Sashe 63
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni kuwa Ina dariyar na ce." Wallahi anti Yagana dariya kike ba ni, wani irin turare ne wannan da har sai na yi tum'bur haihuwar uwata, na rantse da Allah malaman nan suna nema su jefa mata a masifa."
Ta sha kunu tana cewa." Kina d'auka abin nan da wasa ko Amina, nema ma ki ke yi ki mayar da ni mahaukaciya saboda baki da mutunci ko ina tsaye akanki amma ki sanya ni a gaba kina yi mini dariya ba za ki fahimci abinda nake nusasheki ba sai ranar da ma'kiya suka kai ki 'kasa tukkuna."
Ganin yadda ranta ya 'baci ya sanya na tashi zaune sosai na kar'bi ledar da turaran yake daure Ina fad'in." Zan yi yadda ki ke so anti Yagana"
Shiru ta yi mini tana cigaba da wurgo mini harara.
Babu yadda na iya da ita haka na tashi na fara cire kayan jikina, ya rage daga ni sai rigar mama tana tsaye tana kallona na dubeta tare da cewa." Ko suma din na cire su?"
Ta girgiza kai." Ki bar su kawai ai."
Ban sake cewa komai ba na zuba turaran akan wutar lokaci guda hayakin mai kauri ya tashi na yi sauri na rufa zanin ajikina na dukufa kan wutar ita kuma da sauri ta kama hanyar fita tana fad'in." Kada ki manta ki dinga ambaton sunansa fa."
Na ce." To shikkenan."
Ina jin karar jan kofarta na cillar da zanin na tashi daga kan wutar na matsa gefe ina haki da tari ya sarke ni.
Hayakin ya cigaba da bin iska ina gefe guda.
Na ji motsin bude kofarta a guje na d'auki zanin na je na dukufa kan wutar ta leko tana cewa." To kin ga haka ai ya fi, kin shaki hayakin sosai, in sha Allahu da izinin Allah zai kira waya yau din nan sai a daidaita, malamin ma cewa ya yi hakuri zai bayar."
A zuciyata na ce.'' Anti Yagana da tun farko kin k'adaita Allah ba za ki nufi wajan wani malami ba, suma duk hasashe suke yi.
To haka muka yini muna tattauna sha'anin Hadiza da abinda ta aikata, ni ma yanzu na dawo daga rakiyar Ummansu domin ta zama bakin ganga na yarda itace take dorata a gwadabe mara kyau amma duk lokacin da zata kira ni a waya nuna mini take yi itama Hadizan tafi k'arfinta ha'kuri take da halinta a zahiri kenan amma a bad'ini bakinsu d'aya.
Na riga na gama fahimtar cewa Hadiza da ni take gasa tun daga kan mutuwar aurena kawowa yanzu burinta itama ta tara arziki har ta kere mini.
Tun bayan sallar Isha'i na lura da anti Yagana jikinta ya yi sanyi duk wani abu da take yi babu kuzari domin abincin dare ma ni na yi mana towon samovita miyar ku'bewa tun yamma take ce mini jikinta yana ciwo dalilin da ya sanya kenan tasha Panadol ta kwanta amma dai karin kasalarta yana da ala'ka da dakon kiran wayar Alhaji Tajo domin yadda na fahimta ta gama aminta da abinda malaminta ya gaya mata.
Muna d'an ta'ba hira sama-sama Babandi ya zo, bai samu wata tar'ba ta arziki ba a wajan matar gidan anti Yagana kenan, ni kaina daurewa kawai na yi nake tanka masa amma duk da haka babu cikakkiyar sakewa kamar yadda muka saba, ina jin hakan da ya fahimta ne ya sanya shi yi mana sallama ba tare da ya shirya tafiyar ba domin idan dai za mu had'u muka shafe sama da awa biyar muna hira ba tare da gajiya ba, yanzu kam ko minti talatin bai yi ba ya kama hanya ya tafi ba karsashi a tare dashi.
Anti Yagana ta rakashi da tsaki da harara duk ina kallonta ban ce mata komai ba.
goma da wani abu Babansu Fadila ya shigo ita lokacin ta shiga d'aki tana kintsawa.
Ya tsaya a falon muna dan ta'ba hira da yake akwai sabo a tsakanimu dukda wani sa'in idan na zo garin har na kare kwanakina bai fi sau biyu muke had'uwa dalili shi din babban direba ne kuma yana da muk'ami a tashar da suke ajiye motocinsu da asuba yake fita sai dare yake dawowa kamar i yanzu.
Ya tsaya yana tsokanata da fad'in." Ranki ya dad'e ina kamun 'kafa fa, a cewa maigidan a irin wad'annan motocin nasa muna neman koda guda d'aya ce wadda za mu dinga lodi daga nan kudu, idan haya ake bayarwa a taimaka a ba mu, idan kuma za a ba mu ne sojan haya zuwa shekara biyu in sha Allahu sai mu mayar da kudin, dama tuntuni nake so na samu dama na bi ta karkashinki, kwanaki an ce mana ya rabawa direbobi biyar kuma uku daga ciki ma an ce kyauta ya basu ba mutum biyu ya kar'ba."
Tsakaninsa da Allah yake gaya mini babu wasa a cikin maganar.
Ganin haka ya sanya ni ma na shiga nutsuwata na ce." Aikuwa ban san kana buk'ata ba wallahi tabbas watannin baya na ji yana maganar da wad'anda Allah Ya sa suna da rabo, amma in sha Allahu kuwa zan yi masa maganar idan na koma duk yadda muka yi dashi sai na sanar da kai."
Da farinciki mai yawa ya fara godiya har da kirari kamar wani maroki na dinga dariya ina zolayarsa da cewa sharad'in idan na yi masa hanya ya samu babu shi ba kara aure fad'i yake yi." Na yarda ai tuntuni na gaya mini Yagana ta rufe kofar kece ba ki yarda ba."
Dariya kawai na yi domin nasan yana fad'a ne kawai amma ba har zuciya ba, babu wani namiji da zai so ya rayu ya mutu da mace daya yawancinsu suna ha'kura ne saboda wasu dalilai amma an riga an hallicesu da son mata wannan a jininsu yake akwai ma mazan da suke da tarangahuma sun yarda su tara matan duk abinda ma zai faru sai dai ya faru.
To wad'annan sune za mu kira da masu rashin tsinkaye da hangen nesa.
Ki biyaa ni hakkina kafin ki karanta mini littafi yar uwa akwai hakkina akan ki domin littafin nan na kudi ne.
gajiya na yi da tunani na tashi na je na kwanta wanda bacci da k'yar ya d'auke ni.
Misalin shida da rabi wayar Hamusu ta tashe ni daga b'ingirewar da na yi bayan sallar asubahi
Muka gaisa sosai dalili mun kwana biyu ba mu gaisa ba kamar yasan maigidan yana adawa da hakan a tsukin ya rage kira na a waya sai dai ya turo mini da voice note ta whasap.
Ni ma sai na fi jin dadin hakan.
Nan yake gaya mini Gwaggo ce bata da lafiya dalilin da ya sanya ya kira ni domin jikin nata ya fara tsanani.
Cikin kankanin lokaci na ji hawaye ya cika kwarmin idona.
Gabad'aya sai na diririce hankalina ya tashi sosai, na ce." Hamusu ina nan maiduguri na zo bikin yaran d'an'uwan Dada, ita Gwaggwon za ta san shi tunda tare suka taso.
Amma zan yi kokarin d'auko hanya gobe yadda kake fad'in jikin nata hankalina ya tashi sosai wallahi, ina fatan kun kai ta asibiti.
Ya ce." Kiran da na yi miki kenan, domin babban asibiti nake so mu kaita su bata gado sugar ne da hawan jini, mun je asibitin murtala likita ya dubata ya rubuto magani an Siya kwana biyu an samu sau'ki wallahi jiya kuma sai ta tashi bata iya motsa komai a jikinta, kuma ba damar na yi amfani da kudinki ban gaya miki ba "
Raina ne ya baci jin abinda yake fada.
Na ce." Hamusu wannan wace irin magana ce, ashe akwai ranar da za ka iya nuna mini cewa Gwaggwo ba ta haife ni ba, kudin nawa wanene yake juya mini Ina ce kaine jigo har sai ka tambaye don za ka kai Gwaggwo asibiti wallahi baka taba ba ni haushi ba irin yau."
Ya ce." Ki yi hakuri anti Amina ta wani gefan fa Ina da gaskiya, kudi suna iya shiga tsakanin kowa shiyasa sanarwar take da amfani."
Na ce." Ka ga malam maganar ta isheni haka don Allah, ka je daga dubu daya zuwa dubu dari biyar har abinda ya yi sama na amince muddin akan gwaggo ne.
Sai ya fara godiya ban jira na saurari sauran maganar ba na datse kiran na fita falo.
Anti Yagana tana kicin tana aikin karin kummalo Fadila tana taimaka mata
Yusi da sauran yaran sun fito bakin famfo suna ta burush da wasa da ruwa.
Na dan jingina a jikin bango a sanyaye na ce." Anti Yagana mun tashi lafiya ya hidima?"
Ta amsa hankalinta yana kan abinda take yi, na ce.'' Ina ganin gobe asubanci zan yi zuwa kano Gwaggo bata da lafiya yanzu nan Hamusu yake gaya mini jikin nata sai a hankali."
Ina dire maganar da take bakina Yusi ya zo ya tsaya da burush dinsa a hannuna.
Anti Yagana cikin alhini ta ce." Allah sarki Gwaggwo ciwon har ya kai ace bata san wanda yake kanta ba, kenan tana asibiti a kwance."
Na ce." Ina fa, tana gida saboda shashancin Hamsu bai gaya mini ba har sai da ciwon ya ci k'arfinta wai ya kaita asibitin murtala da farko yanzu kuma abin yayi tsanani shine fa ya kira ni yake gaya mini da abin haushi wai yana neman izini zai yi amfani da kudina.
Ta ja tsaki tana fad'in." Wauta da rashin hankali shikkenan don ya d'auki Gwaggwo ya kaita asibiti da kudinki sai ki ce masa don me, ya ba ni haushi wallahi."
" Wallahi ni ma ba ki ji yadda raina ya baci ba wannan ai shiririta ce rashin lafiya ya wuce komai, kuma ko dukiyata zata kare akan nemawa Gwaggwo lafiya anti Yagana wallahi ba zan damu ba"
Ya girgiza kai tana cewa." Kwarai kuwa ai Ido ba mudu ba ya san kima."
"Mama wai Gwaggo ce bata da lafiya?"
Na dube shi ya zuba mini ido da yanayi na damuwa a tare dashi.
Na ce." E, itace amma jikin da sauki alhamdulillahi."
A sanyaye ya ce." Mama idan za ki je zan biki don Allah....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.