Sashe 211
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Minal ta zo tana le'ka kanta cikin ledar "Mama menene?'' tana fad'a tana k'ara zura kanta ciki.
Na ce" Zo mu je kicin a wanke kayan dadi ne."
Ta kuwa biyo ni da saurinta twins suna zaune da wayarsa a hannunsa game ya kamo musu.
Na cire ledar alawar madarar na jika musu gorubar domin ba za su iya cinta a bushe ba.
Abu ne da ba su saba dashi ba sosai sai ya zame musu kamar nama.
Yalo da d'ata da kad'anya duka na gyara musu suka kewaye ni muna ci Hauwa ta ce ba ta yi sha'awa ba wanda na tabbatar da cewa ta fadi hakane kawai saboda zuciyata tana yi mata zafi babu wata maccan da ko babu uzuri na juna biyu ta ce bata marmarin irin wad'annan kayan gonar.
Ganin yadda muke ci da yaran ya ce shi ma a bashi daya.
Usai ta d'auki yalo 'kato ta kai masa.
Ta d'auki wani ta tafi wajan Hauwa tana mika mata.
Ta kar'ba amma sai ta ajiye shi saman cinyata ta yi shiru duk ta yi sanyi abin gwanin ban haushi da tausayi domin dai Hauwa ko kana jin tausayinta idan ta kuntuka maka wani takaicin sai ka ji kamar ka rufe ta da duka saboda haushi.....
Daga karshe ma sai kawai ta tashi ta shiga d'akinta ina hankalce da shi bai bita da kallo ba balle ya shiga damuwa don ta bar wajen.
Ta gama kwanaki biyunta ban san wainar da suke toyawa ba.
Na kar'bi girki na kasance cikin walwala da farinciki kamar yadda shima ya kasance duk wata hanyar da zata kara mini mutunci da soyayya ita nake bi a yanzu muddin bai shigo mini da son zuciya ba kalau muke zaune a yanzu kuma idan zai nemi ni sau nawa ba na nuna gajiyawata jikina ya horu kwarai da dabi'arsa sai aka yi katari da wannan cikin da nake d'auke shi ba mai k'yamatar lamarin ba ne.
Na kwana biyu ban ji daga Sahura ba ina jin tun bayan wayar da muka yi take gaya mini Idiris ya buge kwado ya shiga gidanta babu yawunta sau biyu muka kara yin waya kuma idan na soko mata da maganar abinda yake faruwa a tsakaninsu ba ta saurarata fadi take yi ta daina gaya mini matsalarta tunda ni ma goyon bayansa na ke yi.
Katsam yau ta kira ni tana gaya mini tana zargin fa auran da Idiris ya k'ara ya gurgud'e.
Na tambayeta dalili ta ce mini kullum a gidanta yake kwana tsayin sati uku kenan kuma neman shiri yake yi da ita.
Jikina ya yi sanyi sosai Idiris bai shirya ri'ke musu yarinya ba ya aura aure duka bai fi wata hud'u ba an fara cin karo da matsala.
Ta ce mini ai tana zargin ma yarinyar tana da juna biyu ta ji Yayarsu wato uwar mijin Yusura tana fad'a a wata had'uwa da suka yi a gidan sunan k'aninsu amma dai ba su fito sun fad'a mata cewa sun rabu ba ta ji dai suna fad'in saura amaryar Idiris a jerin masu haihuwa domin itama ciki ne da ita.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*142*
Na cika da mamaki 'kwarai da gaske da jin wannan lamari
ni babban takaicina ma yadda yake ko'karin mayar musu da yarinya k'aramar bazawara tunda a yadda take ba ni labari duka bata fi shekara ashirin ba idan hakane kuwa ai da kadan ta girmi Yusura. shari'ar aure ba a yanke ta kai tsaye amma jikina yana ba ni cewa matsalar daga wajansa take wanda itama Sahura take zargin hakan domin ta ce har yanzu ya'ki yi mata bayanin komai sai kame-kame ya yi da kuma neman shiri da ita to kuwa duk yadda ya kai ga b'oyewa dole watarana kowa ya ji dalili mussaman a nasa b'angaran tunda har tana da juna biyu Allah kyauta ya kuma rufa asiri shine kawai abinda za a ce.
Kwana bakwai da dawowarsa guda yake gaya mini na shirya satin da za mu shiga juma'a kenan za mu je jigawa d'aurin auran Alhaji Sulaiman mijinsu Hajiya Aziza.
Idan an daura za mu kwana d'aya sai mu dawo gida.
Na ce masa to shikkenan, cikin zuciyata ina ta mamaki ashe auran da na ji kwanaki yana fad'a da gaske ne.
Kuma wata'kila budurwar zai aura lallai tsufa ya yi gardama an kuma shigo da son zuciya iyayen yara da su kansu masu auran yara k'ananu.
To Ashe tana jika a cikin gidana ni ma.
Ni dai bayan dawowarmu daga d'aurin auran Alhaji Sulaiman kamar yadda ya fad'a sai nake ganinsa wani sukuku babu irin sa'ke-sa'ken da zuciyata ba ta yi mini ba akan ganin ya canza na d'an ta'kin lokaci.
Zuciyata na kawo mini ko shima ya yi sha'awar budurci ne tunda mafiakasarinsu abinda sukewa kulafuci kenan ya sanya suke ture kunya da kawaici su auro 'ya'yan cikinsu su kwanta gado daya da su.
Na zura masa ido kawai yanayin yadda ya fara tafiyar da al'amuransa na rashin walwala da yin shiru da nazari ni ma sai na tsiri yin hakan muka cigaba da tafiya a haka bai gaya mini damuwarsa ba ni ma ban nemi da na ji ba.
A d'ayan biyu ne ko matsalar kasuwanci ko kuma shi ma auran yake nema amma kuma yana cike da zullumi da damuwa ga yawan kallona da yake yi daga zarar mun had'a ido sai ya wayance ya tsiri yin wani abin.
Yanayin da ya 'kir'kirarwa kansa bai hana shi yin mu'amula da ni a duk lokacin kwanan aurena ba.
Hauwa dai har yanzu jiya iyau domin ga dukkanin alamu cutar damuwa(Depression )ddaf take da ta kamata abin gwanin ban tausayi da takaici.
Ana haka Sahura ta kira ni take gaya mini Idiris suna kotu da amarya iyayanta sun buk'aci ya saketa ya ce sai an biya shi abinda ya kashe kafin auranta.
Alkali da ya nemi jin dalili kaf aka gaya masa.
Duk wata hidima ta gida ya gaza sai masifar kwanciya da yake yi da yarinyar mutane babu dare babu rana ga rashin k'oshi tunda ya yi na amarci ya jingine k'aramin buhun shinkafa da rabin kwalin taliya da makaroni da kwalbar manja da mangyad'a da had'in maggi.
Da suka 'kare sai ya shiga auno mata wake yace ta dinga yi fate-fate yana 'kara jini tunda tana da juna biyu sai ta fi sati daya tana cin wake fate ko 'kulu da mai da yaji da safe ya sayo mata kunnu da awara.
Yadda yarinyar take fad'a tana kuka sai ya shigo da leda cike da abin dadi ya zauna ya ci a gabanta ya bar ta da tsotse 'kashin da ya sale masa tsoka.
Ya kuma isheta da bala'in kwanciya da daddare ga rashin abinci mai kyau.
Da ta ce ta gaji da cin wake sai ya auno mata tsakin masara mai yawa da barkono da farin maggi da manja wai ta dinga yin d'anmalale.
Yarinya mai garin jiki duk ta tsotse gashi baya dawowa da wuri sai sha biyu na dare wataran har da rabi tukkuna zai sanya mukkuli ya bud'eta tunda idan zai fita kulleta yake yi ta ciki
yau da gobe ta'ki wasa har dai iyayenta suka gane wuya yake bata yaran shago ma suka bada shedar kulleta yake yi kuma wataran akan idonsu yake dawowa tunda suma suna kaiwa sha biyu na dare ba su tashi daga aiki ba.
Sosai na tausayawa yarinyar.
Ita kuma Sahura sai na lura kamar murna take yi tana fad'in hakkinta ne domin duk auran da aka gina shi akan zalinci da kwadayi k'arshensa kenan wallahi ba zata rike masa d'an ko wace shegiya ba.
Na ce." Ke abinda yake damunki kenan ko Sahura an ce mijinki yana raba dare a waje shi ba wani business yake yi ba na cin kasuwar dare ba balle a ce ba ki yi tunanin wani abu ba?"
Ta ce." Ba zai wuce yana yawon neman mata da d'an kudin da ya samu ba, ai ki bar d'an iskan namiji Amina kin ga ni ban ci ba haka zalika yarinyar mutane ma da ya auro bata ci ba ya tafi yana kaiwa matan banza shiyasa tunda ya yi auran nan kamar na sani ban sake ba shi kaina ba."
Na ce." Lallai akwai buk'atar ki sanya ido akan Idiris Sahura kada kishi ya sanya nan gaba ki yi nadama idan ya kasance Idiris ya fad'a harkar bariki kina da kamasho tunda ke kin San wanene shi gashi kina ba ni labarin irin durzar da yake wa yarinyar mutane yanzu da babu ita ai zai sake tsunduma tunda ke kin daina ba shi kanki.
Haihuwar da ta ratsa tsakaninku ta wuce komai."
Ta ce." Haka kowa yake cewa Amina amma bari kiji wallahi yadda Idiris ya cire kawaici a kaina ya gwada mini rashin Imani babu wani dalili da zai sanya ni don ya shiga matsala a yanzu na damu.
Na gaya miki fa yanzu ko ya sake ni ba ni da damuwa Allah ya yi mini rufin asiri ina da matsuguni da 'yan kudi a asusuna zawarci zan buga mai kasafiti Hajiya."
Dariya ta kama ni na ce." Sahura ki dai yi tunani akan maganata ki yi hakuri ku samu daidaito don Allah ko saboda yaranmu babu dad'i Idiris ya lalace dole za a danganshi dake ace tsohon mijinki ne kuma uban yaranki.
Ta furta." Ai ko zamu daidaita ba dai yanzu ba Amina wallahi yadda ya gumami ni ba'kinciki in sha Allahu masifar da zai tsinci kansa sai ta shige wadda ya jefa ni."
Da haka muka yi sallama tunda duk ta inda na biyo sai ta doje ta nuna yanzu ba lokacin da ya dace a ce ta tausaya masa ba ne.
A daran ranar da muka yi wannan tattaunwar da Sahura bayan isha'i muna falon gabad'aya masu aiki da yaran ban da Hauwa da yake girkinta ne tana ta kai wa da kawowa daga kasa zuwa sama.
Na ce da Baba Tabawa ta kawo mini abinci.
Towon shinkafa suka yi miyar taushe da tantakwashi.