Sashe 190
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.
Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.
In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.
Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.
Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.
Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.
Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.
Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.
Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book complete 2k akan telegram normal What'sapp group kuma 1k via 0542382124....
Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*128*
Haka na yi ta zaman jiran ganin Malam Rabi'u ya yi mini izinin shiga d'akin malamin shiru har dare ya yi nis
a ban ji daga gare shi ba hakan nan na ha'kura na kwanta a wannan daran ma bacci sai dai b'arawo domin da ya d'auke ni na 'yan mintina zan bud'e ido har dai asubahi ta yi motsin iyalin gidan ya sanya ni tashi na fito da buta cike da ruwa wadda Hajara jiya ta ajiye mini kafin ta je ta kwanta.
Na jima saman abin sallah ina jan carbi bacci ya fara shammatata tunda dama shi ba a cin bashinsa.
Na ji maganarsa yarinyar tana fad'in." Ina kwana."
Na bude idona da sauri tare da shi zaune ashe har na kai ga kwanciya kan daddumar ta ajiye mini dogon kofi na kunu da silbar k'osai a gabana ta juya ta fita minti biyar a tsakani ta dawo da wata langa ta ajiye mini da ruwan pure water guda biyu.
Na bude langar dumamen towo ne na masara miyar kuka tana ta k'amshin daddawa da zafins
nan da nan yawuna ya tsinke na mike na fita.
Yaran gidan da alama sun shiga makaranta domin shiru babu hayaniya kamar koyaushe.
Inno na bakin tukunya da kwanuka a gabanta ta juyo tana kallona sai ta saki fuskarta tana fad'in." Hajiya kin fito.
Na daure sosai ganin yadda matar ke ko'karin ganin lallai sai ta faranta mini da kwantar mini da hankali na ce." Eh ina kwana ya hidima na gode sosai Allah Ya saka da alheri.".
Ta amsa cikin dadi tana fadin." Ai na ce Hajara ta kawo miki dumame nasan zai yi miki dadi."
Na ce." Sosai ma kuwa wallahi Allah Ya saka da alheri."
Ta amsa da Amin ya rabbi." Bakina na wanke na koma d'akin zuciyata cike da zullumi haka na ci towon nasha ruwa d'aya na fito tsakargidan shiru matan gidan na d'akunansu.
Can bakin 'kofar fita na nufa na lura wajen akwai network sosai na kira Sahura muka gaisa na ce." Sukairaju ya zo jiya ne?" Ta ce." A a sai yanzu dai ya zo kin ga ina shiryawa wai me yake faruwa ne ya ce mini Yallabai ne bashi da lafiya kuna kauyen Bunkure."
Na ce." Sahura abubuwa da yawa sun faru masu muni ba zan iya ba ki labari a waya ba amma ina cikin tashin hankali mai tsanani"
Ta ce." Idan babu damuwa zan iya biyo Sukairaju ko Amina wallahi hankalina ya tashi ban san a wane hali ki ke ciki ba." Cikin rauni take maganar.
Na ji zuciyata ta yi nauyi lallai Sahura masoyiyace ta hakika duk lokacin da na shiga matsanancin hali takan rasa sukuni tun muna 'yan mata haka muke idan daya ya shiga wani yanayi duk sai mu rasa sukuni."
Na daure na ce." Me zai hana ki biyo shi amma bai zama lallai ki samu ganin Yallaban ba tunda ni ma sau daya na ganshi malamin baya bari."
A sanyaye ta furta." Zan dai biyo shi Amina domin ganin halin da ki ke ciki idan kuma ina da sa'a sai Allah yasa a bar ni na shiga na duba shi din."
Na ce." Shikkenan duk abinda ki ka san zan buk'ata ki kawo mini Sahura zama ya kama ni dole."
Ta ce." In sha Allahu."
Na kira layin Anti Yagana cikin sa'a ta shiga na sauke ajiyar zuciya ina jiran ta daga na ji maganarta tana kiran sunana na amsa a sanyaye.
Ta ce." Ya aka yi Amina ya kuke ya yaran fatan kowa lafiya, ki yi hakuri sosai domin ke nauyi ya hau a yanzu ki yi kokarin ganin kin ri'ke yaran nan na Maryam tsakani da Allah domin ki rabauta da lada."
Na ce." In sha Allahu anti Yagana amma akwai matsala fa."
Ta ce." Menene kuma?"
Shiru na yi domin ban ma san ta yadda za a yi na fara yi mata bayani ba.
Ta sake maimaita tambayarta murya na rawa na furta." Maigidan ne ba shi da lafiya anti Yagana ina nan kano wani gari Bunkure ana yi masa magani."
A dan tsorace ta furta." mai ya same shi Amina amma tun yaushe me yasa ba ki gaya mini ba?"
Na ce." Anti Yagana duk yadda za a yi na yi miki bayani ba za ki fahimta sosai ba tunda a waya ne, abinda zan iya ce miki anan shine matarsa ce da ta rasu ta yi masa asirin rai da rayuwa yanzu haka yana kwance sai dai a kwantar a tayar bai ma san a ina yake ba."
Sosai ta ki'dime tana fad'in." Maryam d'in Amina wane irin asiri ne wannan an ya kuwa babu sanya hannun magauta kin san fa ba zai rasa makiya na fili da boye ba don Allah ku daina amincewa da jita jita akan matar nan."
Murmushin takaici na yi tare da fad'in." Ba za ki gane ba ne ai anti Yagana kawai idan da hali ki zo sai ki ji komai ba sharri ake yi mata ba wallahi da gaske ne ga zahiri ya bayyana bayan rasuwarta."
A sanyaye ta ce." Zan zo in sha Allahu tunda jikin baba Sule babu dadi an ce yana kwance a asibiti sai na duba shi."
Na ce." Haka na ji a wajen Hajja ban sani ba wallahi yaushe za ki zo."
Ta ce." In sha Allahu cikin satin nan, zan dai kira ki."
Na ce." To shikkenan anti Yagana"
Sallama muka yi cike da yanayi na damuwa domin abin ya doke ta itama kwarai da gaske.
Wajajen daya da minti goma Sahura ta shigo ina d'aki a kwance na yi muryarta suna gaisawa da matan gida yara suna ta gaisheta sannan suka nuna mata d'akin da nake.
Ina kwance ban motsa ba ta shigo da k'aramar akwati a hannunta..
Na tashi zaune ina kallonta ta zo ta zauna kusa da ni hankalinta gabad'aya a kaina sai na ga ruwan hawaye ya ciko idonta ta ce." Amina ke ma jinyyar ki ka yi ne?"
A tak'aice na ce." Me ki ka gani ne?"
"Kin rame sosai wallahi kin yi wani iri?"
Ban ce komai ba na zuba mata ido ina kallonta ta goge hawayen da ya d'an zubo ta riko hannuna a sanyaye tana fad'in." Menene yake faruwa don Allah ina Yallabai din Amina na ji tsoron ganinki a hargitse cikin k'unci da damuwa."
Na yi ta ko'karin ganin na hana hawayen da yake dannowa zuba amma sai da ya fito ban goge ba na ce." Sahura ashe maganar nan da ki ka gaya mini farkon jin labarin auran Hajiya Maryam a wurin aikinku da gaske ne, ta asirce mini miji ta bi yaranmu daya bayan d'aya ta asirce ko na ce ta tsaface domin haka malamin ya fad'a tsafi take yi."
littafin nan na kudi ne Hajiya kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Ta gyad'a kanta cikin al'ajabi tana kallona sannu a hankali na shiga warware mata tun daga farkon lamarin har zuwa yanzu da za a kira da fad'an k'arshe tunda komai ya bayyana.
Ta jima shiru cikin tsananin tashin hankali da mamaki kafin ta ce." Anya matar nan mutum ce Amina wane irin zalinci ne wannan.
Mutum ta aure shi da iyalinsa da yaransa saboda tsabar mugunta da son zuciya.
Wallahi tunda labari ya fasu a wurin aiki nake ta jin ana magana akanta har na gaza ha'kuri na gaya miki amma kin san abinda hana a gazgata gaskiya ne ayyukan da take yi na alheri da suke a bayyane shine dalili da ya sanya da yawa wasu ba su yarda da wancan zargin ba.
Wai akan namiji Amina ki ga mace ta yarda ta mutu a matsayin 'yar wuta domin dai Hajiya Maryam babu abinda zai hana Ubangiji bai hukuntata ba idan an yi duba da irin ayyukan zalincin da ta gudanar a lokacin da take raye."
Na ce." K'warai kuwa Sahura a raina nake jin idan har mutumin nan bai tashi da lafiyarsa kamar da ba to har na koma ga mahallicina ba zan yafe mata ba zan ta yi mata addu'a har karshen numfashina.
Ta ce." Don kin yi hakan ba lefi ba ne Amina ta cuceku wallahi kuma ta cuce mu domin duka hanyar abincinmu tana ga Allah tana hannunsa babu abinda za mu yi masa sai dai addu'a Allah ya saka masa."
Hajara ta shigo da tire na silba jera da kwanukan abinci ta ajiye a gabanmu ta fita ta sake shigowa da ruwan pure water a leda ta dube ni tana fad'in." Hajiya ruwan da ki ka ce a dora miki ya yi har na kai miki bandaki."
Da kulawa sosai na ce to na gode kwarai Hajara Allah Ya yi miki albarka."
Ta juya ta fita da sauri.