← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 276

Sashe 16

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
*9*
Na dube shi babu fargaba tare da ni na ce." To ai ba haka ake yi ba, kasan ina da hidima da nauye nauye a kaina, me zai sanya lokaci guda ka zo ka ce zaka rusa mini tsarina na shekaru da yawa, idan an yi mini haka zahiri ba a yi mini adalci ba, tunda babu wanda ya san irin wahalar dana sha kafin na ginu.

Ina da yara ina da iyaye da 'yan'uwan da nake taimaka musu to me zai sanya sa'i daya ka zo ka ce ga yadda zan yi."
Ya zuba hannuwansa cikin aljihun faffadan wandon da yake jikinsa ya ce" idan na fahimce ki wato har yanzu kina da burina cigaba da tallata surar jikinki da zummar kasuwanci ko?" Shiru na yi ban ce masa komai ba.

Sai ya cigaba da cewa." Ke ko kunya ba kya ji ko wane titi da hotonki a sa'kale kina yake hak'ori da gantsara jiki meye abin burgewa a ciki.

To bari kiji duk titin da aka kawo mini rahoto anga hotonki nasa an cire, hakan ne kuma zai faru harkokin zasu tsaya cak muddin ba ki yi yadda na ce ba."
Yana gama maganarsa ya kama hanya ya fice daga d'akin da b'acin rai.

A daidai lokacin ne kuma Yusi ya fito daga bandaki bayan ya yi wanka.

Cikin takaici na gama shiryawa na zauna duk raina babu dadi, maganganunsa kawai suke ta yi mini yawa a k'wa'kwalwata.

Ban yi tsammanin zan samu wata matsala daga wurinsa ba don a tunanina tunda ba auran soyayya muke yi ba, ba zai shigar mini hurumi ba, to sai gashi tun ban kwana a gidansa ba ya fara kafa mini wasu sharadai.

Ai ko na goge komai a shafukana na intranet ban isa na goge wanda yake cikin wayoyin mutane ba.

Kuma duk tsiya tarihi ba zai ta'ba mancewa da sunana ba.

Zan goge kamar yadda yake so sai dai dole na nemi wata hanyar domin cigaba da janyo hankalin customers ba zai yiwu na yi wahala tsayin shekara da shekaru ba lokaci guda wani ya rusa mini buri.

Ban shigo gidansa da niyyar na ci dukiyarsa ba, ni nafi gane na nemi na kaina kawai yafi rufin asiri a duk lokacin da zan yi wa wani alheri ba ni da matsala sai dai na cire ba tare da na je na yi ro'ko ba.

Gabad'aya cikina cunkushewa ya yi na kasa cin komai don sai bayan isha'i ma muka fita falon da zummar cin abinci.

Lokacin tuni shi ya fita sai wani matashi majiyin karfi da yake ta goge a wurin.

Ya gaishe ni.

Na amsa a tsanake.

Wurin abincin muka nufa nida Yusi, shi kuma mai aikin ya fita da sauri.

Da kyar na iya cin loma hud'u shinkafa ce dafaduka wadda ta ji kayan lambu da nama.

Ga lemuka nan birjik da yake ni din ba ma'abociyar shan lemo mai gas ba ne ko daya ban bud'e ba ruwa kawai na kurba na d'auki wayata ina dubawa.

Shi Kam Yusi ya zage ciki sai cin abincin yake yi hankalinsa a kwance.

To haka muka yi kwanan kadaici da zullumi.

Yusi dai bacci ya yi sosai, ni kuwa ban iya baccin arziki ba, domin mafarkai na dinga yi marasa kan gado, gashi muna ta fad'a da maigidan, ina ta kuka, sannan na zo na kama mafarkin Kamalu.

Yadda Allah ya nuna mini shi a mafarkin ya kwantar mini da hankali, domin a nutse na ganshi da allo a hannunsa yana rubutu da tawada da alkalami.

Da asuba da nayi sallah nayi masa addu'a sosai da sosai na roki Allah Ya shirya mini su gabad'aya.

Game da mafarkin da nayi da maigidan muna rigima kuwa, ban kawo komai ba a cikin raina, na dai fi tunanin sa'insar da muka yi jiya ce ta assasa mafarkin.

Da wuri mukayi wanka muka shirya da yake dama koyaushe cikin sabbin dinkuna nake ban da matsalarsu.

Na shirya cikin atamfa mai ganye wadda akayi wa dinkin bubu da uban aiki a jiki.

Normal na daura dankwali ban yi wata kwalliya ba in banda mai dana shafa.

Sai na yi amfani da wata humra da Ya Falmata ta aiko mini da ita.

Innalillahi ai gabad'aya d'akin dumewa yayi da bala'in kamshin humarar mai fizgar hankali.

Kad'an na shafa amma jikina ko'ina ya dauka.

Ina da bala'in son kamshi shiyasa turare ko nawa ne bana ganin k'yashin saye.

Wannan humrar ma tabbas zan tura kudi a sake kawo mini wata domin ta yi mini dadi sosai....08089965176
Yusi ma ya shirya cikin kananun kaya.

Muka nemi wuri muka zauna ganin yadda ya yi zukudum yasa na mika masa wayata.

Ya kuwa kar'ba da sauri yana murmushi.

Sai na dan zame na kwanta tare da rufe idona ina tunanin yadda za a yi na je duba Kamalu daga nan.

Hakan ba zai yi wu ba dole sai da Hamusu domin shine ya kai shi makarantar tafiyar kuwa dole sai dashi.

Kira ya shigo wayata na bud'e idona tare da tashi zaune na kar'bi wayar daga hannun yaron.

Koda na duba sai naga maigidan ne.

Na daga tare da daidaita nutsuwata na gaishe shi a tsanake ya amsa yana cewa "Ki fito falo zan yi magana da ku."
Bai bari na amsa ba ya kashe wayarsa.

Tsaki naja na dan harari wayar tare da fad'in." Yusi ta shi muje falo."
Ya sauko daga gadon muka kama hanyar fita.

Yana zaune cikin kayan bacci masu santsi kirjinsa duk a waje.

Na yi gaggawar kawar da kaina gefe dan ko da zan gaishe ma ban kalleshi ba.

Ina jin ganin ganin hakan ne ma ya share bai amsa mini ba.

Sai ya janyo hannun Yusi yana ko'karin d'ora shi a cinyarsa duk girmansa kuwa.

Yaron yana nokewa shi kuwa Fadi yake." Aboki ba magana, mu gaisa mana." Yana ta mika masa hannunsa.

Ina kallon Yusi yana sinne kai da murmushi a fuskarsa ya rike hannunsa yana cewa." Barka da asuba Baba." Sai ya amsa da sakkakkiyar fuska don yadda yaron ya kira shi da Baba ya faranta masa rai sosai.

Yana cewa." Ya kwanan bak'unta wace makarantar kake so na sanya ka"
Saurin sabo da wayewa irin ta Yusi tana ba ni sha'awa sosai, bashi da gidadanci ko kad'an.

Ganin yadda suke ta rahar kamar uba da dan cikinsa sai jikina ya mutu mutuka da gaske.

Dole ko na ki ko na so na sassautawa mutumin domin hanyar da ya d'auko mai karya lago ce, duk wanda yake nuna k'auna da kusanci kan abinka tabbas kai yake so, koda yana yin hakan ne da zummar yaudara ya faranta mini rai da wannan Alhaji Muntari ya siye zuciyata har na aminta na aure shi.

Haka zalika ma wannan mutumin hanyar da ya d'auko kenan.

Jikina ya shika sosai na dinga satar kallonsu ina dan murmushi kamar wadda aka yi wa dole....

Ya dube ni a hankali yana cewa." To ke wace makarantar kike ganin za a kai shi umm?" Sai na fara dibi-dibi domin kwarjini ya yi mini a lokacin da yake tambayata da kyar na furta." Duk wadda aka kai shi Yallabai, Allah Ya saka da alheri.''
Ya amsa da "Amin." A takaice kafin ya dan lumshe idonsa ya bud'e su a kaina muryarsa can kasa ya ce." In sha Allahu za a kai shi makaranta mai kyau boko da islamiyya sai ya dora karatunsa a inda ya tsaya Allah Ya bashi sa'a.

"
Na amsa da "Amin Ya Allah mun gode sosai Allah Ya kara arziki."
Har muka gama karyawa ina ta diri dirin yadda zan gaya masa na goge duk abinda na yi posting din kamar yadda ya buk'ata.

Wani kwarjini ya kara a idona sakamakon irin karamcin da ya nuna mini akan yarona.

Hankalina ya d'auke wurin tunani na ji maganarsa yana cewa." Mu ga wayarki."
Ban yi jayayya ba na mik'a masa.

Ya kar'ba yana dubawa sai ya ce ." Ai ba ki bud'e mini ba."
A hankali na ce." Sunana ne da karamin harafi." Ya yi shiru bai ce komai ba.

Yadda yake lallatsa wayar shi ya tabbatar mini da cewa ya bude.

Akwai lambobin mutane da dama.

Har da maza abokan nan kasuwanci ne, saboda wasu idan sun ga tallan kayanmu sukan kira su ce suna so su sayawa iyalinsu kaya.

Sai da ma naga abin yayi yawa ne ya sanya na sayi sabon layi na mussaman domin hakan yana wayar Hamusu yanzu haka, amma dai duk da haka akwai wasu a wayata kuma ban yi tunanin ajiyesu zai kawo mini matsala ba tunda babu abinda yake had'a ni da mutum sai idan ya bukaci wani abun.

"Wanene Hamusu na ga kina yawan waya dashi da sa'kkonin gasu nan da yawa ."
Tambayar da ya jefo mini kenan fuskarsa babu yabo babu fallasa.

Wannan littafin na kudi ne 'yar uwata k
da ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ban ji dadin yadda yake mini bincike a waya ba, amma abinda ya yi mini a yanzu shi ya kautar da b'acin raina na jure ban nuna jin haushina ba na ce." Kanin Babansu Yusi ne."
Ya zubo mini idonsa kuri! yana kallo.

Sai na ce." Shine wanda na dam'kawa ragamar kula mini da harkokina tunda gaskiya ba zan boye maka ba mun saba sosai kuma yana da amana, na d'auke shi kamar d'an'uwana na jini."
Shiru yayi bai ce mini komai ba yana dai ta cigaba da duddubar wayar.
Chapter 16 · 0% Book details