← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 276

Sashe 110

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To shi ma sai a ka ci sa'a ya yi amfani da hikima wajan ganin ya isar da sa'kon da yake so ya isar din wanda shi ma daga 'bangaransa na fahimci abin ya yi masa ciwo sosai, kuma kamar yadda ya fad'a din na tabbatar da baya sona da buk'atar cigaba da zama da ni ba zai ta'ba bibiyata da nufin kome da sulhu ba, duk da Baban Saude bai yi amfani da tsautsauran kalamai ba, amma yadda na fahimta ya ji haushi kawai ya danne ne domin samun a zauna lafiya.Tabbas idan hakane kuwa Ina da ya'kinin zai gyara anan gaba tunda na lura ya tsani a kai shi k'ara don ko lokacin da na ta'ba Kai shi 'kararsa wurin Hajja akan lamarin Hamusu fushi ya yi da ni mai tsanani idan ban manta ba ya dinga gaba da ni sai da kyar ya sauko.

Dama tun asubahi ya ce na yi duk shirye-shiryen da zan yi jirgin karfe takwas za mu bi zuwa abuja kafin lokacin ma ya cika mun fito ni dashi a kintse Sukairaju dama tuntuni ya sanya mana kayanmu a mota.

Kafin mu isa airport din Anti Yagana ta kira ni a waya kamar yadda ta fada na ce mata ai mun riga ma mun fito muna mota zuwa filin jirgi.

Sai ta ce na had'ata da shi.

Ba tare da na ce komai ba na mik'a wayar tare da gaya masa anti Yagana ce take so ta yi magana dashi.

Ya kar'ba a nutse suka gaisa sai kawai ta fara yi masa godiya har ina jin yadda muryarta take rawa godiya sosai na abin alherin da ya yi wa su Dada da Baban Saude.

Sai kuma alkawarin kyautar motar da ya yi wa maigidanta.

Da kulawa sosai ya nuna mata cewa ta daina yi masa godiya akan abinda ya yi, ai duka an riga an zama daya don haka ba abin mamaki da godiya ba ne akan duk irin abinda zai yi mana.

Ta cigaba dai da godiya dai har tana cewa dashi ya kara da hakuri dangane da zamantakewa ta dashi in sha Allahu wani abu ba zai sake faruwa ba.

Ya ce mata babu komai shi ma a b'angaransa magana ta wuce hakan ba zata sake faruwa ba.

Suka yi sallama ya miko mini wayar muka dan yi magana kafin ta katse kiran.

Ya dube ni a tsanake yana ce wa." Yagana mutuniyar kirki ce sosai Amina."
Murmushi kawai na yi ban ce masa komai ba, tunanina yana can wani waje na daban.

Ya gaya mini ni da Hauwa ne za mu sasanta kanmu abin nufi shine za mu raba zama.

Wata shida a Legos wata shida a Abuja.

Abinda yake damuna shine mai yasa ita Hajiya Maryam din ba za mu raba da ita ba, ai matarsa ce ita kamar yadda muke matayensa.

Ban ga dalilin da zai sanya ya ce mu biyu ne za mu dinga wannan zurga-zurgar ba.

Ba na so na yi wata magana ne ya ga kamar kishi ne ko neman fitina shiyasa kawai na yi shiru amma zahiri wannan hukuncin bai yi mini ba kuma sai na rusa shi domin kuwa ba zan ta'ba yarda ya kafa abinda nasan lallai anan gaba zai zama rikici ba.

Muka isa abuja wajan sha daya na safe.

Gidanshi yana nan tsaf tunda akwai hadimai tare muka shiga amma ko zama bai yi ba ya sake fita sai zuciyata ta shiga wasiwasin akan fitarsa da gaggawa irin haka.

Tun d'azu a mota kafin zuwanmu airport na ji sun yi waya da ita sai nake zargin gidanta ya nufa.

Zuciyata ta cika da takaici da b'akinciki irin yadda yake rasa sukuni akan sha'anin matar nan abinda yake yi yana nema ya wuce gona da iri ban hana shi kula da matarsa ba amma yana da kyau ya daina nuna muguwar damuwa da ita a gabana domin kuwa ba zan iya jura ba.

Ina fitowa daga wanka Yusi ya shigo.

Na zuba masa ido har ya k'araso wajan da nake gefan gadon yana dariya yaro ya zama wani lafiyayye ya yi haske da kyau sai kace wanda yake rayuwa a k'etare kayan jikinsa ma abin kallone.

Ya zauna kusa da ni tare da ri'ko hannuna ni kam kallonsa kawai nake yi na kasa cewa dashi komai.

Ya ce." Mama ina yini."
"Lafiya lau Yusi kai ne kuwa?" Na fad'a ina d'ago fuskarsa.

Sai kece da dariya yana cewa." Ni ne mama me ki ka ga ni?"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali na ce." Na ga abubuwa da yawa Yusi wanene ya gaya maka na zo?"
Kai tsaye ya ce." Baba ne Yana gidan Momi shine yake gaya mini tare kuke wai na zo mu gaisa." Yana rufe bakinsa Adam ya shigo da sallama a nutse ya k'araso wajan da muke jikinsa sanye da irin kayan dake jikin Yusi.

Bashi da jikin girma da alama ya d'auko jiki irin na Mamansa ya d'an risina yana gaishe ni na amsa da kulawa.

Ina fad'in" Adam mai kuke bawa Yusi ya zama d'an lukuti haka?" Ai kuwa sai ya fashe da dariya yana kallonsa ya ce." Wallahi babu komai Mama jikinsa ne irin haka momi ma kullum da asuba sai ta sanya shi ya motsa jikinsa amma baya raguwa gashinan duk ya fi mu girma.

'Yar dariya na yi tare da cewa." Abinci zai rage ciki kawai idan ba so yake yi wataran ya kasa tashi ba." Ya ce." Haka ma Yaya Salim ya ce wai sau biyu zai dinga cin abinci a rana kuma daban da irin wanda muke ci ba shine Momi ta ce a'a, a kyaleshi 'kibarsa ta kuruciya ce yana zama saurayi zai sa'be, ba zai daina cin abinci ba."
Na gya'da kaina ina d'an murmushi zuciyata kuma cike take da nazarin irin rikon da matar take yi wa yaron ko ni dai da na haife shi albarka tunda ga zahiri nan na gani da Ido.

Jikina ya sake yin sanyi sosai to ai da kunya da nauyi a ce na bijiro da wata fitinar wadda zata kawo rud'ani a tsakaninmu.

Tare suka fita da zummar zuwa su yi shirin tafiya islamiyya sha biyu na rana suke shiga su tashi shida na yamma.

Gudun aure littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Shi kam maigidan ai tunda ya fita din nan bai shigo ba sai bayan la'asar wajan hud'u da rabi Ina zaune a falo cikin daya daga cikin kujerun da suke jere.

Gajiya na yi da jiranshi ga yunwa ina ji a gaban idona kukunsa ya gama shirya komai a teburin cin abinci.

Na tashi na je na d'iba daidai cikina na dawo falon na zauna ina cin abincin zuciyata na tunanin abin.

Shi kansa sai da ya ji nauyi da kunya a lokacin da ya shigo ya same ni, ni kadai a zaune sai tibin dana kunna.

Ya zauna a gefana yana fad'in." Amina kin ji ni shiru ko, ina can wajan Momi ne tun jiya take fama da zazzabi da mura."
A takaice na ce." Allah Ya sawwa'ke." Daga haka ban sake magana ba.

Na cigaba da cin abincina cikin nutsuwa.

Sai ya ce." Yusi ya shigo ko?"
"Eh Ya shigo tare da Adam.'' Ya furta." Ni ne na gaya masa ya zo ku gaisa."
Na ce." Ai kuwa ka Kyauta."
Shiru ya yi yana dan kallona da wani yanayi kafin ya ce." Mai ya faru na ga yanayinki ya canza ko ni ne?"
Ya fad'a yana matsowa kusa da ni.

Cikin zuciyata na ce aiki ya same ka.

Shiru na yi ban ce masa komai ba.

Ya tsargu sosai don gabad'aya kin sakar masa fuska na yi.

Ganin haka sai ya tashi ya haye sama.

Na yi zamana ban bi shi ba domin wallahi har cikin zuciyata haushinsa nake ji.

Ni ba zuwan da ya yi wajenta ne yake ba ni haushi ba yadda yake d'aukar lamarinta da muhimmanci shine abinda ya fi 'kona mini rai.

Yanzu ga matarsa can a wata uwa duniya d'auke da cikinsa amma ban ji ya kira ta ba tun jiya ai muna tare maganarta ma bai yi mini ba.

Amma kan wannan tsohuwar yanzu sai ya gigice.

Bai sauko ba sai daf da magariba, Ina zaune a falon ina kallon wani movies da ya d'auke mini hankali
Na hangi saukowarsa cikin jallabiya da hula tashi kafiye naci a saman kanshi cikin shirin shiga massalaci.

Janye idona na yi daga kansa shi ma bai ce mini komai ba ya fice.

Na sauke ajiyar zuciya a hankali na tashi na hau saman domin gabatar da tawa ibadar.

Ana idar da sallar ya shigo.

Na lura yana so ya gyara abinda ya yi a d'azu shiyasa ya dawo da wuri.

A saman dadduma ya same ni a zaune na idar da sallar amma ban tashi ba.

Ya zauna kan wata kujera mai kamar gado da take can wani gefe a d'akin.

Yana fad'in." Idan kina idar miko mini Loptop dina ga ta nan a gefanki.

Ba tare da na ce komai ba na tashi na je na d'auko masa ya kar'ba tare da nuna mini wajan zama a gefansa.

Zama na yi da hijabin a jikina.

Shiru ya ratsa wajan yana ta dube-dubensa bai ce komai ba.

Sai da ya gama tsaf sannan ya rufe computer ya dube ni tare da cewa." Za mu je gidan Momi ki dubata ko?"
A sakarce na ce." Wacece Momi?" Duk kuwa da cewar na gane wadda yake kira da sunan irin yadda na ji yaran na kiranta da shi.

Ya ce." 'Yar uwarki mana, da gaske ba ta jin dad'i kin san zafin zazzabi da mura dai."
A nutse na ce." Mai zai hana ni zuwa na dubata, to Allah Ya sawwa'ke."
Ya amsa da "Amin."
Shiru ya sake biyo baya kafin na ce." Ya Hauwa kuna waya ko?

Da sauri ya ce." Sosai ma kuwa, d'azu nan kafin na shigo sai da na kira ta, wannan watan da ya mutu shine na haihuwarta har wani ya kama sakamakon scanning ya nuna bakwai ga wannan watan da muka shiga shine daidai lokacin da suka bada result.
Chapter 110 · 0% Book details