← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 276

Sashe 150

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma yanayinsa kadai ya tabbatar mini da cewa lalurar da matarsa take ciki ta dame shi saboda ga yanayin yadda yake bawa Baba Tabawa labarin ciwon tabbas ya ci jikinta da k'arfi.

Bayan shud'ewarsa daga wurin da kamar minti goma na tashi na bi bayansa zuciya cike da zullumi da fargaba.

A kwance na same shi kawai ya tsirawa rufin d'akin ido.

Gabad'aya sai gwiwa ta yi sanyi (wai shin me cece ma duniyar nan ne) tausayinsa ya d'an kamani, amma bari tasirin hakan ya raunarta da ni ba.

Har yanzu da sauran takaicinsa a cikin zuciyata.

A nutse na zauna gefan k'afafunsa.

Ya dube ni bai ce komai ba sai ya janye idanuwansa.

Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Wallahi ba mu san ta yi ciwo ba, ashe har kwanciya ta yi a asibiti babu labari ai da mun shiga mun dubata."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba.

Sai na janye idona daga kansa na yi kasa da kaina ina dan wasa da yatsun hannuna.

Shiru d'akin ya yi na minti kusan goma kafin na sake dubansa yanzu idonsa a lumshe yake kamar mai shirin bacci ganin haka sai na tashi da niyyar fita.

Ba tare da ya bud'e idon ba ya ce." Koma ki zauna ina son magana dake....
*Yau fa mutumin ko ni ma ya ba ni tausayi
Amina a sassautawa Babanmu mana.*
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima:
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2K COMPLETE ON TALGRAM.*
*VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*102*
Na zauna din kamar yadda ya buk'ata.

Ya tashi zaune tare da sauke k'afafunsa kasa.

Ya dube ni a nutse kafin ya furta." Akwai matan da annabin rahama ya fad'a cewa ya gan su a can karkashin wutar jahanama, kuma suffofinsu sukan bayyana tun a duniya.

Akwai kuma matan da tun a duniya za a dinga yi musu ishara da nuni da cewar aljannar Firdausi madawamiya ce a gare su.

Sune muminai wad'anda ayyukan alherinsu yake bayyana ga ko'ina."
D'akin ya yi tsit bayan ya gama maganarsa.

Na dube shi tare da furta." Ni ina a wane babi kenan, ko kuma na ce a wane ajin ka ajiye ni ai ba kai kake bada aljannar ba."
"Tabbas ba ni nake bada ita ba, amma tana k'asan kafafuna haka annabin rahama ya fad'a."
Na jima ina dubansa da mamaki wato yabi duk hanyoyin da zai raunatar mini da zuciya bai ci galaba ba shine ya fara wa'azi.

Ni abin ma dariya ya so ya ba ni, Ashe ya sani yake takewa da yake hakkinsa ne, ashe da ciwo kuma babu dadi.

Na daure sosai kafin na furta." Ayyukana ba su kai ka daga mini kafarka ba kenan?"
Ya gyada kansa yana ce wa." Gaskiya ba su kai ba har yanzu.

Momi ce ko yau ta fad'i ta mutu wallahi na yafe mata ki shaida aljanna da izinin Allah zata tabbata a kanta."
Na yi shiru zuciyata tana hantsilawa saboda tsabar bala'in b'acin rai.

Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un na cigaba da nanatawa ban sake mayar masa da martani ba, kuma ban tashi daga wurin ba na ji gyaran muryarsa yana cewa." Kwanaki mun yi waya da Hajja take sanar da ni za su tafi maiduguri da yaran zuwa hidimar bikin 'yar anti Yagana hakane ko."
Ban dube shi na ce." Hakane yau saura kwana tara, jiya dai Hajja take ce mini ranar alhamis za su tafi."
Shiru ya d'an ratsa wurin kafin ya nisa ya sake ce wa." Yanzu nawa ki ke ganin zamu ba su gudumawa ni dake?" A takaice na furta." Duk abinda Allah Ya hore maka."
"Ai shawara na tambayeki ni Allah Ya hore mini tuntuni.

Kawai ki gaya mini abinda za a ba su ai auran fari za su yi ko."
Na kalle shi babu sukuni na furta." Ya za a yi na yanke maka abinda za ka bayar, ai ba kudina ba ne, naka ne, kuma dai daidai gwargwado sun yi hidimarsu ni ma kuma tuntuni na tura mata da tawa gudumarwar abinda ka ga dama shi za ka ba su."
Ya gyada kansa yana fad'in." Ok na ba su 5m ya yi ko?"
"Idan haka ka yi niyya ni ina ruwana?" Na fad'a tare da d'auke kaina domin har ga Allah zuciyata zafi take yi mini game da irin mummunan fatan da ya gama yi mini yanzu.

Ya ce." Kada ki gaya mini magana Amina, ba na son rashin kunya da fitsara ko kin ga na ta'ba jikinki ne, kin ga alamar sha'awarki a k'wayar idona, ina ce wannan shine yake kawo mini raini a wurinki to ki ri'ke kayanki ba na so."
Na fashe da kuka tare da cewa." To ai dama ban ce ka nemi shawarata ba ni ma, kuma ban ce ka neme ni ba, abinda ka yi niyya shi za ka yi, ni ma abinda na yi niyya shi zan yi, aljanna dai kuma babu wani bawan da yake bada ita ta Allah ce, ta hanyoyin alheri ana samunta ba sai ta dalilin wani ba."
"Na ji abinda ki ka ce ta shi ki tafi."
Na tashi haka kawai na tsinci kaina da buga siket din da yake jikina na kama hanyar fita raina a masifar 'kuntacce.

Ban sauka ba tukkuna sai da na daidaita yanayina na sauka na same su suna nan a wurin suna hira Hauwa hannunta ri'ke da apple tana ci babu abinda ya dame ta sai addu'a da ko'karin rabuwa da cikin jikinta lafiya.

Ban zauna falon ba kai tsaye d'akina na nufa na yi zaune zugum a gefan gado zuciyata na ta yi mini sa'ke-sa'ke masu kyau da marasa kyau!

Lallai cikin wannan duniya babu komai face rikici da tarin kalubale.

Babu yadda ban yi ba da Hauwa akan ta shirya bayan magriba mu shiga mu duba Momi amma fafur taki tace itama abar dubawa ce domin kuwa bata kaita jin jiki ba.

Ganin taki fahimtata ya sanya na kyaleta kawai muka shirya da Baba Tabawa muka tafi dubanta.

A harabar gidan muka riski Salim da Adam a tsaye suna magana.

Da sauri shi babban ya d'auke kansa yayin da karamin ya sassauta a nutse ya dube mu da ladabi yake fad'in." Mama ku ne."
Na ce." E, mune Adam mun shigo duba Momi ne.

Sai ya yi yar dariya wadda babu annashuwa a cikinta ya furta." To shikkenan mu je na yi muku jagora."
Gaba ya yi muka bi bayan shi yayin da Salim din yake ta ciccin magani har da jan tsaki.

Murmushi kawai na yi a zuciyata gabad'aya yaron ma ni tausayi yake ba ni, domin kuwa ya d'auki lamarin da zafin gaske.

Falo muka zauna ya nufi bedroom din ta yana fad'in ."Bari na sanar da ita." Ba mu kai minti biyar da zama ba daya daga cikin masu aikinta ta fito daga kicin da wata madaidaiciyar roba a hannunta Hassana da Minal suna biye da ita.

Ganinmu a zaune ya sanya yaran suka tsaya.

Ita kuma mai aikin ta karaso wurin da muke har sai da ta risina kafin ta gaishe mu gabad'aya.

Ina kallon yadda Baba Tabawa take jan yaran da wasa da tsokana amma suna can nesa da mu sun tsaya suna ta kallonmu kamar sun ga dodanni.

Duk da akwai sabo a tsakaninmu dalilin shigowar da suke yi amma ganinmu a gidan sai ya zame musu wani banbarakwai
Raina ya 'baci nan take zuciyata ta dinga raya mini abubuwa marasa kyau to idan ba an zauna da yaran an fadi wata magana ba mai zai sanya k'ananun yara irin wad'annan su dinga yi mini wani irin kallo.

Abin b'akinciki da takaici ma har da 'yar cikina 'kiri-'kiri saboda kin gaskiya.
Chapter 150 · 0% Book details