Sashe 120
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Irin rikon da take yi wa yaran nan ko ni uwarsu albarka yadda zuciyata take raya mini mummunan nufi akan abinda take yi ba tsakani da Allah ba ne na'ki aminta, domin babu wata alama ta mugunta da ta ta'ba nunawa akan yaran wanda zan gazgata hasashen zuciyata.
Na kan zauna na yi ta tunani akan hakan wataran har na share hawaye idan zuciyata na kissima mini zarginta.
To me ta yi mini idan ba alheri ba, muddin na cika 'yar halak kuwa duk irin abinda zuciyata ke raya mini akanta na yi tsalle na dire na ce ba haka ba ne.
Amma wani abin mamaki a wasu lukutan sai na dinga jin mugun haushinta da kishi mai tsanani mussaman idan na tuna yadda maigidan yake bada muhimmanci kwarai da gaske akan abinda ya shafeta.
Ni dalilin alherinta a gare ni nakan kawar da kaina na mayar da komai ba komai ba ne, amma Hauwa kuwa ba ta iyawa sun sha yin fad'a akanta don bata iya jurewa ba.
Wasu lukutan ni nake shiga tsakani na nuna masa cewa duk sanda zai yabi matarsa ya daina yi a gabanmu zuciya bata da k'ashi.
Amma ya'ki dainawa.
Hauwa ba ta fi ni jin takaicin abinda yake yi ba, kawai ina daurewa ne, kuma ba ta fini kishinsa ba.
Idan har muka ce zamu hade mata kai mu biyu abin ba zai yi kyau ba, shiyasa dai nake ta jurewa.
Amma na soma yarda da maganar da kullum take gaya mini cewa duk abinda take yi akan yaranmu ba tsakani da Allah ba ne.
Shi kansa maigidan ta d'aure shi, kuma baya ta'ba zuwa ya gaya mana ta yi masa lefi duk kuwa da cewar suna samun matsala mussaman ta fannin auratayya ni ina ganewa.
Dawowar Salim daga karatu abubuwa suka fara lalacewa.
Shine yaronta na biyu bayan Nusaiba itace babba sau daya kacal ta ta'ba shigo wa ta gaishemu, Shima kamar an yi mata dole Shekara daya da wani abu yanzu bata sake shigowa ba duk kuwa da cewa tana yawan ziyartar uwar akai-akai, sa'i da lokaci idan ta zo su Yusi sukan shigo da yaronta, amma dai ita kam ba ta da fuska da fara'a, irin na Mamanta.
Kwana biyu da dawowar yaron muna zaune ni da Baba Tabawa a falo muna hira, gefe kuma muna d'an ta'ba kallo a tibi da yake Baba Tabawa ma'abociyar son kallo ce dalilin da ya sanya ma kenan wasan kwaikwayon dadin kowa baya shigeta.
Yanzu ma shi tashar arewa24 din suke haskawa.
Kamalu ya shigo tsaf dashi cikin Pakistani da yake ire iren kayan da uwar rikon nasu ke sayarwa kenan, duk rabi kayan ma da suke sanyawa irinsu ne da jallabiyoyi wattanin bayane ma na ga ta yi musu sabbin 'dinkunan shaddodi da yadika.
Sune sanye a jikinsa kansa da farar hula mai raga.
Tun da ya shigo nake nazartarsa.
Yana zama a gefena k'amshin turaransa ya kama mini hanci.
Na zuba masa ido Ina kallo ban ce komai ba.
Ya dube ni a nutse kafin ya ce." Mama mun yini lafiya?"
Na amsa da "Lafiya lau ina Momin?''
A takaice ya furta." Na bar ta a gida, lafiyarta lau."
Ya dubi Baba Tabawa da take ta tsokanarsa da yake da sheik take kiransa irin yadda taji maigidan na kiransa.
Itama Momin hakan take ce masa.
Ya yi 'yar dariya yana gaisheta ta amsa tana fad'in." Mai zaka ci anan din duk da nasan dai Momi ba za ta barka malami da yunwa ba."
Ya ta'ba cikinsa yana dariya ya ce." Aikuwa kamar kin sani wallahi tare ma muka ci abincin rana a koshe nake.
Amma da daddare dai zan ci kwad'on zogale."
Ta ce." Idan wannan ne ai mai sau'ki ne, zan yi maka in sha Allahu."
Ya ce." Na gode Baba."
Daga haka sai ya shiru bai sake magana ba, ya fito da sabuwar wayarsa Samsung da Momin nasu ta saya masa ya fara dubawa fuskarsa babu walwala.
Shiru falon ya yi.
Daga ni sai shi domin Baba Tabawa ta shiga kicin domin dora sanwar dare.
Kamalu tun yana yaro yake da wani irin hali na bakar zuciya da fushi.
Wannan dabi'unsa ne raunanarsu kuwa yana da ala'ka da tafiyarsa karatu da kuma shekarun girma.
Amma ba haushe ya ce idan ka jima ba ka ga mutum ba, to duk ranar da kuka hadu ka tambayeshi halinsa.
Ni na haifi abina nasan halinsa ciki da waje.
Yana da mu'amula ga wanda ya so su yi mu'amular.
Amma baya jurar wulakanci a ko'ina ne, akan hakan suka dinga fad'a da Turmizi a can baya.
Duk da har yanzu bai fad'a mini abinda yake damunsa ba, ni da kaina na karanci damuwa mai yawa a tattare da shi.
Amma ba zan ce masa uffan ba har sai ya magantu tukkuna."
"Mama ina ta kiran Lambar wayar Baba Hamusu bata shiga tun safe fa." Ya fad'i maganar yayin da yake kallona da wani irin yanayi.
Na ce." Wata'kila network ne, amma Hamusu ai baya kashe wayarsa, ko jiya da yamma mun gaisa."
A sanyaye ya ce." Ina tsammanin hakan."
"Neman me kake yi masa ne?'' Na fad'a idona a tsaye a kansa.
Bai dube ni ba ya furta." Ina son zuwa kano din ne na kwana biyu a wurinsa" Na ce." To ka gayawa Baban?" Ina nufin maigidan.
Ya gyada kansa a nutse ya ce." E jiya naso na sanar masa kuma sai na manta, kuma mun yi waya fa, amma dai zan gaya masa ina jin tsoron ya ce a a ne Mama."
"Ka dai gaya masa mu ji mai zai ce, itafa Momin taku?'' ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce." Mun yi maganar dazu har ta fara had'a mini tsaraba."
Shiru na yi kawai ina kallonsa.
Har yanzu yanayinsa bai canza ba.
Na ce." Kaga ka gaya mini dalilin da zai sanya ka zuwa kano ina tsammanin ai baku wani jima da zuwa ba ko ba haka ba ne?"
Shiru ya yi bai ce komai ba sai da na sake maimaita maganarta sannan ya ce." Eh kafin tafiyarku legos ke da Baba muka je wata shida kenan yanzu.
Mama ba na tsammanin zan cigaba da zama anan, can wurin Baba Hamusu zan koma?"
"Akan wane dalili?'' Na fad'a ina kallonsa.
Wannan maganar za ta iya janyo rikici a gidan, ta kuma janyo mana b'acin rai ni da shi, abinda maigidan ya tsana kenan.
Ya dai yarda dai ya sanya akai su su yi kwana biyu gidan Gwaggo kwana biyu gidan Hajja a dawo dasu wajan matarsa.
Ni kuma ba ni da damar magana ko da ta maslaha ce sai ya juyata ya yi ta neman rigima yana fad'in don ba shi ya haifesu ba zan nuna masa iyaka, zan nuna masa bai iya ba, duk yadda zan yi masa misali ba zai gane ni ba, karshe ma sai ya ce zai kira Baban Saude dole nake jan bakina na yi shiru na kyale shi.
Gudun aure paid book ne kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba
"Mama ba zan rufe miki ba, tunda Salim ya dawo daga karatu yake yi mini wasu abubuwa na rashin kyautawa da nuna k'yama.
Ba zai ci abinci tare da ni ba, ba zai kwanta d'akin da nake ba, haka zalika a cikin kwana biyun nan baya bina jam'in sallah a massalaci, ina kallonsa ya ke tafiya wani massalacin na daban.
Ban san menene dalili ba, Mama amma kuma baya nunawa Yusi k'yama, wannan dalilin ya sanya ni yanke shawarar barin gidan gabad'aya domin ba na so watarana na kasa jurewa muddin a haka zamu dinga tafiya dashi babu kyakykyawar ala'ka, babu musabaha da girmama juna sai k'yama, zuciyata ba zata iya jurewa ba, Ina jin tsoron mu yi fad'a hakan ya ta'ba zumuncinku da zamantakewarku.
Kin ga Momi babu komai a tsakanina da ita sai alheri Ina sonta sosai wallahi irin yadda nake sonki Mama, amma ba na so mu yi abinda duka zai bata muku rai shine dalilana."
Nasan dama ruwa baya tsami banza.
Amma kuma sanin da na yi wa yaron a baya kafin ya tafi karatun ba haka yake ba.
Yaro ne mai nutsuwa da son mutane irin d'an uwansa Adam ga barkwanci.
Nusaiban dai ce mara fuska.
Na daure ban nuna b'acin raina a fili ba na ce." Kenan ba ku taba magana ba tunda ya dawo?"
Ya ce." Idan na mik'a masa hannu domin musabaha baya kar'ba.
D'azu da safe a gaban Momi ya y hakan ya 'bata mata rai sosai ta yi masa fad'a.
Shine ya tashi ya fita bai dawo ba har na fito, wallahi mama kada ki so ki ga yadda hankalinta ya tashi, shine take cewa kada na gaya miki."
Shiru na yi ina nazarin al'amarin.
Kamalu bai yi lefi ba domin kuwa anan ya yi aiki da hankali da kuma iliminsa.
Na kuma ji dad'in abinda ya yi da har ya iya danne zuciyarsa bai biye masa ba.
Shawarar da ya yanke itace mafita muddin kuwa ana son zaman lafiya.
Idan har Salim bai gane abinda yake yi kuskure ba ne, to babu mamaki wataran gagarimar matsala ta faru tunda ni nasan wanene Kamalu a fagen zuciya.
Amma yadda zan yi na sanar da maigidan halin da ake ciki shine matsalata.
Na riga nasan rikice ne akwance domin kuwa baya d'aukar abinda ya shafi matarsa da wasa.
Maganarsa daya amanarsa ce 'ya'yanta ma amana ne, a wannan ga'bar kuwa ya zame masa dole ya bincika domin tabbatar da gaskiyar abinda yake faruwa ya kuma gyara matsalar kafin ta yi nisa.
Na ce." Abinda za a yi yanzu shine ka d'an daure kad'an, ai ni ka burgeni sosai da har ka yi irin wannan tunanin wannan ya sake nuna mini cewa Kamaluna ya bambamta sosai da wanda na sani a baya.