Sashe 254
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban yi tunanin zuwansa a ranar ba tunda duka bai fi kwanaki uku da komawarsa ba
Allah sarki sai gashi wajejan k'arfe goma sha biyu na dare har da mintina akai ya shigo gidan Hajja wata'kila tafiyar mota ce kuma bai fito da wuri ba.
Ya d'an ba ni tausayi ganin yadda rayuwarsa take gudana a tafe daga nan sai can babu wani hutu idan har an kwanta to dare shima a cikinsa sai an yi wata ibadar ta jijjiga jiki.
Lokacin da ya samu kwanciya da wadataccen hutu na dole da rashin sukuni
shine lokacin da Hajiya Maryam ta shimfid'ar dashi shine ya yi kwanciya mai kamar mutuwa hutun dole ba don dad'i ba.
Muka kwana tare da shi a b'angaransa na gidan inda na sauka da zuwana.
Sosai ya yi mini ta'aziya ya jajanta rasuwarsa ya kuma bayyana alherinta tare da jadadda mini ri'ke amanar da ta bashi kafin rasuwarta.
Da gari ya waye ya riga mu yin gaba domin ko cikin gidan bai shiga ba wurin su Hajja basu san ya zo ba.
Ya ce duk idan sun had'u gidan rasuwar sai su gaisa.
Haka kuwa aka yi a can gabad'aya suka gaisa da su Dada ya zauna cikin jama'a ana ta kar'bar gaisuwa da shi Babanmu a gefensa da Baba Sule sai Idiris dana hange shi a gefe a zauna kusa da Baba Sule duka muka gaisa kafin mu shiga ciki nan ma ma'kotanta suna ta hidima da wasu daga cikin danginta da suka sauka jiya da daddare.
Ranar sadakar uku daga gidan Hajja aka yi abin sadaka abinci mai kyau ciki har da wainar shinkafa fanke da wainar gero da sauransu haka Magaji ya d'auki kololin abincin ya tafi ya kai gidan da sassafe.
Kafin ya dawo ya dauke mu gabad'aya zuwa gidan.
A ranar ne Sahura da Yusura suka zo mini gaisuwa da yamma kuma sai ga anti Maimuna uwargidan Alhaji Muntari tare da Salima babbar yarinyarsu goye da d'anta a baya.
Na ji dadin ganinsu kuwa abubuwa da yawa suka hana ni neman inda suke a duk lokacin da na zo garin amma ina samun labarin Turmuzi a wurin Hamusu tunda ragamar kula da shi tana hannunsa har yanzu shine ma yake zuwa duba shi makaranta kamar dai yadda ya dinga d'awainiya da Kamalu.
Muka gaisa sosai cikin karamci da kulawa ta ce mini itama labarin rasuwar ta ji ta ce bari su zo tun kafin a watse tasan ina nan ban tafi ba sai su yi mini gaisuwa.
Na dinga godiya kuwa ina tambayarta yara ta ce mini duk suna nan lafiya lau. salimat ta kwanto mini yaronta daga bayanta tana sinne kai Sahura na tsokanarta to abin ai ba wahala tunda dama 'kawar Yusura ce kusan sa'annin juna ne itama gata nan da d'anta daga zarar an yi auran ne sai haihuwa yanzu shiyasa wasu samarin a cikin irin abinda suke saye na angwanci suke hadawa da pampas da set din kayan sanyi domin jiran ko ta kwana.
Anti maimuna ta ce mini tana nan tana sana'arta sai abinda ma ya yi gaba domin har ta kama shago gaba da su kad'an ana sauke mata motar itace da buhuhunan gawayi tana gaya mini ita Jamila tana can harkar film take yi.
Kuma sau biyu ta zo ta duba yaranta tun bayan rasuwar Babansu ta tayar da masifa a sayar da gidan a bata gadon yaranta sai da aka yi mata rubdugu jama'ar unguwa suka yi mata tara-tara kamar za su daketa sannan ta kama borin kunya yaran unguwar marasa kunya masu jini a jikina suka ce duk ranar da ta sake shigowa unguwar sai sun zane mata jiki.
To tun daga lokacin ne bata sake zuwa ba wai da har ta yi barazanar shigar da kara kotu tana fad'in ba ta yarda da wajan da aka kai mata yaro ba sannan ba a nemi shawararta ba.
Kuma shiru har yanzu dai ba a sake jin doriyarta ba sai dai suna ganin seriars film dinta mai suna *Gidan kashe ah* tana fitowa a magajiyar karuwai wai acan garin lakwaja ake shirya film din gidan karuwai.
Abin ya dinga ba ni mamaki da al'ajabi Jamila mai take nema a duniyar nan ita a maimakon ta zauna ta yi hakuri ta kula da yaranta marayu kamar yadda 'yar uwarta ta yi sai take ganin kamar cutar da kai da kuruciya ne gwara ta fita yawon bariki domin dai a matsayinta na ya mace mai sauran kuruciya bai kamata ta wulakanta rayuwarta irin haka ba.
Salima ta d'auko wayarta daga cikin jaka ta lalobo film din tana nuna mini.
Na kar'bi wayar ina dubawa Sahura na leko kanta muka cika da mamaki tana tsakiyar karuwai da sigari a hannunta suna buga karta ana shewa da tafi kuma wai film ne.
Na yi sauri na mik'awa yarinyar wayarta ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.
Lallai idan ka ga wannan tambad'ewar akwai hakki ko kuma baki na iyaye.
Ai akwai y'an film 'din masu nutsuwa da suka mayar da harkar sana'a kuma ta yi musu riga da zani wasu har da mahalli da jari amma ita hanyar da ta d'auka ba za ta yi mata kyau ba domin su kansu masu d'aukar film din suna duba dacewa akan abinda za su d'ora mutum akai wata'kila shiga da mu'amularta ya nuna musu ga abinda tafi k'warewa a kai Ubangiji Allah Ya tsarkake mana zukatanmu.
kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Washe garin ranar da Gwaggo ta yi uku a gidanta na gaskiya muka tashi da azimin farilla na Ramadan.
Kowane bawa ya samu nutsuwa da kuma kad'aita kansa ga mahallici domin samu rabauta da dacewa.
Ranar sadakar bakwai addu'a kawai aka yi mata ba a zauna ba tunda dama azimi ake yi Yallabai din yana nan bai tafi ba tukkuna shi da mahaifiyarsa suna ta fitar da abinci buhu buhu da abin masarufi domin sadaka da aka sha ruwa aka fita da d'anye hadiya ga marigiyar kamar yadda na ji Hajjan tana fad'in.
goma ga azimi suna ta wannan aikin harabar gidan Hajja cika take yi da mutane har da mata abin dai gwanin ban tausayi daga waje ma jama'a ne cike buhun shinkafa ce da kudi dubu goma ga mai rabo ban san iya adadin mota nawa ya sauke ba bayarwa ake yi jama'a na k'aruwa har sai da azimi ya raba tukkuna abin ya yi sau'ki.
Lokacin kwanan su baba Tabawa tara da a kasa mai tsarki tunda hud'u ga azimi suka tafi a yadda yake gaya mini yaran suna can gidan Hauwa duk da har yanzu jikinta bai dawo daidai ba akwai mai aikinta Ladidi da kuma Inna Uwani ba ta tafi ba wai sai bayan sallah.
A lokacin ne na ji hankalina ya yi gidan gabad'aya saboda ban yarda da zaman yarana a gidan Hauwa ba.
Na fara yi masa maganar tafiya ya ce sai ashirin ga wata yana lissafin zakka ne sai ya kammala.
Babanmu ya kira ni a waya yana ta godiya wai an kai musu abinci har buhu biyar da taliya da sukari har da gero shi da Baba Sule na ce babu komai sadaka ce anan yake yi mini albishir din fitowar Hadiza kwana biyu da suka wuce gwamnati ta yi yasa da sasaauci a gidan gyaran halin da take zaune duba da watan da muke ciki an duba iya adadin shekaru da zamanta a gidan Allah Ya taimakata ta shiga cikin wad'anda suka fito ba tare da tsananta bincike akan lefin da ta aikata ba.
Magana ce ta gwamnati bisa sahalewar gomna duk abinda aka ce hukuma a gidan duniya ai k'arshen magana kenan sai dai idan an je can lahira anan Ubangiji zai fitar da sakamako.
Yana gaya mini tana nan koyaushe cikin sallar dare da ro'kon Allah gafara kuma duk ta tsangwami kanta bata fitowa ta yi walwala da jama'a.
Tausayinta ya kama ni sosai na ce ya gaya mata zan kira ta a wayar Ummansu mu yi magana idan na yanke shawara dama dole hakan ta kasance fita ma gagararta za ta yi tunda kowa ya san abinda ta aikata jama'a za su yi ta kallonta wasu ma har su jefe ta ko kuma a farauci rayuwarta kamar yadda suka farauci ta wani ita da abokiyartata Hajiya Alili da har yanzu ba san a ina ta boye ba.
Da yamma ranar Hajiya Saratu ta zo domin yi mini ta'aziyya ba ta samu zuwa ba a lokacin rasuwar sakamakon ciwon kafafun da ta d'an yi a cikin kwanakin.
To da daddare kafin mu kwanta nake gaya masa halin da ake ciki tare da yi masa godiyar bisa alherin da ya yi.
Bai yi jayayya ba ya amince mini akan abinda nake so yana fad'in Hadiza 'yar uwata ce kuma gida dai sunan nasa ne amma ni nake rayuwa a ciki da yarana tunda har na aminta da zama tare da ita shima yana yi mata murna samun ku'buta tare da addu'ar Allah Ya tsare gaba.
Ban samu yin waya da ita ba sai da gari ya waye tukkuna na gaya mata hukuncin dana yanke ta dinga kuka tana yi mini godiya tare da jaddada mini a shirye take domin na ce zan turo Magaji ya zo ya d'auketa mu zauna tare a gidan Hajjan kafin lokacin da za mu tafi can abujan.
Ummansu ta yi kuka kamar me a waya tana yi mini godiya ina fad'in hannu baya rub'ewa a yanke a yar Hadiza har yanzu tamu ce kuma 'kaddara tana kan kowa farincikin ayadda ta tuba take kuma neman afuwar Ubangiji lallai shi din mai gafara ne da jin kai.
Kuma hakika fitowarta da wani lamari da yake kwance wanda mu ba mu san shi ba, da ya so da tun farkon lamarin ya kar'bi rayuwata don haka ni ma daga nawa b'angaran wannan kad'ai zan yi mata domin ta samu sassaucin zuciya killaceta a waje daya da ababen more rayuwa da kula domin ta dawo nutsuwa da hayaccinta.
Shi kansa Babanmu rasa abinda zai ce ya yi domin da da farko ya nuna rashin yardarsa yana fad'in Hadiza ta yi girman da za a ce ta je ta zauna mini a gida ita ba yarinya k'arama ba.