← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 265 OF 276

Sashe 265

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu buk'atar godiyarki ko zubar hawaye ina so ni ma na shiga cikin ladan da kike samu don haka don na sanya miki hannu cikin lamarinki kaina na yi wa taimako babu wanda ya san gawar fari sai Allah ko bayan babu raina ina da tabbacin yarana kaf da naki da ba naki ba ba za su wulakanta ba.''
Hannuna na sanya na sar'kafo wuyansa ina kuka sosai wanda yake fitowa daga can karkashin zuciyata.

Ya d'ora hannuwansa biyu a gadon bayana yana d'an bubbugawa kafin ya dago fuskata muka dubi juna da wani irin murmushi a fuskarsa ya furta." Kukan sam bai yi miki kyau ba giwa na hango muninki." Ya sanya yatsu yana ta'be mini hanci da kumatu haka dai na dinga daurewa ina cire hannunsa yana mayarwa dole dai sai da ya sanya ni dariya ya cika mini kumatu yana fad'in ." To ko kefa kuka ko mutuwa na yi kada ki yi mini kuka domin abin sai ya zai zame mini biyu na tafi na barki wata'kila shekaru kad'an ki manta da ni wasu mazan su fara zawarcinki."
Na ce." Don Allah wace irin magana ce wannan ka daina ba ni son jinta."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Gaskiya ne ai Amina idan na rasu mazan zamanin nan ba za su iya d'auke ido a kan ki ba."
"Idan ka riga ni rasuwa babu yadda zan yi ba kuma zan kalubalanci Ubangiji ba domin ni ma ita nake jira amma ka sani wallahi ko shugaban kasa ne zai fito neman aurena ba zan aure shi ba na gama aure har abada zan zo na riskeka a aljanna mu cigaba da rayuwa."
Yana dariya sosai ya ce."Shugaban kasa fa Amina?' Na tare shi da saurin gaske ina cewa." Ko da sarki ne wallahi ai na gama yin rashin mijin da babu wanda ya isa ya maye mini gurbinsa to me nake nema a duniya komai ka yi mini fa."
Fuskarsa ta yawalta da wani 'kasaitancen murmushi yana ta 'kan'kance idonsa a tsakiyar nawa idon dad'in kalamaina sun sanya shi cikin wani irin shau'ki ya rasa ma abinda zai ce mini duk bakinsa da iya maganarsa na kashe shi a zaune sai murmushi.

Na cigaba da cewa." Kamar yadda ka kawo shawara hakan za a yi Plaza ta cigaba da amsa sunanta na (GIWA PLAZA) Shops din kuma AminatuAminu na amince da hakan na kuma gode bisa wannan kara da ka yi mini Ubangiji Allah Ya bar mu tare."
Ya rike hannuna na dama ya had'e yatsun waje d'aya ya d'amke sosai." Za a yi hakan in sha Allahu amma sauran shagunan ai ba ki da hurumi tunda hayarsu za ki bayar dole masu kar'ba sune suke da zabin abinda za su sayar a ciki kin gane abinda nake nufi ko?"
Na gyad'a kaina a nutse na ce.'' Na gane ni dai wurina sunansa GIWA PLAZA saboda suna ne na mussaman da babylove ya sanya mini kuma ina alfahari da sunan ya fito daga bakinsa."
Ya sa dariya har sai da duka hakoransa suka bayyana." Me yasa ba ki ta'ba nuna mini sunan na yi miki dadi ba uhumm?"
Ina murmushi na ce." Wallahi da gaske sunan dadi yake yi mini har wani tunkaho nake yi fa?"
littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Aikuwa dadi ya ishe shi ya kwanta saman gado yana ta dariya sai kace wani shashasha ni ma ina ta ya shi yau na gama kashe masa karsashin jiki da 'yan kalaman da ba su wani sun kai sun kawo ba abin har ya ba ni tausayi wato ita soyayya jahilar mahaukaciya ce babu talaka babu mai kudi haka zalika babu sarakai babu attajirai duk lokacin da ta so illatarwarta sauka take yi a duk inda ta so ta yi sharafinta amma idan ba ita ba din ba ai ban ga wani dalilin da zai sanya mutumin nan yin wannan dariyar ba wallahi.
****
Lamarin da ya kara dakusar mini da jiki akan sha'aninsa yadda da kansa yake yi mini tallah status d'insa da kuma babban pege dinsa na facebook da Instagram bayan an gama shirya duka shagunan shidan kowanne d'ankare da kayan masu inganci da quality shaguna biyu da ya yi alkawari sai da ya shirye mini su da lates Textiles yaduka na manya da shaddodi d'ankare kowace kanta abin gwanin burgewa shagon cosmetics d'aya na supplements d'aya d'ayan kuma na zannuwa leces atamfofi kowane nau'in da b'angaran abaya (dogayen riguna) d'ayan kuma ya zama na takalman mata da maza da kuma b'angaran huluna iri daban daban.

Mussaman ya sanya masu shirya advert da muryar da lallai dole ta isar da sa'ko aka yi bidiyon na mussaman tun daga kan shagunana na kwari market har zuwa wad'annan sabbin da aka bud'e.

To sanya hotonan wajan a peges din sa na sadarwa ya sanya jama'arsa yin shearing kafin ki ce me messages na 'yan uwa sun fara cika inbox dina mussaman daga maiduguri mutum kusan shida na buk'atar samun gurbi daga cikin dole ne a cikinsu zan duba wad'anda suka dace daga cikinsu.

Rasa abinda zance masa na yi tunda ya ce ba shi buk'atar godiya sai dai daga zarar na kalleshi sai na ji tausayinsa ya tsirga mini har ina jin taruwar hawaye a idona da kansa yake ta yi mini tallah ya cire girman kai ya cire son a sani ya kuma cire k'yashi irin na wasu mazan ya kuma nuna shi din duk arzikinsa me nema ne ya kuma tabbatar mini da cewar abinda ya yi shine kasuwanci domin kuwa shi arziki ai ba a nemansa da sau'ki.

Ban yi gangancin kwatanta abinda ya yi ba a ganina yadda jama'arsa ma suke sharing ya isa gefe guda kuma daga can kano Hamusu da Usaini suma sun dage sosai da tallah ta kowace kafar sadarwa abin ya yi ta ba ni mamaki.

A daran na amsa wayar Baban Saude addu'a ce dai da fatan alheri anti Yagana Sahura Hadiza ma ta kira ni Ya Falmata kuwa kamar ma ta fi ni farinciki fadi take yi na jima da gaya miki cewa akwai haske cikin rayuwarki domin kina da nasibi gaba kad'an za ki zama abar kwantace.

Washe gari da safe kafin ya fita yake gaya mini akwai wanda suka gama magana da shi gogaggene fannin kasuwanci kuma mutum ne mai kula da amana don haka ya saya mini sabbin layikan waya shi wanda ya kira da Lawan zai zama kamar manager a wajan domin sa ido da kuma kula da yaran da za a sanya a shagunan
sannan akwai buk'atar samar da securities saboda dukiyar da aka zuba shaguna dai tuni an kar'be su domin a yinin ranar da bidiyon ya fita duk guda shidan kyasa da sama aka kama saboda sun yi sau'ki duk kuwa da cewar an kashe kudi an kuma yi komai cikin inganci ga soler ga Ac sannan ko'ina teis kuma akan miliyan shida duk d'aya ga wurin fuskar jama'a daf da titi jama'a na hada-hada a fannin babu cunkoso mai yawa.

Wallahi cikin yammacin ranar naga shigowar kud'ina miliyan talatin da shida.

Ya kira ni domin ya tabbatar da shigowarsu ya ce kudin shagunana ne yaa katse jin na fara yin godiya abinda baya buk'ata kenan.

Sai da ya dawo yake gaya mini sun yi waya da Baban Saude har da Babanmu ma suna yi ta yi masa godiya na ce nima duk sun kira ni sun yi mini addu'a sosai.

Anti Yagana kuma tun abin nan da ya faru a lokacin da ya yi mini kyautar kamfani suke jin kunyar juna ita dashi Ya Falmata ce dai ta kira shi a waya har ta had'a shi da Dada sukai ta yi masa godiya.

Wannan shine abinda ya haddasa mummunan rikici tsakaninsa da Hauwa wanda ya kaita ga tsautsayin kunnawa gidanta wuta tunda tsabar bala'in da tashin hankali a ranar da taga abinda yake faruwa a social media da kuma status dinsa ta d'ora abinci jallop din taliya har sai ta babbake ta yi baki tana can d'aki a kwance ta manta tana ta kuka gidan ya fara canzawa da k'aurin hayaki ga mai aikinta Ladidi bata nan ta je ganin gida.

Sulaimanu mai yi mata hidima gidan shi ya ankara domin masu gadi na can nesa abin bai je musu ba ya shiga gidan a gigice hayaki da kauri daga kicin tukunya ta yi jajawur gas na neman yin bindiga da ita da shi Allah ne yasa suna da nisan kwana ya yi namijin kokari sosai domin kuwa shine ya tunkari gas din ya kashe ya toshe hancinsa a gaggauce ya fita sai a lokacin ne ta fito a ki'dime ita da shi suka yi waje Ubangiji Allah Ya ta'kaita k'auri da haya'kin suka gama fita tukkuna ta koma cikin falon.

To tundaga ranar suke rikici shi fad'ansa yana so ya ji dalilin da ya sanya take nema ta had'a masa gobara a gida domin dai duk b'oyenta sai da ya gane lallai akwai abinda ya faru a gidan kuma Sulaimanun bai boye masa komai ba.

Ta dinga kuka tana fad'in sai ya saketa ita gaji ya ce shi kuma haka kawai ba zai yi saki ba sai da hujja.

Rikicin dai har sai da ya kai su gaban Hajja anan ne ta fad'i abinda yake sasakarta Ya gina mini plaza ya ya zuba mini kaya sannan ya kuma bude mini shaguna a kasuwar kwari guda uku ita kuma ya had'a ta da wani lalataccen kamfaninsa da ya tabbatar da cewa shi kansa ya tashi daga aiki don haka wallahi idan har adalci za a yi itama a yi mata plaza sannan a bude mata shaguna.

To sai a lokacin ne ya san dalilin tashin hankalinta.

Ya ce yadda ya mallaka mata kamafani ba tare da ya cire na'urorin da ake aiki da su ba haka zalika don ya gina mini plaza ya sanya mini kaya a ciki ba lefi ba.
Chapter 265 · 0% Book details