← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 249 OF 276

Sashe 249

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ashe neman aure ka ke yi ban sani ba?"
Ya kuwa diririce ya juyo ya dube ni da sauri dalili yana da tabbacin na ji abinda ta ce tunda murya ya bud'e..

Ya nemi gefan gado ya zauna da wayar a kunnansa yana sauraranta ni ma duk Ina jin abinda take gaya masa wato Hajiya Ayya ta je har gida ta same ta maganar Nabila domin a yadda ta yi mata bayani ma tana gaya mata sun daidaita junansu amma shi ya ce mata ta d'an saurare shi sai bayan sallah sai a d'aura auran tunda daf muke da mu shiga wataran azimi.

Ya cika da mamaki ainun gabad'aya yanayinsa ya canza da b'acin rai ya shiga rantse mata da Allah kan cewa bai san da maganar ba Nabila dai tana sonsa tuntuni ya gane amma bai yi mata alkawarin aure ba, duk abinda ta je ta gayawa Hajiya Ayya karya take yi.

Hajja ta ce." To ni dai abinda ta zo ta gaya mini kenan sai nace ban sani ba don baka gaya mini ba amma zan tambayaka na ji shin da gaske ne?"
Ya girgiza kansa kamar yana gabanta ya ce." Karya take yi wallahi ban ce zan aurta ba." Ta ce." Ba ka ce zaka aureta ba amma ka san tana sonka tunda gashi ka fadi da bakinka me yasa ka biye mata har aka yi magana da kai kace za ka yi shawara idan da ni za ka yi shawara to babu yawuna ga mata nan da yawa a gari idan lallai auran zaka 'kara ba zan hana ka ba, domin na fahimci tunda aka samu akasin auranka da yarinyar nan Hajara ka ke ta kame-kame babu yawuna wajan auran Nabila kanwar Maryam domin idan ka manta ni uwarka ban manta ba.

Abinda ya faru a baya ba ni fatan ya sake faruwa ba.

Idan za ka yi aure ka duba nagarta da cancanta kada kyale-kyale ya rudeka ka jefa rayuwarka a masifa ka jefa jama'ar da suke kewaye da kai.

Tunda zuciyar taku a haka ta ginu kuma kana ji kana da kudi za ka iya to sai ka zo nan d'ambatta a duba maka wadda ta dace wadda kuma zata zauna lafiya da iyalinka."
Ya furta.'' Babu ma buk'atar karin aure a yanzu Hajja, kuma in sha Allah yadda ki ka ce hakan za a yi dama ba ni da ra'ayin auranta a cikin raina."
Ta ce." Abinda na gayawa Hajiya Ayya kenan zan tambayeka na ji ta bakinka wata'kila duk bada'kalar da ta faru ba ta da labari shiyasa har ta iya zuwa ta same ni domin na hada jini da dangantaka da zuriar Maryam Allah Ya yi mini tsari da su."
Haka suka yi sallama ta yi masa tas!

Ya kashe wayar yana kallona a hargitse ya ce." Wato duk kara da kawaicin da nake yi wa yarinyar nan ba ta duba ba take bin iyayena har tana fad'in mun tsayar da magana bayan sallah d'aurin aure ni mahaukaci ne Amina?"
Na d'aga kaina alam e amma ban ce komai.

Ya nuna kirjinsa da yatsa yana fad'in." Mahaukaci ne ni ko?"
Shiru ban ce masa komai ba dai ya d'auki wayarsa da sauri yana fad'in." Kin ga ni da idonki na goge lambar wayarta tunda bata da hankali ni me zan ci da yar banza."
Bai goge ba ya sake kallona yana cewa." Kafin na goge yana da kyau na yi mata gargadi ba ni son sakarci da shirme?"
Na ce."Tambayata kake yi?"
Ta gyad'a kansa na furta." Lokacin da ku ka yi serving lambar juna ai baka nemi shawarata ba.

Me zan ce maka yanzu duk abinda za ka gaya mata domin ta kiyayeka ka sani ba sai ka nemi shawarar wani ba.

Ya ja tsaki yana fad'in." Dogon rubutun ne ba ni so ai kar'bi ki shiga Whasap din ta ki rubuta mata cewa ba na sonta babu kuma maganar aure a tsakaninmu ta nemi miji daidai da ita ta aura.

Na sanya hannu na kar'bi wayar kamar zan bi umarinsa.

Whasap number dinta na shiga ya yi serving da sunanta Nabila.

Nan na dinga cin karo da stickas na soyayya da gaisuwar Juma'a iri iri tare da wasu irin wasik'u da kalaman soyayya masu motsa sha'awa irin dai yadda matan bariki ke janye hankalin mazan mutane.

Gasu nan birjik kuma idan ta turo yana bud'ewa ya gani amma bai mayar mata da martani ba.

Maganarsu da ta d'an yi tsayi akan tallan kayanta da ta yi masa shine ya kula ta har ya yi mata rubutu a takaice ya ce da ita yana so zai saya.

Kunya da takaice suka hana ni cewa komai na yi kasa da kaina tsabar b'akinciki wasu matan dai rako wasu suka yi duniya.

Babban abin b'akinciki da takaici shine ka turawa mutum sako ka tabbatar ya gani kuma yana hawa online bai baka amsa ba gobe ma ka sake tura masa saboda rashin zuciya
messages kuma irin na soyayya da nuna kulawa har da fatan alheri amma mutum ya share abin da ciwo sosai amma ita kamar kidahuma mara sanin ciwon kai ko wannan ma kora da hali ne an nuna ba a yin ki a fakaice amma kin nace su kansu wasikun da suke d'auke da zantukan soyayya masu tattare da batsa babban dalili ne da zai sanya ya k'yamaci auranta bayan wad'ancan dalilah masu girma.

Duk wayewarsa a gida yake yi a d'aki kuma tare da iyalinsa akwai gogewa a wannan fannin kam yanzu ya yi mata wannan wulakancin tana sake ma'kale masa sautari maza sun fi naci da bibikon macan da take wahalar da su wadda take nuna musu so da k'auna kuma sai su d'auketa sakarai su yi ta wasa da hankalina kamar dai yadda yake yi mata a yanzu ta kasa ganewa.

Na dube shi ina fad'in." Ashe ga dalilin da ya sanya ka kasa fitowa ka gaya mata gaskiyar abinda yake zuciyarka.

Tana yi maka irin wannan zantukan na rashin mutunci ai ka ga duk ranar da ka fito fili ka gaya mata ba ni da ra'ayin auranki za ta daina turo maka kai kuma ba ka so ta daina kana so ta turo ka karanta domin ta motsa maka sha'awa ko?

Ba ka ji kunya ba don girman Allah.

Wataran fa sai dai ka ga ta d'auki hoton wani sashi na jikinta ta turo maka tunda baka tsawatar mata ba ka yi shiru hakan ya nuna mata cewa ta cigaba kana so tunda yar iska ce ita wallahi tallahi ka yi bala'in bani mamaki."
Ya yi shiru jikinsa a mace ya kar'bi wayar yana dubawa messages din da ta tutturo.

Ya jima yana karantawa daya bayan d'aya kafin ya dube ni yana fad'in." Bai zama lallai ki yarda da abinda zan fadi ba.

Amma ki sani cewa ban ta'ba tsayuwa na duba messenges dinta ba balle na fahimci abinda yake a rubuce.

Wannan stickers din kuma idan kin lura wasu sun bud'e da kansu wasu kuma ba su bude ba, ba ni da lokacin wannan sakarcin nata kuma ban san da cewa bata da hankali ba sai yanzu."
Na jima ina kallonsa da ko'karin gazgata maganarsa za ta iya kasancewa gaskiya ne abinda yake fad'i tunda wasu sticks din ni na bud'e su da hannuna Rubutu da karantawa abu ne da dama can yake bashi wahala k'aramar magana idan zai yi ya fi gane ya kira waya zaman sa ma a online babban jidali ne domin da ya hau baya mini goma cikakku yake sauka sai wata goben Kuma idan kuma ka gan shi a online tabbas akwai muhimmin abu.

Na ce." Ka dai ji tsoron Allah wallahi tallahi kuma ka suturta furfurarka ka haihu mata gasunan a gabanka duk abinda za ka yi ka tuna Allah Ya na ji yana kuma yana kallonka sannan kaima kana da zuria.

Ya yi bala'in shan kunu! yana fad'in." Me ki ke nufi ne Amina duk bayanin da na yi miki ba ki aminta ba, har yanzu kin kasa fahimtar abinda zan yi da wanda ba zan yi ba, bayan rantsuwa da Allah da na yi hakan bai yi miki ba kina ganin akwai abinda na boye wanda nake aikatawa, idan har na fahimci maganarki anan kina so ki ce mini ina neman matan banza a waje?"
Na ce." Ni ban fad'i hak.....

Ya katse ni ta hanyar buga gefan katifa da hannunsa na kalle shi cikin kad'uwa da mamaki yanayinsa gabad'aya ya canza.

" Ya furta." Ba ki fad'a ba na yi miki k'arya kenan kuma za ki k'aryata kan ki ne, gashi kina misali akan yarana idan na 'bata na wasu ni ma za a 'bata nawa.

Duk tsayin shekarun da na yi a can baya ban yi aure ba kuma ban yi zina ba sai yanzu da girmana da kuma shekaruna.

Kin jima kina kausasa mini kalamai irin yadda ranki ya so, ba ki da mutunci wasu lukutan ba ki daraja ni, kuma ba kya kar'bar kuskure da ajizancina.

Idan ina neman mata tsayin zamana dake duk takatsantsan dina watarana za ki gane hakan me yasa ba ki da kirki ne Amina."
Cikin tashin hankali nake kallonsa ganin yadda gabad'aya ya rikice har zufa yake yi kamar ba wanka ya yi yanzu ba fitowarsa ya kashe Ac din dake d'akin.

A rikici da b'acin rai ya nuna ni da yatsa yana cigaba da cewa.

" Idan har zan nemi matan banza bari na gaya miki yadda nake fitacce
masu aji da tsabta zan nema irina ba irinsu wannan matar ba da kuka matsanta mini a kanta ba, ina so ki kara sani ni mutum ne mai kishi idan ba dole ba da kuma 'kaddara ba ba ni so na yi tarraya da abu wani ma ya zo ya yi, ban ta'ba sha'awar wannan harkar ba duk tarin ni'imar da Ubangiji ya yi mini, abinda kuma ki ke fata ya kasance kan abinda muka haifa ba zai faru ba tunda ban yi ba Allah ba zai jarrabe ni ba."
Daga haka ya tashi tare da d'aukar hularsa ya sanya ya nufi ma'adanarsa da yake ajiye gilasansa ya zari daya ya sanya ya kwashi wayoyinsa ya kama hanyar fita babu annuri a fuskarsa.
Chapter 249 · 0% Book details