← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 185 OF 276

Sashe 185

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fara maganar da karamin sauti ban ji komai ba, ni kuma daman ban so na jin ba na ji yana fad'in." Babu halin hakan."
A tak'aice ya gaya mata haka duk kuwa da cewa doguwar magana ta yi masa ya sake dai kashe mata wayar a karo na biyu na ji shi can kasa yana fadin." Na d'auka mutuwa zan yi a cikin kwanakin nan ban zaci zan sake moruwa ba wallahi saboda tsabar yadda ga'bobin jikina suka mutu."
Na ce." Ni ma na tsorata gaskiya amma dai duk da haka yana da kyau likitanka ya dubaka sosai baka da lafiya."
Ya ce." Hakan za a yi in sha Allahu." Ya d'auke yana gyara zamansa na ce.'' Kasan yaran nan sun koma makaranta yau ko?''
Ya ce." K'warai kuwa mun yi magana da Masa'udu d'azu dana fita sallar la'asar zai maye gurbin Dauda direbansu na can gidan Maryam."
Na ce." Hakan ya fi."
A daran ranar ma sai da ya yi auratayya da ni, na dinga daurewa domin akwai buk'atar hutu da samun bacci a tare da ni ga jikin babu kuzari.

Sai da ya gane kuwa ya d'an saurara mini da asuba da yawo daga massalaci bai sake nema na ba.

Nima tunda na koma bacci bayan sallar asubahin ban tashi ba sai wajan sha biyu da kwata sai da na yi wanka tsaf na kintsa jikina sannan na fito yaran suna makaranta a falon na samu Mairo da Nusaiba suna hira Taburni da Baba Tabawa suna kicin suna aiki.

Cike da girmamawa duka suka yi mini barka da fitowa na nemi wuri na zauna cikina na hautsinawa yunwa da tashin zuciya bakina salam.

Ina fad'in." Yaushe ki ka zo ne?"
Da murmushi a fuskarta take fad'in." Wajan sha daya da rabi Baba ya kira ni yana sama amma bai sauko ba mun dai yi magana a waya ya ce mu jira shi."
Na ce." Allah sarki Ina yaran na gan ki ke kadai."
Ta ce." Suna makaranta anti."
Salim da Adam suka shigo cikin kaya iri daya gabad'aya yaran daga lokacin rasuwar Mamansu zuwa yanzu sun ladabtu sosai ba kamar Salim da yadda yake risina mini ke ba ni mamaki yaron da ya d'auki mummunan gaba da ni.

Itama Nusaiban har yanzu bata iya had'a Ido da ni.

Adam kuwa dama d'an d'akina ne tunda suna tare da Yusi.

Muka gaisa cikin kulawa na tashi ina fad'in." Bari ina zuwa."
saman na nufa domin sake sanar dashi zuwan yaran.

Sai na same shi shi da Sukairaju suna ta kicin-kicin bud'e wannan dirowa da aka shigo da ita kwanakin da suka shige.

Da kyar suka samu nasarar bud'eta da dabaru da kuma wasu mukkulai da na gansu a hannun Sukairaju...

Na ce." Nusaiba da 'yan uwanta sun zo wajenka."
Bai ce mini komai ba sai da Sukairaju ya fita tukkuna ya fura." E, wannan ma'ajiyar ta Mamansu zan bud'e a gabansu.

Ya d'auki wayarsa ya kira Nusaiban ya ce mata su haho saman.

Muna zaune suka shigo gabad'aya suka gaishe shi ya amsa cikin kulawa yana tambayarta yara da yanayin jikinta.

Ta nuna masa wuyan nata tana fad'in." Wurin ya warke alhamdulillahi.

Ya ce." To alhamdulillahi kamar yadda na gaya muku cewa idan na samu nutsuwa sosai zan bude wannan ma'ajiyar domin ni daku muga abinda yake ciki ma sha Allah cikin ikon Allah yanzu Sukairaju ya samu nasarar bud'eta don haka ku ba ni hankalinku gabad'aya.

Ya sanya hannu a nutse zai bud'e
na fara ko'karin tashi domin ba su waje ya ce na zauna.

Ba don raina ya so ba na zauna din
Tana da d'an zurfi amma ni da nake zaune kusa da shi na gama ganin duk abinda yake ciki.

Da saurin gaske na d'auke kaina gabana na wani irin fad'uwa.

Daga b'angaransa ban hangi wani razani ba da hannunsa ma ya shiga fito da abubuwan da suke ciki.

Farko dalar amurka ce ta fi bandur ashirin ya gama fito da su sannan ya kwaso tarin akwatinan gold's dinta kusan set biyar manya ba k'ananu ba bayan zobuna na tsayun hannu dake cikin akwatinansu.

Ya debo wasu takardu ya mi'kawa Salim yana fad'in " Duba nan ka ga menene.

Ya kar'ba da sauri ya fara dubawa.

Abubuwa biyu da suka yi saura cikin dirowar ya d'auko
Mutumin-mutumi ne mai d'auke da suffarsa da suffarta tsirara kammaninsa sak haka zalika itama kammaninta sak an had'e su waje daya an matse sosai da farin likkafani da jan zare aka nannad'e sannan 'kasa da sama duk an kulle da ko'ina da kwa'do. (Key)
Sai wata kwalba doguwa mai kama da ta lemo cike da turare mai maiko da k'ananun layu a ciki kimanin takwas kowacce soke da allura.

Ya dubi Nusaiba da ta gama kidimewa ganin abinda ya biyo bayan dukiyarsu da Mamansu ta boye musu ya nuna mata yana fad'in." Wannan shine abinda ya rage cikin wannan dirowa Nusaiba."
Sai ta rushe da kuka tana 'kunshe bakinta da hannu hawaye suka fara kasa tsere a kumatunta.

Adam kuwa sunkuyar da kansa kasa ya yi yana cike da damuwa mai yawa.

Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un kawai take fad'in tana kuka.

Shi kuma Salim sakato kawai ya yi da takardu a hannu ya tsirawa abubuwan ido yana kallo cikin jin nauyi da kunya.

Ganin yadda duk suka ki'dime ya sanya ya fara rarrashinsu yana fad'in su nutsu Nusaiba dai fadi take yi don Allah Baba ka rufa mana asiri ka ce ka yafe mata ko zata samu rahama.

Anti Amina kuma don Allah ku yafe mata ban sani ba ko ta yi muku wani abin na cutarwa ni dai wallahi ban san Momi tana bin wannan hanyar ba domin kullum idan mun zauna da ita cikin yi mana fad'a da nasiha take bantaba sanin abinda take yi ba."
Ya ce." Babu komai ku nutsu kowane dan Adam yana tare da jarrabawarsa a duniya mai kyau ko mara kyau ni daku duka ba mu san abinda yake lullube ba domin alherinta muka sani shi kuma muka dinga fad'a bayan mutuwarta.

Ba ni da masaniyar cewa ta tuba kafin Allah Ya d'auki rayuwarta tunda zuciyarta a kirjinta take kuma ba a bud'e mini na gani ba.

Na yafe mata Ina kuma roka mata sasaauci daga mahallicinta.

Wannan abin da kuka ga ni zai zama sirri in sha Allahu, abinda nake so daku gabad'aya shine ku samu nutsuwa kada cikinku wani ya sanya damuwa a ransa.

Ina nan har yanzu a madadin mahaifinku kamar yadda ya ba ni amanarku in sha Allah......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Paid book ne 2k complete on telegram WhatsApp Gruop 1k 0542382124....

Binta Umar gtbank*
*07084653262*
Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Mu kiyaye mu kula da hakkin junanmu.

Kukan da Nusaiba take yi shi ya fara ta'ba mini zuciya na ji hawaye ya cika kwarmin mini idona.

A hankali na janye idona daga kanta gabana na fad'uwa cikin raina ina ta kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Yadda yaran nan suka ki'dime ganin abinda Mamansu ta mutu ta bari na sa'bawa Allah shine ya tabbatar mini da cewa duk zargin da ake yi mata na cewa mushirikiya ce ba su gazgata ba sai yanzu da mutuwa ta yi mata tonan silili.

Babu kama ko d'aya a zahirance da kuma mu'amularta domin ni kaina ban ta'ba gazgata maganar dake yawo a kanta ba saboda ban ga ni da idona ba a wasu lukutan dai idan abin ya yi tsanani nakan ji a raina anya babu k'amshin gaskiya akan abinda ake fadi akanta.

Tun farkon neman auranta Sahura ta gaya mini har nake kwa'barta kan tabbatar da abinda baka da sheda a kansa.

Na sanya hannu na d'an share guntun hawayen da ya sauka saman kumatuna sun gama karya mini zuciya yaran yayin da tausayinsu ya zauna a zuciyata me ya fi wannan takaici ace ana binciken sirrin uwarka bayan ta rasu a gano wani abu na takaici wanda ta aikata.

Ban ankara ba kawai na ganta a kusa dani gwiwa a kasa ta kamo hannuna tana fad'in." Anti Amina don Allah ku rufa mana asiri don Allah anti Amina."
Na ri'ke hannunta har na ji yana karkarwa na gane akan abinda take yi wa kuka da tashin hankali kada maganar nan ta fita mutane su gazgata zarginsu.

Sosai na ri'ke ta ina fad'in." Ki kwantar da hankalinki Nusaiba, yadda Ubangijin da ya hallice ta ya rufa mata asiri a lokacin da take raye ya amince da jama'a su ambaci alherinta da kyakykyawan fata har ta rasu to ban ga dalilin da zai sanya don ganin wani sirrinta da ya kasance tsakaninta da Allah ya sanya ni fad'i a gari ba.

Na yi miki alkawari kan cewa ni dai babu wanda zai ji haka daga b'angarena, muna ro'kon Allah Ya yafe mata, mu kuma rayuwarmu ta yi kyau a duniya da lahira ."
Ta dinga godiya cikin rawar murya da tashin hankali.

Na ji maganar Salim yana fad'in." Wannan takardun gidan da ta saya ne a kano da filaye uku sai na shagunanta biyu dai na san haya ta kar'ba amma watannin baya kafin ta kwanta ciwo ta ce mini sun gama magana tana so ta biya kudin duka su zama mallakinta."
Ya ce." To tunda ka ga baka ga shedar mallaka ba a cikin wannan takardun da suke hannunka wata'kila ba ta biya su ba, amma dai ka bincika mana wanda suka bata hayar wajan mu ji daga gare su kafin nan sai a had'a kan komai a zauna domin sauke mata nauyi."
Ya amsa a sanyaye yana had'a kan takardun ya mik'a masa ya kar'ba ya mayar cikin dirowar da kudin da sarkokin.

Sauran biyun da suka zama na karshen fitowa kama bai mayar da su ba.

Tsabar fargaba da tashin hankali a duk lokacin da na dubi mutum-mutimin da ya sha d'auri tamau sai gabana ya fad'i lallai bokan da ya sassa'ka suffofinsu ba 'karamin hatsabibi ba ne.
Chapter 185 · 0% Book details