Sashe 223
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su zo na ji dadin hakan na kwashi yarana cikin sau'ki komawa kuma sai dai ya koma da ita da yaranta amma ni mun dawo nan gabad'aya a nema musu wata makarantar.
Ganin na yi shiru ban ce masa komai ba sai hankalinsa ya sake kwanciya domin ya d'auka na yarda.
Jallop din taliyar da na yi tsammanin ba zai ci da yawa ba wadda na rage masa kaf ya cinyata ya sha ruwan da lemo yana gaya mini tun tea din da muka sha tare a d'akina bai kara cin komai ba.
Abinda ya faru kenan da assuba yana dawowa daga sallah ya fara kimtsawa na yi ko'karin gama abin kari da wuri domin ya karya kafin ya tafi.
Gabad'aya duka a dame yake haka dai ya zauna yana karyawa yana gaya mini jikinsa gabad'aya a mace yake domin baya tsammanin Malam D'aha zai amince da duk wani bayanin da za a yi masa.
Na ce." Ka yi ta addu'a Allah Ya zab'a maka abinda ya fi alhari kawai idan har ya amince na gaya maka ka sanar da ni zan nemawa wani auranta ."
Ya amsa mini da to shikkenan.
A gabana ya kira likitan ya yi masa bayani sosai yadda zai tsara malamin duk da aikinsa ne wayar da kan jama'a akan mas'aloli masu yawa a matsayinsa na likita amma dai ya kara tunasar dashi cewa wajan wanda za su je babban malami ne kuma mai tsauri wanda boko bata ratsa shi ba sai tsantsar tauhidi da kadaita Allah ."
Ya kira Hauwa ta ce sun taso tun wajen shida yanzu kuma k'arfe shida da rabi kenan sun yi minti talatin akan hanya.
Har mun yi sallama zai tafi ya dawo yana tambaya wai sai na gaya masa wanda zan nemawa auran idan dashi bai yi yuwa ba.
Na ce." Me kake ci na baka na zuba, za ka san shi in sha Allah."
Sai kawai ya girgiza kansa babu kuzari ya furta." Sai na dawo." Ya fice da sauri Minal tana fad'in." Baba sai ka dawo."
Ya daga mata hannu ba tare da ya amsa ba ya fita.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*150*
Na sake sauke ajiyar zuciyar da ba zan iya lissafa adadinta ba.
Hannun yarinyar na ja muka nufi d'aki ina mamakin sha'anin Hauwa ni yanzu ma ta daina ba ni haushi da mamaki dariya take ba ni wallahi.
Gefan gado na zauna kafafuna na dan rawa haka kawai nake jin faduwar gaba da fargaba akan wannan sha'aninan wani sashe na zuciyata na gaya mini bai zama lallai malamin ya yarda da duk wani nau'in bayani da za a yi masa ba akan wannan lalura.
Wanda na gama fahimtar cewa abinda shima ya assasawa maigidan gigita kenan da damuwa da kuma rashin nutsuwa.
A nasa tunanin idan malamin ya kafe akan ra'ayinsa sai kawai ya bari a d'aura auran wanda hakan ba ita mafita ba tunda da wani kudiri a ransa da kuma abinda ya niyyata akan yarinyar wanda yake nuna tsantsar son zuciya da rashin tausayawa kuruciya.
Malam D'aha Malami ne kuma mutumin da ne kuma mutumin karkara wanda ba shi da wayewa da ilimin zamani na boko abu ne mai wahala duk bayanin da za a yi masa akan illar ciwon ya amince da cewa ba kutse aka yi wa shariar Ubangiji ba gashi dai bincike domin samun mafita ya sanya har manyan likitoci da shugabanni suka kafa dokar yin gwajin jini kafin k'ulla rayuwar auratayya ta din-din don samun sahihan yara masu wadatacciyar lafiya.
Jikina a mace na dauki wayata dake saman dirowar gefan gadona
babu wanda na yi wa sha'awar auran yarinyar Hajara sai Usaini.
Yaro ne nutsatstse mai kuma zuciya tun yana yaro ba shi da matsala har zuwa yanzu da ya kai munzalin girma.
To sai dai kuma hanzari ba gudu ba anan shine duk da bai zama dole ba wata'kila Usaini yana iya zama As tunda ni ma itace mun had'a uba uwa kowa da tasa.
Na ji daga bakin mutane da dama cewa yana iya canzawa a wasu lukutan amma zuciyata ba ta gazgata hakan ba a ganina idan har sakamako na farko ya nuna matsayin jini da wahala ya sake canzawa.
Can kasan zuciya na ji tana gaya mini cewa babu lallai Usaini ya kasance As don kin kasance Amina.
Wannan hasashen na zuciyata ya kara sanya mini kwarin gwiwa sosai
Har indai k'addara ta raba auran da za a daura shi a yau kuma za su ba mu yarinyar zan yi farinciki da hakan domin kuwa duk inda ake neman nutsuwa da tarbiya yarinyar ta kai daidai gwargwado kuma ta yi sa'a da auransa tunda shi ma bai wuce ashirin da takwas ba.
Bugun farko ya daga na ji shi cikin kasuwa da hayaniya a wajen da yake.
Sama-sama nake jin maganarsa na ce." Har ka fita kasuwa Usaini k'arfe nawa yanzu.
Yana dariya ya furta." Takwas saura anti akwai ba'kin da muka yi daga nijar sun yi sayayya jiya mun had'a musu kayan ba su samu damar d'auka ba sai yau da sassafe suka yi mini waya yanzu na shiga kasuwar ma anti."
Na ce." Allah Ya taimaka idan ka sallame su kazo gidana na sharad'a na zo garin yau kusan sati daya kenan akwai maganar da za mu tattauna."
Ya furta." Ba na son rufe shago anti afuwaa zan iya jira Hamusu ya zo tunda sai tara da rabi yake zuwa kasuwar."
Na ce." Babu matsala ka jira shi idan ya zo sai ka taho ina sauraranka."
Sallama muka yi na kashe wayar na ajiye zuciyata na yi mini wani nazari.
Kada fa Ummansu ta bijire akan wannan yun'kuri nasan ba ni da matsala da yaron haka zalika ba ni da matsala da Babanmu Ummansu Saminu itace birkitacciya dama tana jin haushi tana ganin duk sabgata idan ta tashi ba a gayyatarta gidana na abuja bata ta'ba zuwa ba Ummansu Hadiza ce ta je sau biyu ta jima tana yi wa anti Yagana wannan korafin tana gaya mata ita ba mu d'auketa a matsayin uwa ba duk hidimarmu idan ta tashi sai mu nemi Ummansu Hadiza kuma abin ba haka ba ne Ummansu Hadiza ta fita shishshigi ita kuma duk abinda zai faru sai ta ce lallai sai an gaya mata ba idan ba mu sanar da ita ba sai ta k'ullaci abin a cikin ranta.
Itace damuwata kawai tunda d'anta ita take da iko da abinta idan ta ce bata yarda ba babu yadda zan yi dole na ha'kura amma zahiri na yi wa yaron sha'awar yarinyar.
Na nemi lambar anti Yagana ta katse ba ta daga ba ina sake kira kuwa ta daga muka gaisa ta ce." Ya ake ciki Amina Ina fatan babu matsala rashin sukuni ya hana ni kiran ki na ji ya ake ciki."
Na ce." Alhamdulillahi babu matsala ina ganin zan ci nasara akan abinda nake so in sha Allahu dama dalilin da ya sanya na kira ki wata shawara nake so mu yi shin ya ki ka ga ni?"
Duka na kwashe abinda yake faruwa na gaya mata.
Ta ce." To ai wannan ba matsala ba ce Amina alheri fa ki ke niyyar k'ullawa ban ga dalilin da zai sanya mahaifiyarsa ta nuna rashin amincewarta akan hakan ba ke din Yar uwasa ce kuma ba za ki had'a shi aure da yarinyar da ba ki tabbatar da tarbiyarta ba.
Bayan dangantaka ta jini ke uwar dakinsa ce a karkashinki yake idan tana da kunya ai ba zata kalubance ki ba."
Na ce." Hakane anti Yagana amma a cire maganar uwar d'akin nan na dai zauna a matsayina na 'yar uwarsa dalili anan shine ba ni so shi da mahaifiyarsa suga don yana karkashina zan juya masa rayuwa a yanzu ma idan ya zo zan fara tambayarsa shin yana da budurwa tsayayyiya idan ya ce bashi da ita sai na gaya masa shirina.
Ina da tabbacin ba zai bijire mini ba."
Ta ce." Misali na yi miki ai idan ta yi tsalle ta nuna d'anta sai a nuna mata ke kuma uwar dakinsa ce a kasuwa sanadinki har yake saya mata atama super ta daura ta yafa mayafi mai tsada ."
Dariya ta kama ni ina fad'in." Anti Yagana kenan, to kin ji dama dalilin da ya sanya nace bari na gaya miki kafin na yanke hukunci Babanmu bashi da matsala hakan zai yi masa dad'i."
Ta ce." Ni ma na baki goyon baya amma kafin nan ki fara tambayarsa genotype dinsa da blood group idan ya sani shikkenan idan kuma bai san matsayin jininsa ba sai ya yi maza yaje a yi masa
Na ce." To shikkenan haka za a yi in sha Allahu anti Yagana a gaishe mini da masu jegon."
Ta ce." Gasu nan suna bacci gabad'aya tunda aka yi wankan safe suka kwanta." Na yi dariya ina fad'in." Fadila manya a shafa mini kan Shahida." Sunan anti Yagana aka sanyawa yarinyar sai uwar tace tana so a dinga kiranta da Shahida a lokacin da ta fad'i hakan na ce wata shekarar sai ki haifo Shahid.
Kunya kuwa ta kamata na ce to idan ba rashin kunya ba duk muna zaune ita zata za'bawa 'yarta suna ai ta yi kara ta bari a samu sunan da za a dinga kiran yarinyar tunda ai dole a sakaye dalilin sunan uwarta ne.
Goma da sha biyu ya kira ni a waya ya shigo gate amma maigadi ya hana shi shigowa.
Na sanya hijabina na fita harbar gidan suna daga can bakin gate har da Ayuba direba.
Ganin fitowata ya sanya ya kafe babur dinsa Yana kallon Ayuba yake cewa." Idan shi zai ce bai gane ni ba ai kai za ka sheda fuskata ko ba kai ba ne direban da ka dinga zurga-zurgar kai su asibiti a lokacin da Babanmu ya kwana rashin lafiya."
Ayuba ya dinga fad'in." Tabbas ni ne yanzu na sheda fuskarka ka yi hakuri wallahi d'ayan muka fi ganewa." Yana nufin Hamusu.