← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 276

Sashe 143

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya kammala tukkuna a nutse ya goge bakinsa da tissue ya dube mu gabad'aya kafin ya furta." Hauwa da gaske ke ce ki ka tura Masa'udu direbanku ya sayowa Amina maganin wankin mahaifa?"
Ta dube shi a tsanake ta furta." E, ni ce Baban Saude."
Da d'an mamaki a tare da shi ya ce." Kenan da gaske hade baki ku ka yi ba kwa tsoron Allah dama?"
Murmushin takaici ta yi kafin ta furta.'' Ko daya Baban Saude kaddara ce ta gifta wani lamari mai rikitarwa ya faru a gidan nan gabad'aya muka shiga cikin gigita, to wannan ya assasawa Amina abortion bisa tsautsayi cikinta ya zube .

Ganin yadda ya fice ba tare da an samu wata tangarda ba ya sanya na rubuta magani jikin takarda na sanya aka sayo mata domin ya k'ara taimaka mata wurin wanko abinda ya rage a mahaifarta?

Ya ce." A lokacin mai yasa kafin ki yanke hukuncin yin hakan ba ki yi yun'kurin sanar da mijinku ba, ko ko cikin bashi da uba ne?"
Shiru ta yi ta kasa cewa komai sai da ya sake maimaita maganarsa tukkuna ta ce." Wallahi ban san abinda yake tsakaninsu ba domin kuwa na d'auka ita Aminar ta gaya masa shine dalili kuma dai ni kaina ba magana yake yi mini ba a lokacin gaba yake yi da ni."
"Shine dalilin da ya sanya ki kenan yin gaban kanki a matsayinki na ma'aikaciyar lafiya ai kin fi karfin ki yi masa magana dalili yana fushi dake, kamar doka ce babba a kowane asibiti sai da amincewa da sanya hannun mai ruwa da tsaki, ina nufin wanda yake da hurumi akan abu, akan wane dalili zai amince cewa da gaske k'addara ce ba shirya zubarwa kuka yi a tare ba?"
Ta fashe da kuka tana ce wa." To ni dai Allah ne shaidata Baban Saude ni ma cikin ne fa da ni, a ganina kafin na bada goyon bayan wata ta zubar da nata ai ni zan yi yun'kurin zubar da nawa dalilin abinda ya ratsa tsakanina da shi, ai gashinan a zaune yana ji ni ba matarsa ba ce yanzu domin ya sake ni."
Baban Saude ya dube shi da saurin gaske domin maganar Hauwa ta karshe ta kidima shi.

Bai ce komai ba still hankalina na kan computer dake gabansa kuma bai dago ya dubi Baban Sauden ba..

Sai ya juyo gare mu yana fad'in." Ban san da haka ba Hauwa, kuma ni nan ban titsiyeki domin naga iya gudun ruwanki ba.

Abinda ya sanya ita Amina muke zarginta da aikatawaa saboda ta ta'ba yun'kurin yin hakan a shekarun baya, abinda ku ka yi ba daidai ba ne, mai yasa a lokacin da za ki aika Masa'udu ya sayu maganin ba ki kira shi kin sanar da shi ba a matsayinsa na jagoranku kuma wanda yake da hakki a kan cikin."
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.

Sai ya cigaba da cewa."
ko ni nan babu wata mace da za ta yi mini haka na amince da gaskiyarta.

Sannan ya sanar da ni cewa kun had'a kai kun ware d'ayar mutuniyar kirkin cikinku, ai duk macen da mijinta zai zauna ya dinga yabo tare da fad'in kirkinta ita ta amsa sunan mace ba irinku 'yan amshin shata ba, to me ta yi muku, mutuwa ce fa ta raba tsakaninta da mijinta mai rasuwa Alhaji Amadu, kuma ya barwa Amininsa wasiyya akan ya aureta domin cigaba da kula da ita da yaranta.

Ban ga matar nan ido da ido ba, amma zaman nan da na yi kaf alheri da kyautatawarta mijinta yake gaya mini, ni ma gashi na ga ni yadda ta sauke ni da hidima daban daban tamkar wani basarake.

Ba ku ji kunya ba Hauwa, ita fa macen da ta fi biyayya ga miji itace sarauniyarsa wannan matar ta dame ku ta shanyeku a komai sannan kun yi sake wanda kuke jin haushinta dominsa ya fi sonta kun hade mata kai shi kuma ya had'e kai da ita, ina kara gaya muku kun cika shashasha!"
Tsit! wurin ya dauka bayan yin shirunsa, zuciyata ban da dokawa babu abinda take yi wannan wane irin cin mutunci ne da cin fuska Baban Saude ya shirya yi mini.

Menene lefin Hauwa anan da za a sanyata a gaba da cin zarafi haka.

Shikkenan a rayuwa mutam ba zai yi kuskure ba.

Wasu hawaye masu d'umi da yaji suka fara simiyowa suna bin kumatuna.

Wannan karon hawayen ne kawai suke fita masu zafi da ciwo babu damar yin gunji sai dai ciwon zuciya.

Ya d'auki kofin shayinsa ya kurba kafin ya cigaba da ce wa." Gaskiya ku gyara domin kuwa babu wata gadara da za ku yi a karkashin ikon namiji, mijinku gashi nan yana ji ko shine ya yi ba daidai babu ruwana zan titsiye shi na gaya masa gaskiya ko ta yi masa dadi ko ta yi masa zafi wannan shine zaman tare Alhaji Tajo ba surukina ba ne a yanzu abokina ne, mun yi sha'kuwa ta ban mamaki a sha'aninsa zan yi tsalle na dire a ciki koda kuwa bai shafi Amina ba. kuma za ki koma dakinki Hauwa kin ji ko?"
Tana kuka ta ce." A, a Baban Saude ni kam na ha'kura gaskiya wallahi zuciyata ba za ta iya d'auka ba."
Baban Saude ya yi shiru yana kallonta da mamaki kafin ya ce."Zuciyarki ba za ta iya d'aukar me ba?"
Kafin ta furta wani abu ya rigata ta hanyar fad'in." Ka ji abinda na ke gaya maka ko, gabad'ayansu fa Maryam ta tsone musu idan ba haka ba menene na fad'in wannan maganar, zuciyarta ba za ta iya d'aukar ganin Ina tare da Maryam ba, idan har ina son zama da ita amsar kawai na saki Maryam sai zuciyarta ta d'auka."
Yana ajiye maganarsa na ce.

"Baban Saude gabad'aya maganar ba haka take ba zahirin gaskiya bai gaya maka wasu abubuwan da suke faruwa ba.

Wanda ya zama lallai ace an zauna a kansu.

Wallahi ba mu ware Hajiya Maryam ba illa iyaka shi da ya fifita a kanmu, gashi nan a zaune idan har na yi masa sharri to ni Amina ina ro'kon Allah Ya d'auki raina a yanzu wallahi tallahi zalitarmu yake yi." Na kai karshen maganar muryarta na rawa.

Ya nisa kafin ya ce." Ai dama shari'a ta aure ba za a ce mutum d'aya ne yake da laifi dole ta kowanne b'angare a samu abin fad'a, kuma dama ni ba ni da niyyar rufe wannan mas'alar ba tare dana tambayi kowaccenku ba,
ni babban abinda ya ba ni haushi daku shine yadda kuka had'ewa abokiyar zamanku kai kuka ware ta sannan da ki ka san cikin ya zube mai yasa ba ki gaya masa ba har sai da aka ja lokaci dole ya d'ora alamar tambaya a kanku."
Hauwa tana kuka ta ce." Dukan mu fa yake yi akan ita Hajiya Maryam din a gaban mai'aikinmu Baba Tabawa ko ita sheda ce ya dinga marina ya tunkud'e ni da karfi na fadi har sai da na yi targad'e a hannuna duk da hakan bai ishe shi ya sake ni."
Ta dinga kuka da iyakacin karfinta!

Baban Saude jikinsa ya yi sanyi ya dinga maimaita kalmar duka yana kallonsa shi kuma jikinsa duk ya mutu don da alama bai tsammaci faruwar hakan ba.

Baban Saude ya dube ni yana fad'in." Kenan kema sheda ce Amina?"
Na gyada kaina tare da fad'in." I, wallahi ni na shiga tsakaninsu ma." Na fad'a a dan tsorace dalili ina jin tsoron allura ta tono garma ya gaya masa na ta'ba toshe masa hanci da fillo.

Ya ce."To akan me, Allah ya taimakeka dama akwai duka mai illatarwa a cikin shara'din aure kuma mace mai d'auke da yaron ciki, anya akwai imani a nan?"
Fuskarsa ta had'e sosai yana kallonsa da mamaki.

Sai ya kasa daga kansa ya dube shi cikin kame-kame ya ce." Baban Saude yaran nan ba su da kirki ko kad'an ni kuma ban yi mata dukan da zai illatata ba."
Cikin 'yar 'kure baban Saude ya ce." To wane iri ka yi mata?"
Ya furta." Marinta na yi?"
Ya ce." To ai mari karshen tozarci kenan a mari mutum a fuska yanzu tsakani da Allah ko tunkiya ka daure a gidanka ka mare ta, ina lefin ma gabar da kake yi da su duk da itama a shari'a haramun ce, anya kuwa ranka shi dad'e ka shirya sulhunta gidanka kuwa?"
Shiru ya yi bai ce masa komai ba.

Sai ya juyo kaina yana fad'in." Sai me kuma?"
Na ce." Magana ce akan yaranmu da ya kwashe ya kai wa matar tasa, to wannan ma yana daya daga cikin abinda yake mana ciwo koyaushe idan mun yi magana sai ya nuna kamar ya fi mu iko a kansu yana kiranmu da marasa tarbiya komai muka yi ba mu iya ba."
Ya dinga jijjiga kansa kafin ya sake dubansa a karo na kusan hud'u kansa yana kasa bai dago ba tsabar kunya ta hana shi musantawa yadda na lura yana tsoron ya tanka mu sake 'baro wata wata maganar da za ta zama abar tattaunawa tare da nuna masa kuskuransa.

Baban Saude ya ce." Idan kuwa hakane ka takewa yaran nan hakkinsu Alhaji Tajo kasan tsananin so da k'auna da sha'kuwar dake tsakanin uwa da d'anta kuwa? me yasa ka d'auki ga'barar raba sha'kuwa iyaye da 'ya'yansu.

Mai yasa ka fifita Maryam a kan su?

Idan har gaskiya ne abinda suka fad'a tabbas akwai zama tsakani na dakai na mussaman ko ba mu yi yanzu ba za mu anan gaba wannan ba daidai ba ne bari na gaya maka, ai ka haihu to muddin kana so 'ya'yanka mata su rayu cikin mutunci da kulawa a gidan mazajensu to kada ka zalinci 'ya'yan wasu tare da biyewa son zuciya.

Maganar nan fa gaskiya ce da ake cewa duk abinda ka yi sai an yi maka." Ya nisa kafin ya cigaba da cewa."
Ban yadda ba gaskiya dole nasan a cikinsu akwai wadda ta fi kyautata maka kamar yadda ka gaya mini yanzu kana jin dadin zama da Maryam.
Chapter 143 · 0% Book details