← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 276

Sashe 179

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na dube shi idonsa biyu rufe idon kawai Yayi kamar mai bacci.

Na ce." Ka tashi kasha maganin to."
Bai yi mini jayayya ba ya tashi na d'auki ruwa na tsiyaya a cup na mik'a masa ina ciro maganin ina bashi yana sha tsaf ya gama ya ajiye zai kwanta na ce." Ka dan bari ya fad'a maka." Bai ji ba ya yi kwanciyarsa minti biyu kuwa sai yun'kurin amai.

Ya tashi da azama ya nufi toilet ya fara watso shi duk abincin da yaci da maganin da sha suka yo waje.

Na rasa yadda zan yi gabad'aya damuwa ta dabaibayi ni.

Haka nan na tarairayo shi muka fito ya je ya kwanta ya nishi.

Na lura baya son ciwo kuma bashi da wani dauriya idan bashi da lafiya haka ya yi mini lokacin da ya kwanta ciwon mura a gidana na kuntau na sha dawaniya.

Toilet na gyara na fito na same shi bacci ya d'auke shi sosai.

Aikuwa ba zai yiwu ba, tashinsa na shiga yi ya bude idonsa na ce." Dole fa sai ka tashi ka sake cin wani abincin da maganin idan yaso sai ka yi baccin."
Bai ce komai ba ya gyara kwanciyarsa ya rufe Ido.

Na ce." Ka tashi don Allah ka ji.''
Ya yi mini shiru bai motsa ba.

Kawai sai na zuba masa ido tsabar takaici da damuwa na ce." Shikkenan gaskiya zan sanar da Hajja an ta'ba yin ciwo ba cin abinci da magani."
Ya bude idon yana kallona yace." Wai ba na ci ba ne?".

Na ce." To nawa yake wanda ka ci, kuma duk ka amayar dashi da maganin."
Ya tashi zaune tare da tallafe ha'barsa.

Sosai na zura masa ido ina nazarinsa sai nake ganin kamar bayan ciwon da yake damunsa akwai wata damuwar.

Zuciyata ta fara raya mini ko ya fara kewar matarsa ne da ta rasu.

Wani sashe na daban yake ce mini 'Anya kuwa' ai an yi masa mace-mace da yawa ya ha'kura kuma bai ta'ba yin wani ciwo ba, kawai dai ciwon ne ya zo masa akan ga'ba ne.

Nasa hannu na cire hannunsa da ya tallefe ha'barsa da shi a d'an sanyaye na ce." Wai menene don Allah, kada ka jefe ni cikin tashin hankali, yau kana tallafe ha'ba ko akwai wani abu da yake damunka?"
Ya dube ni.

Muka tsirawa juna ido sosai mun jima a haka bai ce komai ba sai ni na janye idona na sake zubo masa abincin da kaina na dinga bashi cikin ikon Allah kuwa ya ci da yawa da kamar minti goma tukkuna na sake bashi maganin a karo na biyu, ban yarda ya kwanta ba sai da muka yi zaman kimanin minti ashirin har ya fara gyangyadi sannan ya kwanta ni kuma na sauka k'asa.

Na samu anti Yagana ta jima da yin bacci. wanka na yi a gurguje na sanya kayan bacci tare da a turare a jikina na koma saman.

Lokacin baccinsa ya yi nisa sosai, na shiga cikin bargon kusa dashi sosai na kwanta kafin na fara yin addu'ar kwanciya bacci.

Da asuba da d'an kuzari ya tashi domin ya riga ni ma tashi motsinsa na ji a bandaki na yun'kura da sauri na dira daga gadon domin ina tsoron ya ce zai watsawa jikinsa ruwa.

Na same shi yana alwala sai na sauke ajiyar zuciya na tsaya har ya kammala tukkuna ya fita zuwa massalaci sannan shiga toilet din sosai domin yin nawa uzurin.

Tun bayan da ya fita da asuban bai dawo ba sai wajejan goma da arba'in na safe.

Na d'an shiga yar damuwa saboda yanayin jikinsa.

Amma nasan abinda ya zaunar dashi bai wuce yin addu'a ba kamar yadda aka yi duk ranar da mamaci ya cika kwanaki uku da rasuwa.

Anti Yagana Hajja da inna Uwani Gwaggo sun shirya tsaf da Shirin tafiya muna falo da su gabad'aya domin jiran shigowarsa Kamalu ya riga shi shigowa da kusan minti goma kafin ya shigo.
idan kin karanta ba ki biya ni ba ina bin ki bashi.

Cikinmu ya zo ya zauna kujera kusa da ni.

Suka gaisa sosai.

Hajja ta gaya masa tafiya za su yi.

Na d'auka zai ce su yi hakuri su bari ayi bakwai sai bai nuna damuwarsa akan hakan ba ya ce ." Ita anti Yagana ta bari zuwa an jima kadan Sukairaju ya dawo sai ya d'auketa a mota ya kaita har gida.

Hajja kuwa dama a babbar mota suka zo da direbanta duk zai kwashe su har Hajiya Saratu Kamalu da Yusi da Shima shigowarsa kenan yanzu a lokacin da suke maganar cikin shiri tunda ya san da tafiyar tun jiya 'dan uwansa ya gaya masa
Cike da damuwa muka yi sallama na kasa daurewa sai da na yi kwalla na d'auko hijabi muka bi bayansu harbar gidan ni da anti Yagana har sai da suka shiga mota suka tafi tukkuna muka koma cikin gidan.

Anti Yagana ta koma d'aki ta kwanta jiran dawowar Sukairaju kamar yadda maigidan ya fad'a.

Na bi shi saman na same shi a kwance.

Na zauna a d'an sanyaye ina fad'in." Ina kwana?''
Ya tashi zaune yana amsa da kulawa tare da tsira mini ido.

Tun jiya yawan kallon nan da yake yi mini ya fara damuna."
Na ce." Ji ki ya yi sau'ki ko?"
Ya gyad'a kansa yana fadin." Alhamdulillahi, na ji sau'ki ina godiya."
A tak'aice na furta." Me za ka ci yanzu?"
"Shayi kawai zan sha idan da hali a yi mini farfesun kifi bakina babu test ko daya."
Na ce." Da hali mana da kaina ma zan yi maka sai ka had'a da bread ko?"
A tak'aice ya ce." Amma fara had'a mini tea din."
Na tashi na sauka kasa kicin na nufa Baba Tabawa tana ta gyare-gyare tare da wanke kwanunan da aka yi karin kummalo na hada duk abinda zai buk'ata na kai masa.

Na sake komawa kicin din Baba tana fad'in na bari ta yi na ce mata a a kawai ta bari ta huta jiki da jini tun asuba take tashi tunda aka yi rasuwar nan ga hidima da Sultan dama wani lokacin yana hannun inna uwani ko Gwaggo.

Farfensun ya yi masa dad'i sosai kuma ya sha da yawa ya hada da bread har da gyasa Yana fad'in." Ya yi mini dad'i sosai na gode."
Na ce." Sai shan magani?"
Ya gyad'a kansa yana dan murmushi na dinga cirowa ina bashi daya bayan d'aya ya sha.

Sannan ya kwanta yana. yi mini godiya.

Sai wajan sha biyu muka yi sallama da anti Yagana wai ita da ta zo gaisuwa har sai da ya bata kudi bayan sanyawa da ya yi a kaita.

Tare muka fito har da shi muka yi mata rakiya Sukairaju ya d'auketa a mota tana d'ago mana hannu.

Gidan ya kasance shiru kowa ya watse gabad'aya ma area ta yi tsit kamar ba a yi wata hada-hada ta jama'a ba tunda zahirin gaskiya ta samu mutane wannan kuma yana da ala'ka da su waye mazajen da ta aura da kuma fannin kasuwancinta sai danginsu daga can jos din da suka dinga zuwa.

Tun da ya yi sallar azuhur ya kwanta sai daf da la'asar tukkuna na tashe shi.

Ya tashi kuwa da kuzari sosai ya ce zai yi wanka na ce a a tunda la'asar ce babu kyau haka annabi ya ce.

Kuma gashi ba shi da lafiya.

Yana d'an murmushi ya ce." Ban ta'ba jin wannan hadisin ba Amina, sannan a ina aka ce idan mutum ba shi da lafiya ya daina wanka, ba zan iya ba gaskiya."
Na b'ata rai ina fad'in." Wallahi haka aka ce babu ky
u wankan daf da la'asar da bacci.

Sannan kuma duk mai zazza'bi bayan son ruwa sai ka ga ciwon ya sake tsananta ka manta jiya kana zubawa jikinka ruwa ya rikice."
Ya ce." Kwarai kuwa hakane amma ai yau gabad'aya ban yi wankan ba fa tun safe kin ga kuwa babu lefi don na yi yanzu, tunda na ji sau'ki gaskiya."
Na ce." Kadai bari sai da daddare idan za ka kwanta."
Bai ce komai ba ya nufi toilet din ba bi shi a baya sai naga yana burush ina tsaye ina kallonsa ya gama ya daura alwala ya fito.

To a daran ranar can gidan Hajiya Maryam dai ba su rintsa ba duk da an cire rumfuna kuma maigidan ya sallami kowa amma su anti Yabi ba su tafi ba.

Ita Nabila dama ta ci alwashin zama domin ta cigaba da kula da yaran.

Anti Yabi Saliha da Rukky da shi Bashir din suka zauna wai sai an yi bakwai sai gidan ya kasance sai su kadai da masu aiki Taburni da Mairo sai yara Khalil Twins da Minal da suke hannun Mairo domin itace jigon kula da su shi Khalil yana tare da Adam tare suke kwana dakinsu daya itama Nusaiba tana nan ba ta tafi ba tukkuna.

Talatainin dare wajan biyu da yan mintina duk sun yi bacci Bashir ya kusa kansa d'akin da suke kwance wanda ya kasance nan ne bedroom din Maryam din matattarar sirrinta anan suke ta dabdalarsu.

Anti Yabi da Saliha sun yi washar da su a makad'ed'an gadonta suna ta bacci yayin da Nabila ke kwance kasan kafet ita kuma Rukky na can kan wata shirgegiyar kujera dake can gefa bacci ya shammceta ta bar wayarta a kunne tana yi kallo take yi wata'kila baccin ya cimmata.

A kan Nabila ya tsaya yana fad'in." Ta shi, ke anti Nabila."
Ta tashi zumbur ta ganshi a tsaye dogare a kanta ta ce." Baka da hankali za ka shigo mana a wannan daran wai Bashir me yake damunka ne?"
Ya ce." Na gaya miki tun muna sheda juna ku sallame ni na ware, idan ba haka ba wallahi sai na yi muku illah."
Ta mutsika idonta sosai tana fad'in.'' Dame zan sallama ka Bashir na rantse da girman Allah zan yi magan.....

Ba ta k
rasa ba ya fille 'yar k'aramar askar da take hannunsa mai bala'in kaifi ya yi mata bille a kumatu gefan idonta.

Cikin tsananin kid'ima da tashin hankali ta kurma ihu! jini ya mamayeta fuska tunda askar ta shiga sosai kuma ta samu tsokar kumatu.

Gabad'aya suka tashi zaune.
Chapter 179 · 0% Book details