Sashe 241
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Usaina sai dariya take yi tana kallonsa ta ce." Baba ka ga hancin wannan irin nawa ko? dama Mairo ta ce da ni suke kama?''
Hassana kamar wata shashasha ta ce." Ni zan dinga goya d'aya kema ki goya daya ko?"
Minal ta ta'be fuska za ta yi kuka tana ce wa." Baba ni fa? ni ma ina nawa wanda zan goya."
Sai kuka hawaye share-share suka shiga kasa tsare a kumatunta.
Ya janyota da saurin gaske ya d'ora saman cinyarsa yana share mata hawaye.
Ta rike shi tana kuka tana fad'in." Ina nawa yake Baba." Na kar'bi Usainin daga hannun Hassana na ce." Ga naki nan shine Usaini na bar miki."
Ta fara ko'karin ri'ke shi nasa mata a jikinta ya tare da hannunsa.
Ta saki dariya tana ta'ba kumatunsa ya d'an bud'e ido d'aya sai kuma ya rufe tasa dariya tana cewa." Baba ka ga ya bud'e idonsa nan d'insa ya yi ja ko ciwo ya ji." Ta nuna kumatunsa da wani tabo a wurin wanda ya yi jaa sosai ya bambamta da fatarsa.
Da wannan alamar Allah Ya bambamta mana su Amma kamanninsu daya shi Usainin ne mai wannan tabon.
Ya ce." Ba ciwo ya ji ba haka Allah ya yi masa baiwa."
Ta ce." Mama kin bar mini shi ko?" Na d'aga kaina.
Yarinyar bakinta ya'ki rufuwa tasa yatsanta a cikin hannunsa ya kuwa d'amke ta dinga k'yalkyala dariya tana duban 'yan uwan "kin gani ko ya rike ni, Usaina kin ga ya rike mini hannu."
Su dai dariya kawai suke yi mata.
Khalil ya shigo bakinsa har kunne da yake sun riga shi dawowa shi yana cikin yaran da za su yi saukar al'kur'ani sun bambamta musu lokacin tashi mahukunta makarantar.
A nutse na ce." Shigo sosai mana." Ya shigo yana ta washe baki ya ce." Masa'udu ne ya gaya mini Mama ta haihu kuma guda biyu Irina."
Uban ya kama yi masa dariya.
Ya matsa kusa da shi yana ta duba fuskar yaran ya kar'bi na hannun Usaina yana cewa." Wannan shine a babban mama." Na ce." Shine na hannun Minal kuma Usaini." Abinda ya yi gabad'aya sai da ya ba mu mamaki har uban ya rungume shi a kirjinsa ya rintse idonsa kimanin minti biyu ya bud'e cike da kwalla ya dinga fad'in." Allah Ya raya ku, Allah Ya sa mu yi zumunci domin Allah mu so junanmu domin Allah, Ubangiji Allah Ya yi wa Babanmu tsayin rai."
Na yi saurin sunkuyar da kaina kasa jin k'walla ta cika mini ido.
Yaron nan yana da kaifin basira da tunani.
Yasan shekarun girma sun cimma Babansu gasu k'ananu shine yake wannan addu'ar yana so su girma tare dashi
Shi kansa jikinsa sai da ya mutu.
Amma da yake namiji ne bai nuna rauninsa ba yaron ma yana addu'a amsa masa yake yi.
Sai da ya gama tukkuna ya ce." Za mu je umara bayan mun yi bikin suna ni da kai ko Babana." Ya gyad'a kansa cikin dauriya da ko'karin hana 'kwallar idonsa zuba." Ya furta." Akwai wurin da zan nuna maka jikin d'akin Allah sai ka tsaya sosai ka roke Allah Ubangiji Ya raya ni cikinku na ga girmanku ko?"
Shiru ya yi bai ce komai ba 'kwallar dai da yake ko'karin hana ta zuba ita ta fara d'igowa saman towel din jaririn da yake hannunsa.
Ya ce." Menene haka kuma Baban masu gida, a gaban 'kananka za su yi maka dariya."
Ya d'an share hawayen ya fakaice ya dube ni yana cewa." Mama."
Na amsa Ina kallonsa da wani irin yanayi gabad'aya duk ya dakusar mana da walwalarmu."
Ya cigaba da cewa." Mama ta ji kin haihu ko na je na gaya mata?"
Na ce." A a bata ji ba dama jira nake ku dawo daga makaranta."
Ya tashi tsaye da yaron a hannunsa Usaina na mik'a hannu ya bata ya k'i ya mi'ko mini uana fad'in." Zan je yanzu na gaya mata."
Na kar'be shi a hankali na ce." To hakan ya yi."
Fita ya yi daga d'akin da d'an sauri.
Muka dubi juna ni da shi bai ce komai ba haka zalika ni ma haka.
Na dube su a nutse na ce.
"Ku je ku cire kayan makaranta a yi alwalar magriba sannan a samu nutsuwa a ci abinci."
Suka tashi a tare har ita Minal din da take saman cinyarsa ya kar'bi yaron dama kusan rabi a hannunsa yake ta dira kasa tana kallona ." Mama za ki goya mini shi idan an jima ko?"
Na gyad'a kaina alamar E ta juya da niyyar fita tana d'an tsalle.
Shiru na wani lokaci kafin na ji sautin numfashinsa." Ko yanzu Ubangiji Allah Ya d'auki raina Amina kin gama biyana hakika alherin da yake tattare da tarayyata dake ba zan k'idaya shi babu abu mafi girma da arziki face wannan.
Allah Ya saka da alheri, ba zan boye miki ba na jima ban tsinci kaina cikin yanayi na farinciki kamar wannan rana ba.
Sai dai jikina ya yi sanyi ainun da lamarin yaron nan Khalil ko lokacina ya kusa ne zan tafi na bar ku."
Hararsa na yi ina fad'in." Kai ma abinda za ka yi kenan wace irin magana ce wannan don Allah."
Ya dubi fuskar yaron da yake hannunsa a tsanake ya ce." Sai dai shekarun girma suka cimmani Ubangiji Allah Ya azurta ni da 'yan baiwa gasu nan kin san dai ba zan maimaita shekarun da na yi a baya ba ko Annabi Muhammadu s a w ya ce sittuna au saba'una.
Yanzu hamsin da takwas nake."
Shiru na yi ban ce masa komai saboda takaici mutuwa dole ce amma a ganina bai kamata a kawota a yanzu da muke cikin annashuwa ba.
Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Wayarsa aka kira ya canza harshe larabci yake yi sosai.
Na tsinci wasu daga cikin abinda yake fad'a wasu kuma ban fahimta ba yana dai ta fad'in sunan Sukairaju a maganarsa ya gama ya dube ni yana fadin." Ba'ki na yi daga madina akan wani lamari ina barar addu'a."
Na ce." A cikinta nake kullum Allah Ya yi riko da hannayenka, ni ma na gode sosai Allah Ya saka da alheri."
Ya tsare ni da ido yana fad'in." Me na yi na godiya Amina?"
A takaice na ce." Abubuwa da yawa.
" Ya yi shiru bai ce komai yana dai ta kallona ina kici-kicin gyara rigata ya taimaka mini Hasan din ne yake mamulan baki da neman abinci ya d'ora mini shi saman cinyata na tallafe shi sosai nasa masa nonon a baki.
Ya kuwa kama yana sha yaran yanzu duka da wayonsu ake haifarsu amma dai duk da haka na d'an taimaka masa wajan ganin ya rike a bakinsa.
Ya ce." Idan Allah Ya kaimu za mu je asibiti tare kamar yadda na fadi da farko domin a duba mini su."
Na ce." Allah Ya kaimu." Ya duba agogon dake d'aure a hannunsa magriba ta yi ya shiga toilet dina ya dauro alwala ya fita zuwa massalaci.
Duka su biyun na shayar.
Baba Tabawa ta shigo tana fad'in.'' ko akwai abinda nake buk'ata wanda zan ci.
Na ce ta dama mini kunun gyada kawai na fara dumama cikina an jima idan na yanke shawara akan abinda zan ci zan gaya mata.
Ta dubi yaran suna kwance a gado bacci suke yi ta furta." Ko za a goya su ne Hajiya?"
Na yi dariya tare da fad'in." Sultan din fa?"
Itama tana dariya ta ce." Ai ya girma shi ya zama saurayi."
Na ce." Mu bari zuwa gobe tukkuna Babansu zai dawo."
Ta gyadq kai tare da juyawa da sauri ta fita.
Cikin kwanaki biyu da haihuwa dangina da nasa babu wanda bai ji ba.
A kuma yau da suke da kwanaki uku a duniya Hajja da yayarsa Hajiya Saratu suka sauka a garin da abin arzikinsu akwati biyu cike da kayan yara kowanne da tasa
Anti Yagana kuma ta ce mini itama dai tana tafe da muka yi waya da ita.
Baban Saude kuwa kwana d'aya da haihuwar ya zo bakinsa kamar zai yage ganina kalau yaran ma haka domin ni da shi baban nasu mun sake samun nutsuwa da kwanciyar hankali a lokacin da aka tabbatar mana da ingancin lafiyarsu sai farinkinmu ya sake hauhawa.
Kwana ya yi da safe bayan ya karya kummalo ya yi mana sallama ya wuce wajan sana'arsa har yana yi mini alkawarin zuwan iyalinsa tunda mun ce da taron suna ko dai ba su zo gabad'aya ba Anti Saude da Mamansu za su zo idan mun tsayar da ranar da za mu yi bikin sunan ya ce na gaya masa.
Na yi ta murna kuwa ina yi masa godiya kafin ya tafi.
Shud'ewar wannan kwanakin babu Hauwa babu dalilinta.
Khalil ya gaya mata ranar dana haihu haka zalika ma mijinta ya gaya mata da bakinsa ya gaya mini ta sani.
A yadda na fahimta yana tunanin ta zo tunda ba yini yake yi a gida ba tunda ya yi ba'kin nan bai zauna ba sai da daddare yake shigowa kuma kwana daya da haihuwar ta kar'bi girki.
Yau da su Hajja su ka zo ya dawo gidana.
Zuwa yanzu ni ma na fito falo cikinsu amma ta ko'ina jikina a rufe yake kafafuna ma koyaushe suna cikin safa.
Tunda na haihu Allah ya hore mini lafiya ba ni jin ciwon irin na gigita bayan haihuwa kuma babu abinda ba na gudanarwa na abinda ya shafe ni.
Wannan kad'ai ya isa na godewa Ubangiji.
Rashin zuwan Hauwa ya ta'ba mini rai ainun na kuma yi mamaki ba kad'an ba.
Masu aiki na hidima da yara ta kowace siga kowa k'auna da kulawa yake nuna mini me zan ce da Ubangiji.
Salim baya garin yana Legos amma Nusaiba zuwanta biyu Adam ma tunda na haihu yake shigowa haka zalika ma Nabila ta shigo mini kwana daya da haihuwa ta yi mini barka sosai ta fita...
Kwanansu Hajja biyu ranar biyar kenan suka fahimci akwai matsala daga bangaran Hauwa dalili da ni da maigidan da masu yi masa hidima daga waje har zuwa cikin gidan kowa cikin annashuwa yake yi.