Sashe 259
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hadiza na ga wautarta kwarai domin yanzu a k'alla da fitowarta daga gidan gyaran hali za a samu wata hudu to tun a lokacin ya kamata a ce ta sanar mini da abinda yake damunta domin neman magani ka'in da na'in.
Zubar ruwa da kumburin gaba abu ne mai tsanani watarana zata iya wayar gari da susa tunda shi infection din idan ba a yi sauri an tare shi ba girmama yake yi har wasu su d'auka ta dalilin da rashin kula.
Dama tun zuwanmu daki daban na ware mata a falon nan take kwana hakan ya sake yi mini amfani kywarai domin kuwa ina ganin da an yi had'akar toilet to wani zai iya d'auka wannan lamarin ba abin yin shiru ba ne kenan da wannan mas'alar ba ta zo ba haka za ta cigaba da zama da ciwo yana cin ta har sai ya zama babba irin wanda ake gudu.
Tabbas babu maganar aure a wannan yanayin da ake ciki tukkuna sai an magance matsalar idan ya so ko ma menene sai ya biyo baya babu amfanin gaggawa cikin kowane lamari kuma aure ba abin wasa ba ne idan har an yi shi to kowace mace tana bukatar zama a dakinta rayuwa ta din-din din ai abinda ya fi infection ma za a iya d'auko shi a wannan gida domin da ta biyewa mazan dake bibiyarta wata'kila da da cutar 'kanjamau za ta dawo tunda yanzu maza da yawa sun lalace da neman matan banza ba wai ma'aikatan gidan ba manyan mutane ma da suke yawo cikin manyan riguna da motoci na alfarma tare da wata suttura ta Allah amma sai ka same su a hotels tare da karuwai suna amfani da su kuma suna da iyali a gida har da yaransu.
Haka dai na kwana cikin tunani da nazari da safe ashe yana hankalce da ni yana ta shirin fita ya ce na fito masa da takalminsa sahu ciki dake ma'ajiyarsa na fito masa da shi din kamar yadda ya buk'ata ya fesa turare ko'ina na jikinsa ya zo ya zauna gefena a nutse ya fara sanyawa k'afafunsa safa sai da ya kammala tukkuna ya dube ni amma bai ce komai ya gyara zaman gilas dinsa ya furta." Akwai abinda yake damunki Giwa ashe mun kai matsayin da yanzu za ki dinga yi mini b'oye -b'oye, an yi wani abu ne a gidan?"
Na kalleshi cikin kame-kame na furta." Wallahi akan maganar Hadiza ne ba wai boye maka nake yi ba abin ne dai yake buk'atar nutsuwa kafin wanzuwarsa."
Ya nutsu sosai yana kallona." To ai babu dole Amina shi aure na mutum biyu ne don Allah idan ba ta so kada ki tursasatata ai ba yarinya ba ce ita tana da damar zabin namijin da ya yi daidai da rayuwarta shi da ya nemi auran nata zan gaya masa ya nemi wata."
Na gyad'a kaina a hankali na ce." Tana sonsa kuma tana son yin auran yadda ta nuna mini to amma kamar yadda ka ce babu munafurci a sha'ani irin wannan itama abinda ta duba kenan ta gaya mini tana da matsala tun fitowarta daga wancan gidan take ta fama da matsanancin infection."
Jim ya yi yana kallona kafin ya furta." Hakan ba zai hana a aureta ba tunda muna da asibitai da masu maganin gargajiya kowace cuta tana da maganinta don haka ku je asibiti tare ko kuma ku yi waya da Dr Sailuba duk abinda yake damunta a sanar da ita ni kuma na d'auki nauyi jinyyar in sha Allahu."
Na ce." Mun gode sosai Allah Ya saka da alheri, amma za mu fara yin na hausa ina da mai maganin Islamic masu kyau da inganci mafiakasari ina ji ana fad'in na Hausa ya fi kassara shi ya lalata tasirinsa har abada in sha Allahu za a yi dace Ina ganin idan har ta yi amfani da maganinta to duk wani nau'in sanyi za ta yi fitsarinsa."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." To hakan ya yi ki yi magana da ita din a jarraba Allah Ya sa a dace Amin."
Na ce." In sha Allahu zan yi magana da ita.
Ya mike yana duba agogonsa cikin zolaya ya furta." Ni ma a samo mini maganin karfi idan da akwai a Islamic din kwana biyu ba ki gan ni ba kuzari ba."
Ban san lokacin da na wurga masa harara ba, ya fashe da dariya yana fad'in.''Menene to Giwa idan na ce ki nemo mini maganin karfi waye ya fi amfana."
Na tashi ina d'an yin tsaki 'kasa-kasa saboda takaici na ma rasa abinda zan ce masa.
Ya riko ni sosai a jikinsa yana yi mini magana a kunne.
Da sauri na dube shi, wai maganar wata haihuwar yake yi mini yana son mai sunan Hajja Halimatussadiya.
A ganina idan na sake haihuwa da wannan shekarun kamar zan zama abin kallo yara na yi kai ma kana yi Kamalu da Yusi sun zama zagada zagadan samari.
Ya rike hannuna sosai muka kama hanyar fita daga d'akin yana cigaba da yi mini maganar samun ciki.
Wai ana samun mace mai sunan Hajja shikkenan Allah Ya sallame shi.
Shiru kawai na yi ban iya ce masa komai ba saboda gudun kada na fad'i abinda zuciyata take gaya mini ya zama lefi tunda shi tsakaninsa da Allah da kuma iya gaskiyarsa yake maganar Allah dai ya kyauta
Sai da na samu nutsuwa tukkuna da yamma na kira anti Yagana a waya muka gaisa sosai tare da tambayar bayan rabuwa ta ce mini Fadila nan tana ta shirye shiryen zuwa domin yi mini kwana biyu na ce ina sauraranta.
Daga nan na shiga gaya mata halin da ake ciki da farko ta dinga murna har tana kwarzanta d'abiu da kyawawan halin Sukairaju tunda ya zauna a gidanta shekarun baya da na je bikin babandi garin a lokacin da ya had'a ni da shi domin ya zame masa security lokacin da yake kan sharafin kishinsa.
Fadi take yi lallai Hadiza ta yi miji kwarai da gaske abin godiya ga Allah ne.
Ban katse ta ba sai da na bari ta gama murna da adduarta tukkuna na gaya mata matsalar da take damun Hadizan.
Jikinta ya yi sanyi sosai cikin kasala da sanyin murya ta furta." Har kin sanya jikina ya mutu Amina wannan matsalar ai babba ce kuma ba zai yiwu a rufe ta ba akan son ranmu amma tasan bata da lafiya mai yasa tun farkon dawowarta ba ta yi magana ba wannan ai rashin hankali ne, domin da ta yi m
agana tun farko da tuni yanzu an ci karfin magani.
Na ce." Ni ma abinda na ce kenan wallahi anti Yagana Hadiza fa sai da na yi da gaske sosai amma duk ta susuce wallahi idan tana yin wasu abubuwan sai ki dauka ta samu matsalar kwakwalwa."
Ta ce." Dole hakan na iya faruwa domin can inda ta zauna din wani darasi ta koyo mai zaman kansa gida ne da idan Allah ya sa mutum ya shiga a sa'a yake fitowa da raunin zuciya da jin tsoro tare da nadama.
Idan kuma mutum bai shiga a sa'a ba sai ki ga ya fito da bushewar zuciya tare da koyo wasu dabi'un marasa kyau wanda suka fi na da muni!
Mu dai godiyar da za mu yi wa Allah yadda ta fito da kyawawan halaye."
Na ce." Hakane yanzu dai mun yi magana da maigidan ya ce a nema mata magani ko na asibiti ko na hausa zai saya."
Ta ce." Ubangiji Allah Ya saka masa da alheri ki yi masa godiya sosai mun gode Allah Ya jikan mahaifa."
Na ce." In sha Allahu zan sanar masa bayan kwanaki biyu duk yadda ake ciki zan sanar dake in Allah Ya yarda."
Muna yin sallama na kira GARKUWAR MATA. ita ce mai maganin da na tabbatar da inganci da sahihancinsa duk eanda ya san ni da ita ya san ni domin kuwa tunda na fara amfani da magungu
anta ban kuma marmarin amfani da wani wanda ba na ta ba. 08089965176
Duk halin da Hadiza take ciki na gaya mata a take a lokacin ta ce sanyi ne amma bai riga ya girmama ba kuma idan har an dage da magani za ta rabu dashi.
Na ce ta had'a mini mai kyau ta aiko mini dashi har da set din kayan mata irin wanda nake saye.
Ta ba ni tabbacin za ta sanya a mota da sassafe.
Muka yi sallama cikin amince sannan na duba details dinta na tura mata kudi har da karin dubu goma akai ta kira ni tana yi mini godiya taga dubu goma ita kuma me nake buk'ata na ce ta sayawa yara sweet domin yadda nake jin dad'in magungu
anta sai nake ganin babu abinda zan bata wanda zan biyata.
To wata'kila shi ma da abin ya yini duk da ba girkina ba ne da daddare da ya shigo yi mini sallama sai da ya sake tuntubata ya muka yi da mai magani har yana gaya mini anti Yagana ta kira shi a waya tana yi masa godiya.
Na ce eh na gaya mata halin da ake ciki ne, mai magani kuma mun gama magana da ita ya ce nawa ne kudin.
Shiru na yi ban iya bashi amsa ba sai nake ganin da kunya ace na bari ya biya tunda ina da halin biya shima ya san haka yau da asibiti ne babu yadda zan yi tunda likitocin da suke duba mu shi yake sallamarsu.