Sashe 202
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dai duk yadda na kai ga kishi da nuna k'iyayyata akan kishiya ba zan iya neman hanyar da zan halakar da ita ba kamar dai yadda Maryam ta yi ba kuma zan 'kir'kiri karya ko da sharri na ya'ba mata ba.
Ina da kishi sosai mussaman akan abinda nake so amma a duk lokacin da ya taso mini nakan iya sarrafa kaina zuciyata bata ta'ba kissima mini na bi wata hanyar domin cutar da kowa ba.
Zazzabi ne mai zafi ya rufe ni da ciwon kai abubuwa da yawa sun yi mini dabaibayi haka na yi wani irin bacci mara dad'i da mafarkai irin na mai mashashshara.
Biyu da minti ashirin na tashi kaina ya tsananta da ciwo na daddafa na shiga toilet alwala na yi na fito na yi salla kafin na fita falon.
Shiru na d'an harari kofar d'akinta a garkame kamar koyaushe tsaki na yi na wuce dakin su Baba Tabawa nan na tarar da Nusaiba ashe tun d'azu ta zo tana cikinsu suna ta hira muka gaisa sosai na tambayeta yara tace mini suna can gidan kakarsu da ta haifi Babansu.
Kamar wancan lokacin ranar addu'ar uku yau ma da shirin kwana ta zo.
Na ce hakan ya yi ka fi na dubi Baba Tabawa da take ta fama da Sultan yana ta rigima ta ce tana tsammanin zazza'bi ne a jikinsa don ya yi zafi.
Na shiga d'akin sosai na sunkuya na ta'ba wuyansa rau zazza'bi yake da gaske kamar ni dole ne kam Dr Sailuba ta zo gidan nan ta duba mu.
Goya shi ta yi tana jijjigashi har ya yi bacci muka fito falon ni da ita ta shiga kicin ni kuma na zauna saman kujera cikin nauyin kai da bugawa.
ci ta kawo mini alkubus suka yi da rana da miyar agushi ya yi mini dadi sosai na ci hud'u nasha ruwa na sake komawa d'aki na kwanta ashe tana hankalce da ni ta biyo ni dakin tana fad'in.'' Hajiya ba kya jin dadi ne tunda ki ka fito na karanci yanayinki."
Na ce." Wallahi zazzabi ni ma nake yi Baba har ma da ciwon kai."
Ta dinga yi mini sannu cikin damuwa.
Na daure na tashi zaune tare da d'aukar wayata na lalubi number Dr Sailuba bugun farko ta daga muka gaisa na ce mata idan babu damuwa ko za ki zo gida ki duba ni da yaron nan Sultan nasan yau babu aiki gashi weakened muke babu matsala ko."
Ta ce." Babu komai zan shigo bayan la'asar maigidan ma baya gari ai."
A tak'aice na ce." Na gode sosai." Na kashe wayar na ajiye Baba Tabawa ta ce." Ko da akwai abinda ki ke buk'ata na game da abinci tun da naga baki ciki alkubus din nan da yawa ba."
Na ce." Da daddare ku yi mana towo a yi kuka maigidan ita yake so amma a yi mini miyata daban ta d'an yi yaji."
Ta ce." An gama in sha Allahu ta juya ta fita da sauri.''
Ledar kayan motsa bakin da Hajara ta ba ni na d'auko na tsinci tsamiyar biri na sanya a bakina saboda galmi-galmi nake jinsa na sake kwanciya da wayata a hannu.
Na rasa wanda zan kira na gayawa tsakanin anti Yagana da Sahura abinda yake damuna a game da abinda Hauwa ta ce mini d'azu abin ya tsaya mini a raina.
Anti Yagana na kira muka gaisa jin maganata da kasala ya sanya ta fara jero mini tambayoyi na ce."lafiyata lau amma ina zargin ciki ne da ni.'
Ta ce." Ba ki na zargi ba kin tabbatar kuma kin gayawa mai shi ko?"
Yar dariya na yi domin nasan dalilin da ya sanyata ta fad'i haka tunda artabun da aka sha a baya na ce.'' Na tabbatar gaskiya shi din ne smma yanayi bai barni na sanar masa ba amma zan gaya masa yau idan ya dawo ya je bunkure wajan Malam D'aha."
Babu tsammanin kawai na ji ta rufe ni da fad'a.
Sai da na bari ta gama na ce." Lokacin da na samu cikin nan fa yana kwance anti Yagana bai ma san a inda yake ba yanzu ne ya dan fara dawowa hayyacinsa babu abinda zai faru in sha Allahu."
Ta sauke ajiyar zuciya kad'an tana fad'in.'' Duk da haka dai Amina tunda kin san halin mijinki da zargi mussaman idan kin samu ciki kamata ya yi ace yanzu ya sani tunda ai ya jima da dawowa nutsuwa ba ki da wata hujja anan."
Na ce." Ki yi hakuri zan gaya masa in sha Allahu anti Yagana ni akwai dalilin da ya sanya ma na kira ki yanzu."
Ta ce." Menene kuma?''
Hanci na dan ja a sanyaye na furta." Hauwa ce take jingina rasuwar Hajiya Maryam da ni." Duk na kwashe sa'insar da muka yi da ita na gaya mata .
Ta ja tsaki tana fad'in." Ta dawo ashe?''
Na ce.''kwarai ta dawo amma ta ki yadda mu zauna lafiya fitinar yau daban ta gobe ma daban tana daga mini hankali wallahi domin ni yanzu anti Yagana babu abinda na fi buk'ata face zaman lafiya duniyar nan tsoro take ba ni."
Ta furta." Kin ga Amina idan za ki kwantar da hankalinki ki kwantar ina abin yake me yasa Hauwa zata razanaki har ki dinga jin fargaba a kanta.
Ban yarda ki zalinceta ta kowace siga ba amma ki daina raga mata balle ta hangi lagonki ta raina ki tunda ita Yar iska ce mara mutunci to sai kema ki sanya rigar rashin mutuncin ku buga aga wanda zai ci riba ina dalilin wannan masifar."
Na ce." Anti Yagana ai na riga na yi wa Hajja alkawari ba na so na biye mata wata matsalar ta faru wadda Hajja za ta ji haka kawai dattijiwar take ba ni tausayi wallahi a ganina idan nima na biyewa Hauwa kin ga mun zama sakarkaru gabad'aya kuma maigidan ba zai samu nutsuwa ba.''
Ta ce." Ai ba cewa na yi ki biye mata ba Amina ki fita daga harkarta ki daina raga mata ko ki nuna mata kina son zaman lafiya da ita.
Kuma ki yi duk yadda za ki yi wajan ganin kin sake samun gurbi a zuciyar mijinki abinda nake nufi kenan."
Na ce." Ni ma shawarar dana yanke kenan wallahi."
Ta furta." Dada kuwa ba ta da lafiya sosai Amina har sai da ta kwanta a asibiti kwananta biyu jiya aka sallamota."
Da damuwa mai yawa na furta." Mai yake damunta ne?"
Ta ce." Lalura ce kawai irin ta girma da shekarun yau ta ce kafafunta na ciwo gobe ta ce bayanta ya 'kage abinda dai ya tsananta a ciwon har ta kwanta a asibiti ciwon wuya da ta yi eanda ta kai ta kawo ma ba ta iya motsa wuyan ya 'kage amma yanzu alhamdulillahi da sauki."
Cike da tausayinta na ce.'" Allah Ya sawwa'ke idan ya dawo zan gaya masa wata'kila mu zo dubata.
Anti Yagana ina labarin Ya falmata ne ko a Whasap na jima ban gan ta ba kuma mun jima ba mu yi waya ba.
Ta ce." Ai Ya falmata tana saudia neman kud'i Baban Saude ya shige mata gaba wajan mahukunta sai da Alhaji Bana ya sake ta."
Na ce.'' To kin ga wannan shine adalci ai ko banza ana samun jajurtatun iyaye a family kamar irinsu Baban Saude da yawa mazan da suke zalintar matayensu za su shiga hankalinsu.
Abinda ya faru shine kowa ya san da cewar Ya falmata macace mai zafin nema domin ni kaina itace madubina kuma sai da na takata tukkuna na tashi.
Harkokinta sun bukasa sosai a lokacin da muka had'a karfi da k'arfe domin gina gobenmu muka tashi a tare.
Tun bayan da na yi auran nan sai kasuwancin da muka yi da ita ya raunana dalili duka ta nuna mini hanyoyin yadda zan dogara da kaina da kuma yadda kayana za su cigaba da zaga 'kasashen waje irinsu sinigal nijar mali kamaru da chadi har ma da saudiya dama kusan sune suke sayan kayanmu a lokacin da muke fafutar ganin mun tashi manyan matan abuja ma suna saye amma duka ta hanyarta tunda ni ce mai aikin dinkawa na yi mata odarsu zuwa maiduguri ta rarraba a sassasa daban-daban.
Ta cigaba da kujiba-kujibarta ni ma na cigaba da yin tawa har Allah ya sanya ta bude katafaran shago ta zuba iyayen kekunan d'inki manyan kai da k'ananu ya yara suna aiki.
Shekara daya ta sake bude wani a takaice dai sai da shagunanta na d'inki suka kai biyar kuma shago bai wai karami ba wanda yake iya cin sama da keken d'inki goma sha biyu.
Mijinta Alhaji Bana shine silar karyata domin had'a ba ki ya yi wasu daga cikin yaranta suka dinga kwashe mata kaya cikin dare suna fita da su a baggo.
Idan suka sayar su raba kudin kashi uku shi ya d'auki kashi biyu yaran su d'auki kashi daya.
Wataran rigima ta shiga tsakanin yaran nata da suke aikata mata haka har da makami abinda ya assasa musu zuwa gaban hukuma kenan daga nan sai suka fara tonawa junansu asiri dama kuma gefe guda ta sanya Malamai ana ta yi mata ro'kon Allah itama ta tsananta da addu'a.
Suka fadi mijinta ne me sanya su da ya ji duka da matsa ya tabbatar da sanya hannunsa wanda da da farko ya fara gardama da jayayya yana fad'in yaushe zai kai matarsa k'asa uwar yaransu har biyu.
Daga lokacin ne ta yi tsalle ta dire ta ce sai ya saketa har suka shiga kotu alkali ya yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata ya kuma tilastashi sakinta tunda gaskiya ba namijin da kowace mace za ta yi sha'awar zama da shi ba ne.
Anti Yagana ta cigaba da cewa." Ai tana fita idda ta lallaba Dada ta tafi makka wata shida fa yanzu tun bikin Fadila
Na ce." Allah sarki Ya falmata zuciyarta a tsaye take irin ta Baban Saude ba ta son zama koyaushe tunaninta ya za a yi ta juya biyar ta koma goma.