← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 276

Sashe 128

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ba ni amsa da dan sanyin jiki.

Shiru kawai na yi ina nazari, Adam dai ko mayya ce ta haife shi dole su rabu domin kuwa
babu wani dalili da a yanzu zai hana yaran nan barin garin nan.

Na ce." Je ka falo, idan sun shigo tare ka turo mini shi." Ya amsa da "to shikkenan.

Kafin ya sanya yaran a gaba suka fita.

Gama sanya kayana ke da wuya Yusi ya shigo ya sha ado cikin yadin kufta d'inkin kansa abin kallo ne ballantana takalmin da yake kafarsa.

Babu shakka matar nan ta na hidima da yaran nan kuma duk abinda za ta yi babu bambanci abinda Adamu zai sanya a jikinsa shi Yusi zai sanya duk tsadarsa kuwa.

Ko turarukan da suke amfani da shi wallahi sai mai karfin jari.

Jikina ya yi sanyi kalau a yayin da nake duban yaron cikin Kamala da nutsuwa tare da kwarjini fatarsa luwai alamar hutu da jin dad'i sun ratsa jikinsa.

Kafin ya zauna a gefana sai da ya d'an risina tare da furta." Mama ina kwana, an tashi lafiya?"
Na amsa a nutse ina sake nazartarsa har yanzu babu walwala da sukuni a tare dashi tabbacin abubuwan da suke faruwa na damunsa.

Ya nisa kafin ya sake fad'in." Momi ta ce tana gaisheki ta ce na gaya miki za ta shigo idan an jima."
Sai da nutsu sosai na dube shi babu fara'a a tare da ni na ce." Yusi ina so ka bud'e kunnuwanka da kyau ka ji abinda zan gaya maka, hukuncin na yanke kuma babu mahalukin da ya isa a wannan ga'bar da tura ta kai bango ya dakatar da ni." Na yi shiru Ina kallonsa yayin da gabad'aya ya shiga nutsuwarsa alamun fargaba da tashin hankali sun gama bayyana a fuskarsa.

Na cigaba da ce wa." Hukunci na yanke akanka kai da d'an'uwanka Kamalu za ku bar garin nan gabad'aya rikonku zai koma hannun Hamusu za ku cigaba da ri'ke mini harkokina yanzu shirin da na yi kenan domin tun jiya na gayawa Hamusu halin da ake ciki saboda haka yanzu za mu je tasha tare na sanyaku a mota in sha Allahu rabbi."
Matsananciyar damuwa ya shiga wadda baki ba zai iya misalta irinta ba.

Ina kallonsa yana ta ko'karin mayar da hawayen da ya cika kwarmin idonsa amma duk dubararsa sai da ruwan hawayen ya kwaranyo kumatunsa.

Murya na rawa ya ce." Mama mai yasa za ki yanke wannan hukuncin, ki dubi Allah da Annabi ki janye kada ki hukuntani akan laifin da ba nawa ba.

Ki dubi k'auna da soyayyar da Momi take yi wa jininki kada ki sanya 'yan uwanta su yi mata dariya.

Mama ni da Adam akwai k'auna da sha'kuwa sannan ba na so na rabu da Baba, ba zan ta'ba mantawa da hallacinsa a gare ni ba.

Sannan Momi tana nan tana yi mana shirye shiryen tafiya karatu saudiya makarantar da Yaya Salim ya yi karatu, ki yi hakuri Mama, kada ki hukunta Momi da laifin da itama ranta yake soyuwa."
Ga'bo'bina ne suka yi sanyi ganin yadda hawaye suke zarya a dakalin fuskarsa.

Ya kama hannuna ya ri'ke kamatau jikinsa har karkwarwa yake yi.

Na ce." Yusi ba ka ji wani iri a cikin ranka ba a lokacin da Salim yake yi wa dan'uwanka sharri, abu mafi muni fa ya jingina masa.

Da farko ban d'auka abin ya yi tsanani ba na danni zuciyata duk domin a zauna lafiya.

Amma Yusi ba abu ne mai wahala ba a yanzu dai na tsaya da Momi da Salim a gaban alkali domin yin shari'a dasu akan wannan mummunan sharrin da Ubangiji ya halakar da wani gari kacokan akan aikatawa.

Sai dai na yi hakuri ne bisa abinda uwar rikon naku take aikatawa a kanku na alheri wanda idanu suke gani sanin bad'ini kuma sai Allah.

Wannan shine dalilin da ya sanya ni tausar zuciyata akan danne maganar ba tare da na d'auki matakin kare hakkin Kamalu ba.

Allah shahidi ne zai bayyana gaskiya da gaggawa.

Yusi kana maganar ba za ka iya rabuwa da Baba ba shin zaka iya tuna ubanka Yaya Aminu? ko ka manta dashi ne tunda yanzu ka kasance cikin daula wurin iyayen rikonka har kake ko'karin canza shi a matsayin wanda ya zama 'kashin bayan samar da kai!"
Na yi shiru Ina mayar da hawayen dake ta yun'kurin zuba.

Shi kam kuka yake yi sosai.

Cikin rawar murya na ce." Nasan ka manta da shi ko Yusi, ni da nake raye a duniyar ma ka manta da ni to balle babanka wata'kila jin dadi ya sanya ba ka yi masa addu'a tunda ka nunawa duniya ka yi sabbin iyaye."
Hawayen da nake dannewa suka goce da karfinsu duka dinga fafara gudu a kumatuna.

Na ri'ke hannunsa da kyau na ce." Ka ture maganar sabo da hallaci da kyautatawa Yusi duka nasan mutanan nan biyu sun yi mini ko da ba don Allah suka yi ba to ni ma ina rokon Allah ya ba ni ikon rama musu, amma ba na ji a zuciyata za a samu zaman lafiya da juna muddin Kamalu da Salim suna zaune inuwa daya kuma a makwanci d'aya.

Kun girma da kai dashi ku tafi ku taimakawa kanin babanku ku nemi arziki ta hanyar halak, ina da shaguna da dukiya a hannun Hamusu sai mu 'bullo da hanyoyin nema domin mu gina kanmu da gobenmu, watarana za ku yi aure, za ku hayayyafa a wannan lokacin ya kamata ace kun dogara da kanku Yusi ba wai a ce koyaushe kuna ra'be-ra'be a gidajen mutane ba."
Kuka kashir'ban yake yi yana fad'in." Mama na fahimci azancin ki, na gane abinda ki ke so na gane, amma don Allah Ina neman alfarma a wajanki duk rintsi kada ki yi rigima da Momi wallahi mutuniyar kirki ce, ina kaunarta kamar yadda nake kaunarki Mama, kuma duk abin nan da yake faruwa babu sanya hannunta ko da anti Nusaiba ta dawo muku da yaran nan wallahi bata sani ba lokacin tana bacci da ta tashi ta samu labari wallahi sai da ran anti Nusaiba ya 'baci da kuka ta bar gidan.

Ita kanta Momi ta rasa yadda za ta yi da su.

Adam ne kawai bai shiga rigimar ba, Yaya Salim da anti Nusaiba sun had'e kansu sun daina jin maganar Momi."
Na ce." Sai ka ce mara hankali Yusi, ba zan yi rigima da ita ba, to akan me? ai ta yi mini alheri, abinda dai nake so da kai shine ka samu nutsuwa ka kuma kwantar da hankalinka, maganar cigaba da karatu kuma ko ba ku fita waje ba sai ku d'ora a bayaro university ku kai matakin da kuke buk'ata in sha Allahu."
Ya rike hannuna yana kuka." Mama zan bi umarninki zan yi abinda kike so muddin hakan zai sanya ki daina wannan kukan.

Jin dadi bai sa na mantaku a matsayin iyayena ba.

Babanmu duk lokacin da na yi sallah ina yi masa addu'a, ban manta daku ba Mama, ni dan halak ne ban mance wahalar rayuwar da ki ka sha a kanmu ba.

Har abada ba zan canza ku ba."
Na sunkuyar da kaina kasa ina tsiyayar da hawaye masu zafi da 'kuna.

Gabad'aya duniyar ta gama fita daga raina saboda masifa da tashin hankali.

Tsaf ya goge mini hawayen idona yana fad'in." Ki yi hakuri Mama ki daina yi mana kuka don Allah."
Ban ce komai ba na tashi tsaye shima ya tashi tare da dafa kafadata da hannunsa.

Lokacin da muka fito falo Kamalu da Adam ne a zaune suna magana da sauri yaron ya zame daga kan kujerar da yake zauna yana fad'in."Mama ina kwana mun tashi lafiya?"
A nutse na amsa da kulawa sai ya koma saman kujerar ya zauna jikinsa duk a sanyaye.

Hauwa ta fito daga d'aki da tawagar yaran a bayanta tana fad'in." Kun shirya kenan?" Kafin na amsa Adam ya gaisheta ba tare da ta dube shi ba ta amsa kamar ba ta so.

Na gyada kaina tare da kallon kamalu da kansa yake sunkuye na ce." Tashi mu tafi."
Baba Tabawa ta fito daga kicin hannunt
ri'ke da madaidaicin baho da dabino a ciki.

A nutse muka gaisa kafin na d'ora da fad'in." Baba zan kai yaran nan tasha zuwa kano yanzu zan dawo in sha Allahu."
Ta ce." To shikkenan sai kin dawo Kamalu a gaishe da mini da Gwaggo da kyau sai kun dawo Yusuf." Yadda take magana shi ya sake tabbatar mini da cewa ba ta fahimci nufina ba domin kuwa da ta gane hukuncin da na yanke sai ta yi magana akan hakan.

Adam da sanyi jiki ya dubi Yusi yana cewa." Za ku je kano amma babu labari Yusi babu neman rakiya, ni ma ina so na je na gaisa da Gwaggo da Baba Hamusu."
Yusi ya riko hannunsa ya tashi tsaye muryarsa sanyi kalau ya ce." Wallahi ban san da tafiyar ba sai yanzu ka yi hakuri d'an uwa, idan har za ka je sai mu je ai babu damuwa."
Da farinciki a fuskarsa ya furta " Zan je mana bari na sanar da Momi kai kun yi sallama ko?"
Yusi ya girgiza kansa a hankali ya ce." Zan shigo yanzu na yi mata sallama.

Adam na fita ni ma na kama hanyar fita zuciyata cike da zullumi da nazari nasan ba karamin gagarimin rikici ne zai 'balle a gidan ba dalilin wannan matakin da na d'auka.

Amma a shirye nake da tarar komai daga maigidan koda kuwa ta rabuwa ce.

Ai an yi abinda aka yi, Allah Ya shige mini gaba.

Muna fita harabar gidan Masa'udu shine babban direbanmu da ya ajiye mana domin zurga-zurga dukda ba kasafai muke fita ba amma tun farko dama ya hana mu tu'ka mota a wasu lukutan ma ya gwammace shi da kansa ya ja akan wata daga cikinmu ta ja
Ya taso da sauri tare da risinawa yana gaishe ni na amsa a gurguje domin ba na so Adam ya sake shigowa ya same mu ban san mai zan ce masa ba.
Chapter 128 · 0% Book details