← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 276

Sashe 85

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na gaza ha'kuri na tambaye shi ya ce." Wai fita suka yi suka yi tare da Sadiya tafiyar kasa mai tsayi saboda rashin hankali tasan tana da karamin ciki bayan sun dawo gida shine take ganin jini kad'an kad'an wai tana tunanin cikin zai iya zubewa dole sai an yi d'aurin mahaifa."
Da damuwa a tare da ni na ce." Aikuwa dai yana da kyau ta yi gaggawa zuwa asibiti gobe wata'kila tana da matsalar mahaifa bata da k'wari shine dalili amma kuma itama ta yi ganganci yin doguwar tafiya a k'afa tana da karamin ciki kamar ba ma'aikaciyar lafiya ba.

Ya ce." Abinda take zargi kenan idan cikin ya zube ai ta huta."
Ya k'arasa maganar cikin takaici da jin haushin lamarin.

Haka kawai na ji na damu da hakan domin har ga Allah bana so wani abu ya samu cikin Hauwa ba don komai ba sai don ganin tabbatuwar farinciki da walwala a fuskarsa.

A yanzu dai zuria itace karshen abinda yake nema a wannan duniyar bayan Allah Ya wadatashi da komai a duk lokacin dana kalleshi na tuna har yanzu bai ajiye magaji ba hankalina yana tashi sosai kuma nakan zubar da hawaye masu yawa domin jarabawar da ta same mu ni dashi na riga nasan ko na saki zuciyata da gangar jikina na haihu za mu sanya rai ne akan abinda muka samu bayan kuma ba mai d'orewa ba ne.

Astagfirullahi wannan shine babban dalilin da ya sanya nake ji a cikin raina ko cikin na samu zan iya zubar dashi ba tare da ya sani ba don gudun shiga damuwa matsananciya bayan na bari na haihu muna ji muna gani mu rasa abinda muka samu kamar yadda muka rasa babynmu ta farko.

Abin mamaki da daure kai a wannan daran ma na jigatu kwarai da aniya a hannunsa don ban ta'ba tsammanin ma zai neme ni ba ganin irin jimawar da muka yi jiya muna abu daya.

Abu na biyu kuma a tunanina gagarimin rashin da ya yi zai dakusar dashi kewar komai na jin dad'in duniya ashe ba haka abin yake ba fahimtata ma kamar idan yana cikin damuwa ya fi kulafucin lamarin washe gari na tashi da ciwon jiki matsananci domin irin sarrafuwar da na yi a hannunsa a daran jiya Ina ganin ko ko kwa'babbiyar fulawar borodi ba ta kaini buguwa ba.

Ina kwance gado bayan na yi wanka na kasa tafiya gidan rasuwar Yusi ya shigo yana gaya mini wai anti Nabila kanwar Hajiya Maryam tana kira na zo ko zan iya rarrashin antin nasu ta karya kumallo.

Na ce masa ya je ganin zuwa yanzu.

Da kyar na rarrafa na tashi na sanya hijabi saukata kasa ta yi daidai da shigowarsa hannunsa da ri'ke da carbi da alama daga wurin kar'bar ta'aziyya ya taso ya ce mini na je maza wurin Hajiya Maryam na zauna tare da ita yanzu Adam yake sanar dashi an yi an yi da ita ta ci abinci taki ci.

Na ce yanzu Yusi ya zo ya sanar da ni.

Na fahimci tunda aka yi rasuwar yake bawa abinda ya danganci matar muhimmanci don jiya ma shine ya k'arfafa mini gwiwar zama a kusa da ita a cewarsa zan deba mata kewa bayan 'yan uwanta.

Ban ta'ba kawo komai ba a cikin raina abinda dai na ajiye shine bai ajiye lamarin Alhaji Amadu a nesa ba domin kuwa Allah ne kadai yasan irin taimakekeniyar da suka yi wa juna ba a lokacin da suke neman rufin asiri na duniya.

Hajja suka sauka kamar yadda ya fad'a Hajiya Saratu da kannan mahafinsa su biyu Maza a ciki akwai mahafin matashi ta biyu wato Aysha wadda ta rasu sakamakon zazzabin typhoid kafin ta tare a gidanshi.

Ba sosai na sansu ba duk da kasancewar suna da yawa kad'an na sani daga cikinsu, hakan yana da ala'ka da rashin zamanmu a gari tun bayan aure dangin Hajja ma in banda rasuwar da aka yi ta kanin mahaifin Hauwa babu wanda nasani daga cikinsu.

Wannan karon mun sake sosai da Hajja da alama sihirin da aka yi mata ya warware babu wani kallo na baibai a tsakanina da ita sai mutunci da girmama juna.

Haka aka yi zaman makoki na kwanaki bakwai mutumin nan bai daga kafa ba.

Kullum da safe zai fita cikin jama'a ya kar'bi gaisuwa da daddare kuma sai ya rikid'e ya koma jarababbe na bugawa a jarida.

Wannan dalilin ya sanya na yanke shawarar guduwa ba zan iya ba don ban san abinda ya zama ba kuma idan zai jima anan din bai koma legos din ba Hauwa sai ta zo ta kar'bi lamarinsa domin dai sha'aninsa ya fara ba ni tsoro da mamaki.

Ban sanar dashi maganar data assasa mini zuwa ba sai bayan an share makoki kwanaki tara da rasuwar tukkuna na gaya masa amma ta sigar da ba zai zarge ni ba ai taimako ne kuma duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi sosai na gaya masa yadda alhaji Muntari ya dinga fad'i tashin akan lamarin yarana kuma ya rike mini su ba tare da ya bambamtasu da wanda ya haifa ba, na kara jadadda masa cewa abinda ya asassa mutuwar aurena dashi akansa ne saboda rubutun da na yi a fece book akan abinda ya faru wanda ya danganci Kamalu dashi.

Bayanin da na yi masa cikin nutsuwa ya sanya ya fahimce ni ya kuma tausaya mutuka da gaske koda yake dama shi mai tausayi dalilin da ya sanya mini fargabar gaya masa saboda tsohon mijina ne ban san fassarar da zai yi mini ba.

A take a lokacin ya ce na yi waya da Baba Sule duk abinda muka tattauna sai na sanar dashi zai taimaka in sha Allahu.

Ban yi kasa a gwiwa ba kuwa na kira Baba Sule a waya ya gaya mini har yanzu dai ba kai ga kar'bar kudin gidan ba domin duk wanda zai zo tayin wulakanci yake yi.

Na ce masa to abar batun sayar da gidan za a biya masu hakki hakkinsu insha Allah rabbi duk wanda yasan yana bin Alhaji Muntari kudi ya yi mini list din sunansu a takarda tare da asusun ajiyarsu idan na dawo sai ya kawo mini ni kuma zan tura masa sunayensu ta whasap sai a biya su hakkinsu.

Na sanar dashi yadda muka yi da ya ce hakan ya yi amma fa na ajiye maganar tafiya don su Hajja ne kadai za su tafi bi ba yanzu sai nan da kwana talatin lokacin Alhaji Amadu ya yi arba'in da rasuwa shi ma kuma a daidai lokacin zai koma bakin aiki can Legos.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*58*
Zaune na tashi ina goge hawayen idonta na dube shi sosai kafin na ce." Ba ni da ajandar komawa gidan Alhaji Muntari domin kuwa da da niyyar hakan a cikin raina wallahi tallahi da kaddarar aure ba ta ratsa tsakanina da kai ba."
Na numfasa Ina kallonsa yayin da shi kuma ya sake hade fuska tare da zubo mini ido da yanayi na neman rikici a tare da shi.

"Abu daya zuwa biyu ya sanya ni kokawa da rasuwar bawan Allan nan ko ka yarda ko kada ka yarda bai dame ni ba na farko shine hallacin da ya yi mini a lokacin da nake buk'atar agaji ya yi mini da kudi da karfinsa daidai gwargwado.

Na biyu yadda gidansa ya tarwatse tun yana raye yaranshi suke walagigi ina ga kuma bayan rasu.

Maganar nan da muke yi da kai a yanzu hankalina nakan babban yaronshi Turmuzi wanda tun asali nasan da cewa fitinanne ne an ce mini yanzu lamarinsa ya sake ta'barbarewa, ba zan manta ba mahaifinsa ba ya sha kokawa akan sha'aninsa.

Wad'annan abubuwa biyu dana lissafa maka sune suka fi tsaye mini a rai domin kuwa na riga nasan sha'anin zumunci a yanzu ya zama abinda ya zama tunda can ma danginsu ba masu zumunci ba ne balle yanzu da baya raye kuma dama shi kadai ne mai dan rufin asiri a cikinsu.

Ni uwa ce kuma na yi gwagwarmayar rayuwa da yarana nasan zafin da ake ji idan aka rasa wani 'bangare dalilin da ya sanya kenan nake tausayawa Anti Maimuna uwargidanshi domin ita amaryar ta gudu ta watsar da yaran yanzu gabad'aya suna hannunta kusan su tara ka gaya mini ya za ta yi dasu wane hali za ta shiga domin ciyar dasu da basu tarbiya.

Shiru ya yi bayan na kammala maganata ya gyada kansa a d'an kausashe ya furta." Wannan shagube ne kawai Amina, ni kike so ki yi wa guri a matsayinki na uwa ko?"
Na yi kasa'ke ina kallonsa tare da auna maganarsa domin na gaza fahimtar inda ya dosa.

Ya d'ora da cewa." Af ai ni na uba ba ne, tunda ban haihu ba ban san zafinta ke da ki ka haihu ke ce ki ka san ciwon haihuwa."
Jikina ya d'an yi sanyi jin yana nema ya canza magana nasan hakan baya rasa nasaba da masifar kishin da yake kasa sarrafa shi shine dalilin da ya sanya yake jujjuya maganar dole sai ya fusata ni.

Sai kawai na share shi ban sake cewa masa komai ba na koma na kwanta hawayen na sake bin gefan fuskata.

Ni har ga Allah mutuwar Alhaji Muntari ta dake ni sosai na kuma kara tabbatar da cewa duniyar nan aikin banza ce.

Wannan ya sanya ni rushewa da kuka da karfin gaske ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ya kuwa zabura! da ganin yadda nake kuka haikan!

Sai jikinsa ya yi tubis ya matso kusa da ni sosai yana d'an jijjiga kafafuna da hannunsa.

Na sake tsananta kukan da nake yi had'e da jan hanci.
Chapter 85 · 0% Book details