuni na ce." Hauwa menene don Allah, duk cikinmu nan babu yaro karami tunda har ta shigo domin mu tattauna magana dan samun daidaito bai kamata wasu maganganu mara dad'i su biyo baya ba kuma."
Ta ja dogon tsaki tana fadin
"Kina jin irin jirwayen da take yi mini ai, ai mu 'yan iska ne marasa 'yancin kai tunda mijinta haka ya nuna mata ba mu da mutunci da kima sannan ba mu da sirri komai muka yi a tambad'e ita nata sirri koyaushe cikin danda'be shi yake baya so kowa ya ji.
Bazan jure d'aukar cin kashi daga 'bangaranta ba wallahi tallahi."
A nutse ta ce." Ba halina ba ne raina mutum Hauwa, kuma kamar yadda ki ke hasashe hakane maigidan ya gaya mini komai ke ce ki ke ko'karin ganin lallai sai an yi 'batacciya domin kuwa abinda muke ta bunnewa dalilin gudun rikici mai muni ke ki ka gayawa mahafiyar yaron nan, kuma ki ka cire nauyi da kunya ki ka dubi tsabar idon yaron nan Kamalu ki ka gaya masa to kin fad'a kin ji dadi kuma in sha Allahu abinda ki ke fata ba zai faru ba da izinin Allah."
Hauwa ta mike tsaye tana huci ta ce." Kin yarda yaronki mahassadi ne, kuma sharri ya yi wa Kamalu ko ba ki yarda ba, ke yanzu don girman Allah ba ki ji kunya da nauyi ba
ai ita karya fure take bata 'ya'ya wallahi ni dai Hauwa Maryam ba ki isa ki siye ni da kudi da abin duniya ba.
Wannan gingimeman sharri da d'anki ya alak'anta marayan Allah dashi saboda rashin adalci da son zuciyarku sai ku ja baki ku yi shiru babu wani mataki da ku ka d'auka.
Sannan kuce ba za a yi magana ba, to ni na sayi rikicin don girman Allah ki d'auki mataki a kaina.