Sashe 221
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk tsayin rayuwar da muke yi ban ta'ba ganinsa yana tu'ka mota ba sai yau duk da yake ya ce tafiyar sirri ce har da sanya takunkumi da rufe hancinsa da bakinsa da (fecemark)
Haka muka isa asibitin Malam Aminu Kano yana ta yi mini zantukan marasa dadin saurare tunda duka akan auran da zai daura gobe ne ni Ina nake da wata shawara da zan bashi a ce sai da asiki ya zo gaban goshi tukkuna zai yi gwajin jinin ya so wata matsala ta faru idan ba su samu haduwar jini ba fadi yake yi akwai matsala domin dai shi ba zai iya gayawa malam 'Daha ya fasa ba saboda wannan dalili zai bari a d'aura auran amma fa zai bar yarinyar a gidansu kafin ya yankewa kansa hukunci.
Jin haka ya sanya jikina yin sanyi tabbas wannan son rai ne tsagowaronsa babu yadda za a yi na yarda ya lalatawa yarinya kuruciya wane irin wulakanci ne wannan gwara duk yadda za a yi a yau din idan results bai daidaita ba a zauna zama na mussaman da muhukunta domin su fayyacewa Malam D'aha illar hakan.
Yana had'a ni da likitan da zai duba ni ya yi mini sallama a ka yi sa'a cikin asibitin in banda likitan babu wanda ya fahimci shine tunda motar da muke ciki babu tambarinsa kamar sauran motocinsa na zurga-zurga wanda suke tabbatar da zuwansa waje idan an gan su a ajiye.
Scanning ya ba ni naje na yi da result ya fito ya gama dubawa ya dinga washe baki yana fad'in." Hajiya wannan albishirin ni ya kamata na yi wa Yallabai please a yi mini wannan." Na yi murmushi ina fad'in." To shikkenan duk da bai gaya
mini abinda sakamako ya nuna ba a jikina na ji cewa tagwaye zan sake haifa domin yanayin wannan cikin yanayin cikinsu Hassana sai dai wannan din da d'an bambanci kad'an.
Na ji yana fad'in." Yara maza ne biyu yadda sakamako ya nuna dukkaninsu cikin koshin lafiya sun kuma juya yadda ake so nan da sati hud'u sai ki sake zuwa a yi miki awo domin mu sake tabbatar da yanayin kwanciyarsu.
Cikin zuciyata na kira sunan Allah tare da yin godiya a gare shi.
Na ce." In sha Allahu Dr na gade sosai.
Muka fito dare da Minal da takardar result din a hannuna sai sannan na sanyata a jakata can na hangi Magaji zaune a gindin wata bishiya ya taso da sauri ya karaso tare da risinawa yana gaishe ni na amsa da kulawa ya kama hannun Minal muka nufi inda ya ajiye motar a tare.
Hajja ta ji dadin ganinmu su biyu kacal a falo ita da Kamalu suna hira yana 'bare ta mata lemo zaki.
Ta dinga washe bakinta ganina da Minal tana cewa." Ke yaushe aka kawo ki ne k'awata."
Minal ta no'ke kafad'arta ta'ki zuwa wajanta ta tsaya kusa da ni tare da dafa cinyata.
Na gyara zamana a hankali cikin kulawa na gaisheta ta amsa tana ta yi mini maraba.
Na dubi Kamalu lokacin da yake gaishe ni girma ya yi mini a ido kwarai ya sake yin fad'i da 'barage mazantaka dai ta bayyana tunda dama tuntuni muryarsa ta fashe an balaga ga wani gemu zororo a ha'barsa.
Cikin zuciyata na ce yaron nan dai ya rantse sai ya zama d'an izala
Gashi makarantar da ya yi ta almajiranci ba ni tsammanin ta 'yan alhalissuna ce.
Kawai dai abinda ransa ya fi ra'ayi kenan yaro ya nutsu sosai cike da wata iriyar kammala ta mussaman zahirin kammaninsa da mahaifinsa ta fito 'baro-'baro bambamcinsu kawai shi Yaya Aminu ba shi da gemu kuma bashi da kuzarin yaron amma duk wanda ya ga Kamalu a yanzu zai tabbatar da cewa hoton ubansa ne
Hajja ta fad'i take daga Ina kuke cikin wannan rana ta k'arfe d'aya Amina."
Na ce." Wallahi Hajja daga asibiti nake shine na ce bari na biyo mu gaisa kawarki mata ta gaishe ki."
Ta sanya dariya tana jan hannun yarinyar tana sake no'kewa a jikina.
Ta ce." Ina fatan dai lafiya ko Amina sannunki da ibada Ubangiji Allah Ya raba ku lafiya."
Na ce." Amin ya rabbi Hajja lafiya lau wallahi abinda sakamako ya nuna kenan.
Ta dinga fad'in." Alhamdulillahi cike da godiyar da Allah da jin dadi kafin ta shiga kwalawa iyami kira mai aikinta wai ta kawo mana ruwa."
Kamalu ya ce." Hajja ni me nake yi bari na kawo mata da kaina.
Ya ajiye lemon zaki da yake hannunsa ya nufi kicin da sauri lokacin Hajja ta d'auki lemon da ya gama 'barewa tana mikawa yarinyar da fad'in." Zo ki kar'ba to tunda kin 'ki zuwa mu gaisa."
kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Ta kuwa tafi za ta kar'bo lemon saboda rashin kunya gabad'aya muka fashe da dariya.
Ta ce." Yusi ai yau tun safe ya fita kasuwa da yake ya ce bashi da karatu yau shine ya yi sammakon fita amma nan da biyar da rabi za ki gan shi ya dawo."
Na ce." Ya zama sarkin kasuwa ai."
Tana dariya ta ce." Haka ake son namiji ya kasance ai."
Kamalu ya ajiye mini ruwa da lemo masu sanyi a gabana.
Na dube shi ina fad'in." Baka da hankali wanene zai sha wannan ruwan da wannan sanyin."
Yana murmushi ya ce." Mama ai na ga ana rana ne sosai ruwan sanyi zai fi kashe miki ishi."
Na ce"D'auke ka kawo mini mara sanyi."
Da sauri ya yi yadda na ce din ya kawo mini ya bude ya tsiyaya mini a Kofi.
Na d'auka na sha na bawa Minal Tasha na ajiye kofin saman plate din da ya kawo ruwan..
Hajja ta ce me za a sanya Iyami ta dafa muku Amina ni dai ce mata na yi ta saka mini danwake."
Na ce." Aikuwa a yi dani Hajja har na yi sha'awarsa.
Tana dariya ta shiga k'walawa iyami kira ta fito ganina ya sanya ta risinawa tana gaishe ni na amsa mata da kulawa Hajja ta ce da ita ta kara garin danwaken ta saka shi da d'an dama.
Ta amsa cike da bin umarni ta koma bakin aikinta.
Kamalu ya shiga dakinsu tsayin minti goma ya fito da wasu littafai a hannunsa gabad'aya muka bi shi da ido Hajja ta ce." Makarantar za ka tafi da wuri haka?"
Ya ce." E, Hajja amma kafin nan zan biya gidan Gwaggo."
Ta ce." Yawwa gwara da ka tuna mini shiga kicin ka ce da iyami ta baka garin danwaken nan leda biyar sai ka tafi mata da shi."
Ya ce." To shikkenan.
Ta dube ni tana cewa." Abu ne na marmari duk ranar da ta yi sha'awa sai ta tsumbula.
Na yi shiru ina murmushi gefe guda kuma ina kara kambaba mutunci da halin dattako irin nata ga kyauta ga kirki Hajja mutuniyar kirki ce sosai Gwaggo ta zama 'kawarta kuma aminiyarta.
Na tsinkayi maganarta tana fad'in." Ai ya sanar da ku d'aurin auransa gobe ne a Bunkure ko."
Na ce." Eh ya gaya mana Hajja Allah Ya sanya alheri."
Ta amsa da Amin.
Kamalu ya fito da ledar garin danwaken a hannunsa yana yi mana sallama tare da ce mini zai zo cikin satin nan in sha Allah.
Ta dube ni cikin nutsuwa kafin ta furta." Amina Malam D'aha mutumin kirki ne kwarai da aniya kuma mutumin maigidana ne tare na san su abokai ne kuma masu rufawa juna asiri ta kowace siga.
Lokacin da Tajo yake gaya mini kyautar auren 'diya da Malam 'Daha ya ba shi na yi farinciki domin sanin da na yi cewa gidan karamci ne da ilimi da addini gidan yi wa al'kur'ani hidima tabbas had'a iri da jinin Malam D'aha abin alfahari ne tare da fatan samun zuri'a nagartattu.
Sai dai kuma jikina ya yi sanyi sosai lokacin da ya nuna mini hoton yarinyar na ganta 'yar karama nama sheda fuskarta tunda itace ta dinga dawainiyar kawo mana abinci a lokacin da Tajo ya kwanta ciwo a gidan.
A mizani na tunanina yarinyar ba tsarar auransa ba ce domin ya yi mata nisa sosai babu hadi gabad'aya babu dacewa.
Amma a mizani na shari'a hakan ba haramun ba ne domin manzon Allah s.a.w shi ma ya yi irin wannan aure ya raini Nana Aisha har ta kai munzali kafin ya fara rayuwar aure da ita.
Malam D'aha Tajo ya yi niyyar bawa d'iyarsa kuma na tabbatar da cewa da zuciya daya ya kulla wannan al'amarin ba don samun abin duniya ba na sanshi sosai a can baya abin duniya bai dame shi ba mutum ne mai dattako da sanin ya kamata."
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zucciya.
Ni kuwa cikin raina ina fad'in anan dai bai san ya kamata ba Hajja tunda har ya iya bawa dattijo yarinya karama irin wannan ai zamanin annabawa daban da wanda muke ciki yanzu.
Ta cigaba da cewa." Na bashi goyon baya akan ya kar'bi kyautar da aka yi masa da kyakykyawar zuciya ku yi hakuri, ku kara akan wanda kuke yi in sha Allahu rabbi ba za ku samu matsala da yarinyar ba.
Itama Hauwa zan kira ta a waya domin na kara tausar zuciyata dama itace fitinanniya ku yi hakuri ku kawar da kan ku na dan wani lokaci komai zai wuce."
Na ce." Wallahi babu komai Hajja ai yarinyar bata da matsala zamu zauna lafiya da juna kuma na yi miki alkawari ba za a samu matsala ta wajena ba."
Godiya da sanya albarka har sai da na ji nauyi da kunya na ce ta daina gode mini domin ban yi abinda ya kai ta yi mini irin wannan godiyar ba a ganina ni ce zan yi mata godiya bisa ayyukan alheran da take yi wa a alhalina.
Biyar daidai na fito da niyyar tafiya har lokacin Yusi bai dawo ba fadi take yi zai ji takaici kuwa idan ya dawo ya ji labarin kin zo.
Na ce." Kawai sai ya zo gida ya same ni Hajja ba zan zauna jiran dawowarsa ba zan yi abinci idan na koma."
Muka yi sallama cikin girmama juna da mutuntawa Magaji direbanta ya d'auke ni a mota har gidana.